Sojojin Italiya 4 sun jikkata a wani hari da aka kai hedkwatar rundunar UNIFIL a Lebanon / Hoto: AA / Photo: AFP

Juma'a, 22 ga watan Nuwamba, 2024

1234 GMT — Sojojin Italiya hudu sun jikkata a wani hari da aka kai hedkwatar rundunar UNIFIL da ke Lebanon, a cewar majiyoyin gwamnati

Wasu sojojin Italiya hudu sun jikkata sakamakon wani hari da aka kai a hedkwatar rundunar kiyaye zaman lafiya ta UNIFIL da ke Shama a kudancin Lebanon, a cewar wasu majiyoyin gwamnati biyu.

"Sojojin Italiya hudu sun ji rauni kadan, kuma rayuwarsu ba ta cikin hadari", a cewar karin da daya daga cikin majiyoyin ya yi, tare da kari da cewa ana kan gudanar da bincike.

Tawagar wanzar da zaman lafiya da aka fi sani da UNIFIL tana jibge a yankin kudancin Lebanon domin sa ido kan hanyar da aka raba da Isra'ila, yankin da aka shafe sama da shekara guda ana gwabza fada tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hezbollah wadanda ke samun goyon bayan Iran.

1244 GMT - Ma'aikatan lafiya biyar ne aka kashe a harin da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon, in ji ma'aikatar lafiya ta kasar.

Ma'aikatar ta ce ma'aikatan jinya uku ne suka mutu yayin da wasu uku kuma suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai musu a garin Qotrani da ke kudancin kasar Lebanon.

Kazalika wani hari da Isra'ila ta kai a baya kan wata mota ya yi sanadin mutuwar ma'aikatan jinya biyu a garin Deir Qanoun Ras Al-Ain da ke kudancin Lebanon, in ji ma'aikatar.

2203 GMT — Isra'ila ta kashe mutum 90 a arewacin Gaza cikin awa 24

Jiragen yaƙin Isra'ila sun kashe Falasɗinawa aƙalla biyu tare da jikkata gommai yayin da suka yi luguden wuta a arewacin Gaza, abin da ya sa adadin mutanen da Isra'ila ta kashe tun daga safiyar Alhamis zuwa yanzu ya kai mutum 90, a cewar likitoci.

Isra'ila ta kai hari a gidan iyalan Al-Dayah da ke yankin Al-Sabra da kudancin Birnin Gaza, in ji kamfanin dillancin labarai na Falasɗinu WAFA, inda ya ƙara da cewa ma'aikatan agaji da motocin ɗaukar marasa lafiya suna can suna lalubo mutanen da ɓuraguzai suka danne.

Kazalika an jikkata ma'aikatan asibiti Kamal Adwan da ke arewacin Gaza, wasu daga cikinsu sun samu munanan raunuka, sakamakon bama-baman da jiragen Isra'ila marasa matuƙa suka jefa a harabar asibitin.

Wani ma'aikacin asibitin ya ce jiragen sun harba bama-bamai a kan janareton da ke bayar da wuta ga ɗaukacin asibitin inda suka lalata shi.

2346 GMT — Biden ya ce sammacin da Kotun ICC ta bayar na kama Netanyahu 'abin takaci ne'

Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana matakin Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya na neman kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa a matsayin "abin takaici".

"Sammacin da ICC ta bayar na kama shugabannin Isra'ila abin takaici ne," in ji Biden a wata sanarwa da ya fitar.

"Bari na sake bayyanawa ƙarara cewa: duk abin da ICC za ta nuna, ba za a haɗa Isra'ila da Hamas ba. Za mu kare Isra'ila daga duk wata barazana ga tsaronta daga kowa."

TRT World