An dakatar da aiki da sabuwar yarjejeniyar haɗin kai tsakanin Rasha da Iran

An dakatar da aiki da sabuwar yarjejeniyar haɗin kai tsakanin Rasha da Iran

Rasha da Iran sun haɓaka alaƙarsu a 'yan shekarun nan domin ƙalubalantar manufofin Amurka a ƙasashen waje.
Shugaban addini na Iran, Ali Khamenei ya gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a Tehran babban birnin Iran a 2018. / Hoto: Reuters

An dakatar da wata sabuwar yarjejeniyar haɗin kai tsakanin Moscow da Tehran na wani ɗan lokaci saboda matsalolin da ɓangaren Iran ke fuskanta, in ji kamfanin dillancin labarai na Rasha RIA da ya ruwaito wani jami'in ma'aikatar harkokin waje na bayyanawa.

"Wannan mataki ne mai kyau na shugabancin ƙasashen biyu," RIA ya ruwaito Zamir Kabulov, jami'in ma'aikatar harkokin waje yana bayani a ranar Talata.

Ya ce an dakatar da yarjejeniyar ce saboda matsalolin da abokansu na Iran ke fuskanta.

Babu wani abu da gwamnatin Iran ta ce har yanzu game da batun.

A 'yan shekarun nan, Rasha da Iran sun ƙara ƙarfafa dangantakarsu da manufar ƙalubalantar manufofin Amurka a ƙasashen ƙetare, suna kuma son ganin ƙasa ɗaya ba ta mamaye dukkan duniya ba.

A watan Satumban 2022 a yayin ganawa tsakanin Shugaba Vladimir Putin da marigayi shugaban Iran Ebrahim Raisi ne aka sanar da ƙulla sabuwar yarjejeniya tsakanin Moscow da Tehran.

Raisi, mai tsaurin ra'ayi da ake yi wa kallon zai gaji Shugaban Addini na Iran Ali Khamenei, ya mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a watan Mayu.

TRT World