An kammala wani muhimmin taro na matan shuggabannin ƙasashen Afirka kan sankara wanda aka gudanar a Nijeriya ranar Alhamis.
Taron, wanda Ƙungiyar Ƙasashe Musulmai ta Duniya OIC ta shirya a Abuja, ya samu halartar Uwargidan Shugaban Turkiyya Emine Erdogan tare da wasu matan shugabannin Afirka, da wasu manyan masu ruwa da tsaki.
Batun Wayar da Kai kan Sankara shi ne ya mamaye taron na kwana biyu, wanda aka fara shi ranar Laraba.
Taron dai ya mayar da hankali ne kan lalubo hanyoyin na zamani na riga-kafi, da saurin gano sankarar da kuma magance ta a ƙasashen Afirka mambobin ƙungiyar OIC.
Uwargidan Shugaban Turkiyya Emine Erdogan wacce ta halarci taron a matayin baƙuwa ta musamman ta nuna damuwa kan yadda aka yi watsi da muhimman darusa na tsarin rayuwa da aka gada iyaye da kakanni, saboda yadda zamani ke sauya abubuwa.
Emine ta kuma bayyana wa taron irin matakan da Turkiyya take ɗauka a yaƙi da sankara da kuma irin kyakkyawan sakamakon da ake samu.
"Na yi bayyana matakan da muka ɗauka na maye gurbin amfani da abubuwan masu sinadarai - waɗanda su ne ke janyo cutuk da dama - da abubuwan da Allah ya ba mu na ainihi, da kuma shirinmu na Kawar da Bola da kuma shirinmu na Amfani da Irin Shuka na Gida da Muka Gada," a cewar Emine.
Dangane da taron kuma, Uwargidan Shugaban na Turkiyya ta ce ta yi farin ciki an samu gagarumin ci gaba tun daga lokacin da ta karɓi baƙuncin taron da aka yi karon farko a Turkiyya.
"Taron da aka yi a Burkina Faso a 2018 yanzu kuma gashi ana yi a Nijeriya alama ce dake nuna cewa irin da muka shuka da taron da na shirya karon farko a 2016 da kuma "Sanarwa Istanbul" da muka ayyana, to ya nuna cea shukar ta yi kyau." A cewar ta.
Ta jaddada aniyarta ta haɗa hannu da ƙasashen Afirka wajen yaƙi da cutar sankara a nahiyar.
"A shirye muke mu baku iliminmu da kuma duk wani haɗin kai da 'yan Afirka 'yanuwanmu," in ji Emine
Da take jawabi a wajen taron, Uwargidan Shugaban Nijeriya Oluremi Tinubu wacce ita ce mai masaukin baƙi ta yi kira da a ƙara samun haɗin kai wajen yaƙi da sankara a duniya.
Ta kuma gode wa Emine Erdogan saboda yadda take nuna damuwa da lamuran Afrika, da kuma yadda ta halarci taron.
“Ina so in gode wa mai ɗakin shugaban Turkiyya saboda kasancewarta ta farko da ta karɓi baƙuncin taron na matan shugabbanin ƙasashen OIC a 2016 a Turkiyya,” a cewar Oluremi Tinubu.
Ta ƙara da cewa, “ina so in ƙara gode miki sosai saboda ƙaunar da kike yi wa yankinmu.” “Kin nuna haka ta yadda a cikin littafinki kika bayyana cewa Afirka rana ce mai fitowa.
"Muna sonki ko don saboda samar da cibiyar Afirka a Ankara,” a cewar uwargidan shugaban Nijeriya.
Shi ma Dokta Ahmad Kawesa Sengendo, Mataimakin Skatare Janar na kungiyar ta OIC ya yabawa Emine Erdogan saboda kyakkyawan misalin da ta bayar da ya kai ga nasarar gudanar da tarukan kan batun sankara. “Muna mika godiyarmu ta musamman ga Mai Girma Madan Emine Erdogan saboda ba da kyakkywan misali, ta yadda aka dama da ita wajen gudanar da taro na farko na musamman na matan shugabannin kasashe tare da OIC, a lokacin da aka yi Taron Musulunci Karo na 13 a birnin Isntanbul a Turkiyya ranar 14 ga Afrilun 2016,” a cewar Dokta Ahmad Kawesa yayin da yake jawabi a wajen taron na Abuja ranar Alhamis.
Sauran waɗanda suka yi bayani a wajen taron sun hadar Uwargidan Shugaban Saliyo, da Uwargidan Shugaban Gambiya da Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya da ministan lafiya, da shugaban Majalisar Wakilan Nijeriya.
Matan na shugabannin ƙasashen sun amince da abin da aka cimma a taron na Abuja kan Shirin Rage Yaɗuwar Sankara na Matan Shugabannin Ƙasashe, wanda Uwargidan Shugaban Nijeriya Remi Tinubu ta karanta, sannan duka matan shugabannin suka saka hannu.