Matar shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta jagoranci taron farko na Kwamitin Mashawarta na Majalisar Dinkin Duniya kan Inganta Muhalli.
Da take jan hankali kan batun cewa ana jan lokaci wajen tsaftace da inganta muhalli a duniya, Emine Erdogan ta ce gusar da shara daga kan iyakar kasa kadai ba zai kawar da matsalar ba.
Ta ce za a iya gyara tsarin ne kawai ta hanyar hada hannu, in da ta kara da cewa Ankara ta cimma hakan ta wajen shirinta na kawar da shara dungurungum, wato Zero Waste Project.
"Mun yi nasarar tabbatar da hakan da kashi 13 cikin 100 a shekara biyar da suka wuce, in da muka kai kashi 27.2 cikin 100 a kankanin lokaci, sannan kashi 30 cikin 100 a 2022," in ji ta. "Burinmu shi ne mu kai kashi 65 cikin 100 nan da shekarar 2035."
"Da wadannan nasarori, mun kare yankin da girmansa ya kai filin kwallon kafa 2,000. Mun kare tekunanmu kwatankwacin yawan ruwan da iyalai miliyan biyu suke bukata a shekara.
"Mun samar da makamashi kwatankwacin yawan lantarkin da iyalai 200,000 ke bukata a duk shekara. A hannu guda kuma, mun samar da ayyukan yi ga dubban 'yan kasarmu," ta fayyace.
Da take bayani kan yadda ba ruwan matsalar sauyin yanayi da bambancin kasashe, Uwargidan Erdogan ta ce a shirye Ankara take don musayar dabarunta da sauran kasashe.
Wayar da kan al'ummar duniya
Ta tunasar da cewa a watan Satumban bara ne aka kaddamar da shirin kyautata muhalli na duniya na Global Zero Waste Goodwill Declaration, wanda ya hada da daukar matakin farko na kyautata muhalli a matakin duniya, karkashin sa hannun Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres.
Ta ba da labarin abin da ya faru a lokacin, na cewa Turkiyya ce ta mika wa Babban Zauren MDD yarjejeniyar Zero Waste da kowa ya amince da ita, in da ta ce sakamakon cimma yarjejeniyar, aka ayyana ranar 30 ga watan Maris ta kasance ranar da aka sadaukar don yin fafutukar tabbatar da tsaftar muhalli ta shirin Zero Waste.
"A wani karin sakamako na matakin, aka kafa Kwamitin Mashawarta na Zero Waste, wanda shi ne dalilin da ya sa muka kasance a nan a yau," in ji ta.
"Tare da hadin kan Hukumar Muhalli ta MDD da UN-Habitat, muna da burin kara wayar da kai a matakin duniya ta hanyar bayyana matakan da suka dace da kuma ba da labaran nasarorin shirin zero waste."
Bikin ba da lambar karramawa
Uwargidan Erdogan ta ba da shawarar cewa ya kamata a dinga wani biki na ba da lambar karramawa a kan shirin Global Zero Waste duk ranar 30 ga watan Maris, tana mai cewa: "Don karfafa zumudinmu kan ranar 30 ga watan Maris, ya kamata mu kuma sanya batun sanar da Shekarar Zero Waste a cikin tsarinmu."
"A yayin da muke yada manufofin nan, ya kamata kuma mu karfafa goyon bayan inganta abubuwan more rayuwa a matakin kasa da na duniya," ta ce.
Da take bayani kan cewa ya kamata dukkan kasashe mambobin MDD su bi matakan shirin Zero Waste, ta jaddada cewa yana da matukar muhimmanci musamman ga kowane dan adam ya aiwatar da wadannan matakan da aka samar.
"Ya kamata mu koyi dabi'ar gyarawa da tsaftacewa maimakon gurbata muhalli, ya kuma kamata mu dinga karfafa tsarin rayuwar da za mu rage samar da shara barkatai a fadin duniya," ta ce.
"Yana da kyau mu karfafa hadin kanmu da MDD da kungiyoyin da take da alaka da su da kuma sauran kungiyoyi irin su Tarayyar Turai da Turkic Council da kuma Kungiyar Tarayyar Afirka," ta kammala.