Uwargidan shugaban kasar Turkiyya Emine Erdogan ta ziyarci wurin baje kolin nau'in abincin Anatoliya "Culinary Journey to Anatolian Centenary Flavours", tare da matan shugabannin da suka halarci taron diflomasiyya na Antalya.
A karo na uku, taron ya tattaro shugabannin kasashe da gwamnatoci da ministoci da jami’an diflomasiyya da ‘yan kasuwa da malamai, da masu fikirai, inda aka gudanar da ƙananan taruka a ɓangarori daban-daban da nune-nune da suka kunshi batutuwa da dama.
Yayin da aka shiga rana ta biyu ta taron a ranar Asabar, an gudanar da bikin baje kolin nau'ukan abincin Anatoliya "Tafiya zuwa Anatolian Flavours" inda aka ba da sarari ga mahalarta don kashe ƙwarƙwatar idonsu wajen ganin irin aikin hannu na saƙe-saƙe da ɗinkuna na yankin.
Uwargidan shugaban kasar Turkiyya ta zagaya a wajen bikin baje kolin tare da tsohuwar shugabar kasar Croatia Kolinda Grabar Kitarović da uwargidan firaministan Jamhuriyar Cyprus ta Arewa (TRNC) Zerrin Ustel da uwargidan shugaban TRNC Sibel Tatar da Ministar hulda da kasa da kasa da hadin gwiwa ta Afirka ta Kudu Grace Naledi Mandisa Pandor, da matar shugaban kasar Serbia Tamara Vucic.
Uwargidan shugaban kasa da jami’an da suka raka ta sun yi wa baƙi bayanai game da tufafi da kayan ado na al’adun gargajiya waɗanda aka ƙawata da launuka.
Bakin sun kuma ziyarci rumfunan da suka baje kolin kayayyakin da ke dauke da takardar shaidar kasa daga Tarayyar Turai, yayin da uwargidan shugaban kasar Turkiyya ta raka su.
An gudanar da mu'amaloli sosai a taron diflomasiyya na Antalya, an kuma yi amfani da damar hakan wajen musayar al'adu.