Jakada na musamman ga Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Jean Henri Todt ya taya uwargidan Shugaban Turkiyya Emine Erdogan murna kan "muhimmiyar rawar da take takawa" a shirinta na Kawar Da Datti baki daya wato Zero Waste Project.
Emine Erdogan ta karbi bakuncin Mista Todt ne a ranar Litinin, wanda ya je Istanbul don yin bikin Ranar Birane ta Duniya da za a yi ranar 31 ga watan Oktoba a katafaren ginin Vahdettin Mansion da ke birnin Istanbul.
A yayin tattaunawarsu, Todt ya yaba wa gwamnatin Turkiyya a kan yakin da take yi da zubar da shara barkatai a fadin duniya tare da taya Uwargidan Erdogan murna kan muhimmiyar rawar da take takawa wajen tabbatar da kawar da datti.
Todt ya bayyana muhimmancin inganta tsarin sufuri da sabunta abubuwa da kuma samar da tsari mai kyau ga masu tafiyar kafa a birane domin rage afkuwar hadurra da inganta kiyaye ka'idojin tituna da kuma habaka tsarin sabunta abubuwa don kyautata tattalin arziki.
Uwargidan Shugaban Turkiyyan ta yi bayani kan tsarin a yayin ganawar, inda ta fayyace cewa gwamnati, a karkashin shugabancin mijinta, Shugaba Revep Tayyip Erdogan, ta samu gagarumar nasarar rage afkuwar hadurra ta hanyar gina manyan tituna da kuma kokarin gyara su a kai akai.
"Na yi amanna za mu samu nasarar samar da birane masu dadin zama idan muna aiko tare," a cewar Uwargida Emine Erdogan.
Uwargidan Erdogan ta kuma yada bayani kan ganawar tasu a shafinta na sada zumunta, inda ta yi magana a kan tattaunawar da suka yi musamman ta shirin "Zero Vision", wanda yake kama da shirin kawar da shara baki daya.