Mai Dakin Shugaban Kasar Turkiyya Emine Erdogan ta gana da Sheikha Moza bint Nasser, shugabar Asusun Ilimi na Education Above All da ke Qatar don tattauna matakan da za a dauka bayan taron nuna goyon baya ga Falasdinu mai taken "One Heart for Palestine".
Emine Erdogan da ta raka Shugaba Recep Tayyip Erdogan zuwa Babban Taron Turkiyya-Qatar Karo na Tara da Taron Hadin Kan Kasashen Gulf Karo na 44 da aka gudanar a Doha, Emine Erdogan ta samu tarba daga Shaikha Hind bint Hamad Al-Thani a ranar Talatar nan, wadda ita ce Mataimakiyar Shugabar Asusun kuma kanwar Sarkin Qatar.
Emine Erdogan ta gana da Shaikha Moza bint Nasser a Gidauniyar Qatar don tattaunawa kan kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza da matakan da ya kamata a dauka don tsagaita wuta da wanzar da zaman lafiya, da kuma yadda za a kai kayan jinƙai zuwa Gaza.
Matan shugabannin kasashen biyu sun kuma yi nazari kan sakamakon Taron Matan Shugabanni don Falasdinu inda suka yi kiran hadin gwiwa na samar da zaman lafiya a duniya.
Emine Erdogan ta kuma yi tsokaci kan matakan da za a dauka karkashin Shirin Gwagwarmaya, wanda ya biyo bayan taron nuna goyon baya ga Falasdinu da ta karbi bakuncin gudanarwa a ofishinta na Fadar Dolmabace da ke Istanbul.
"Kan batun taron 'One Heart for Paletine', mun hada kai waje guda har sai an kawo ƙarshen hare-haren zalunci da Isra'ila ke kaiwa Gaza da kuma samar da dauwamammen zaman lafiya a yankin.
Game da hakan, mun yi musayar ra'ayoyi kan taruka na nan gaba inda za mu hade muryoyinmu tare da matan sauran shugabannin kasashe don Falasdinawan da ba su aikata laifin komai ba," in ji ta.
Mai dakin shugaban na Turkiyya ta shafinta na X ta kuma bayyana cewa "Za mu ci gaba da ƙudirinmu na hadi kai waje guda don sake gina yankin Gaza da aka rusa a yau.
A matsayin na 'yan adam, akwai bashin yaran Falasdinawa kawunanmu. Ina godiya ga SHaikha Moza bint Nasser saboda goyon baya da karrama mu da ta yi."
'Taron nuna goyon bayan Falasdinu'
Uwargidan Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta karbi bakuncin taron 'One Heart for Paletine' ina tare da sauran matan shugabannin wasu kasashe a wani bangare na kokarin da Turkiyya ke yi game da yakin da ake ci gaba da yi a Gaza.
A karshen taron na ranar Talata, Emine Erdogan ta zaga Gidauniyar Qatar tare da Shaikha Moza inda ta sanya hannu kan littafin maziyarta na musamman da suka je wajen.
A baya a ranar 15 ga Nuwamba a wajen Taron 'One Heart for Paletine', Emine Erdogan ta bayyana cewa "Mun bayyana yadda ƙawanya ga Gaza ya janyo rikicin jin kai a yankin, wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma ya hana fararen hula samun muhimman bukatu na rayuwa, kuma hakan take hakkokin ɗan'adam ne.
Tun bakwai ga Oktoba, an kashe mutane sama da 11,000 mafi yawan su mata da yara kanana a Gaza, wanda wannan daya daga cikin manyan take dokokin kasa da kasa ne.
Akwai bukatar a dauki matakin gaggawa don tabbatar da ba a cutar da mata masu juna biyu, yara, jarirai da marasa lafiya da ke fuskantar barazanar kisa ba a yanayi na rashin tausayi da imani."
Isra'ila ta dawo da kai hare-hare Gaza a ranar 1 ga Disamba, mako guda bayan tsagaita wutar da suka kulla da Hamas.
A kalla Falasdinawa 15,899 ne suka mutu inda sama da 42,000 suka jikkata sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza wanda ta fara tun bakwai ga Oktoba bayan harin kan iyaka da Hamas ta kai mata.
Alkaluman da aka bayyana sun bayyana mutuwar 'yan kasar Isra'ila 1,200 sakamakon hare-haren Hamas.