Erdogan

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa a ranar 14 ga Mayu al’ummar kasar za su bai wa kasashen Yammacin Duniya da ba sa kaunar sa amsar da ta dace da su.

“Turkiyya za ta aike da sakon da ya dace ga Yammacin Duniya ta hanyar zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki da za a gudanar, wanda ba Yammacin Duniya kadai ke bibiya ba, har ma da kasashen Musulmai” in ji Shugaba Erdogan.

A wata tattaunawa ta kafar talabijin da aka yi da shi, Erdogan ya ce “Yammacin Duniya na da wani shiri game da Turkiyya. Kuna kallon halin da ake ciki a yanzu haka.

Mece ce hikimar tafiyar shugaban Faransa Emmanuel Macron zuwa China? Wane hali alakar kasarsa da ta Faransa da Amurka ke ciki? Me ya sa Macron ya tafi China?”

Da yake tabo batun cewar sakamakon kuri’ar jin ra’ayin jama’a ya bayyana shugabar masu ra’ayin rikau ta Faransa Marine Le Pen za ta kayar da Macron idan za a gudanar da zaben shugaban kasa a yau.

Ya ce “Le Pen na gaba da shi Macron… Ta yaya hakan ta faru? Kenan akwai sauyi a sakamakon da aka samu.”

Erdogan ya kuma jaddada cewar kasashen Yamma ba sa kaunar sa, kuma a ranar 14 ga Mayu jama’ar Turkiyya za su ba shi cikakkiyar amsar da ta dace da su.

Ya ci gaba da cewa “Turkiyya za ta bayar da sakon da ya dace ga Yammacin Duniya a ranar zabe.

Wannan kasar ba ta kallon me Yammacin Duniya ka fada, ko a bangaren yaki da ta’addanci ko a bangaren dabbaka manufofin cigaban tattalin arziki.”

AA