Shirin "The Zero Waste" ne shirin Turkiyya na kare muhalli mafi girma a tarihin Turkiyya na shekaru dari, in ji Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun. / Photo: AA 

Hadin kai da goyon bayan kasa da kasa zai kawo nasara ga shirin kare muhalli na Turkiyya mai taken "Zero Waste Project", wani babban shirin kare muhalli, in ji Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun.

Shirin 'The Zero Waste Project', wani mataki da ke nuna yadda Turkiyya ke jagorantar diplomasiyyar kare muhalli da yaki da illolin sauyin yanayi, zai habaka ta hanyar goyon baya da hadin kan kasashen duniya." in ji Altun a ranar Litinin, a wajen wata tattaunawa a yayin halartar taron sauyin yanayi na COP29 a Azerbaijan.

Ta hanyar sadarwar bidiyo. Altun ya yi jawabi ga mahalarta taron, wanda sashen sadarwar ya shirya da ya mayar da hankali kan "kyakkyawar sadarwa a duniyar da ke fama da rikicin sauyin yanayi."

Ya yi karin haske game da burin Turkiyya na daina fitar da burbatacciyar iskar carbon nan da 2053, yana mai nuni ga irin gudunmawar da kasar ke bayarwa, duk da karancin fitar da iskar carbon da take yi a duniya.

"Duk da Turkiyya na fitar da kashi 1 na iskar carbon a duniya, ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Sauyin Yanayi ta Paris a ranar 6 ga Oktoba, 2021, a matsayin mambar kasa da kasa," in ji Altun.

Shirin kare muhalli na Turkiyya, wanda mai dakin shugaban kasar Emine Erdogan ke jagoranta, ya samu karbuwa a matakin kasa da kasa, in ji Fahrettin Altun, yana kara da cewa "Shirin 'The Zero Waste"'ne shirin Turkiyya na kare muhalli mafi girma a tarihin Turkiyya na shekaru dari."

Ya ce "Turkiyya ta mayar da hankali wajen cim ma manufofin samar da makamashi mai sabuntuwa ta hanyar kara zuba jari a bangaren, tna mai fatan samu daidaiton habaka a bangarorin muhalli, tattalin arziki da zamantakewa."

Ya yi karin haske cewa cigaba mai dorewa na da laka ta kusa da tsarin kasa, batutuwan tattalina arziki da zaizayar kasa, tare da batutuwan zamantakewa, inda ya kuma bayyana muhimmancin da Turkiyya ta bayar na gina al'ummar da ta damu da kare muhalli, da kuma fahimtar darajar duniya.

TRT World