Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya dauki gagarumin mataki na magance matsalar yada labaran karya, ciki har da samar da sashe na yaki da irin wadannan labarai da kuma "mujalla kan yaki da labaran karya." / Hoto: AA

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya caccaki kamfanin dillancin labarai na Reuters bisa watsa labaran karya game da dan Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Fahrettin Altun ranar Litinin ya bayyana labaran da kamfanin ya watsa a kan Bilal Erdogan a matsayin marasa tushe, yana mai cewa Reuters ya gaza tantance sahihancin labarin da ke cewa Shugaba Erdogan da dansa Bilal suna da hannu wurin karbar na-goro a hannun wani kamfanin Sweden ko kuma ma suna sane da hakan.

"Wannan labarin karya, wanda bayanansa suke cin karo da juna, ya bayyana karara cewa babu kanshin gaskiya a cikinsa, kuma ba a bi ginshikin tsarin aikin jarida ko miskala-zarratan wajen wallafa shi ba, don haka ya kamata a yi misali da shi wurin koyar da aikin jarida," in ji Altun.

Altun ya ambato wasu sassa na labarin domin ya yi karin haske game da batun: "Hakika, ba a bayar da na-goro ba, a cewar bayanin da wasu mutane suka mika wa hukumomi wadanda kuma Reuters ta tantance su.

A kashin gaskiya, kamfanin Dignita Systems AB na kasar Sweden ya bar aikin ba zato ba tsammani a shekarar da ta wuce, a cewar wasu mutum biyu da ke da masaniya game da batun da kuma bayanan daga kamfani da Reuters ya gani.

'Kirkirarren labari'

"Reuters ya gaza tabbatarwa karara cewa Shugaba Erdogan da dansa Bilal suna sane ko kuma sun karbi na-goro daga kamfanin Dignita," kamar yadda Altun ya ambato Reuters yana cewa, inda ya ce labarin "kirkirarre ne."

Kazalika Altun ya ce an wallafa labarin ne da wata manufa domin kuwa an buga shi ne yayin da ake shirin gudanar da taron shugabannin NATO da za a yi a Lithuania a makonnin da ke tafe.

"Muna so mu bayyana karara cewa wannan labarin, wanda masu adawa da Turkiyya suka dauki nauyinsa domin muzanta ta, ba zai taba yin tasiri kan manufar Turkiyya ba," in ji shi.

"Mun yi tir da Reuters bisa watsa labaran karya, lamarin da ya jaddada aniyarmu ta bayar da muhimmanci wajen yaki da labaran kanzon-kurege," a cewar Fahrettin Altun.

Ma'aikatar Sadarwa ta Turkiyya, karkashin Altun, ta dauki gagarumin mataki na magance matsalar yada labaran karya, ciki har da samar da sashe na yaki da irin wadannan labarai da kuma "mujalla kan yaki da labaran karya."

TRT World