Altun ya jaddada cewa jajircewa wajen tsare gaskiya na cikin manyan dalilan da suka sa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karbu a fagen siyasa tun da ya soma ta. / Hoto: AA

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya ce labaran karya sun zama babbar matsala a Turkiyya da ma duniya baki daya kuma suna watsuwa tamkar annoba.

"Muna fuskantar labaran kanzon-kurege sosai... kuma suna barazana ga dimokuradiyya da zaman lafiya da kuma gaskiya," in ji Altun a hirar da wani dan jarida ya yi da shi a shafinsa na YouTube.

Altun ya ce bayyana hakikanin gaskiyar lamura ne kadai babban abin da zai kubutar da jama'a daga sharrin labaran karya, yana mai cewa hakan zai wanzar da zaman lafiyar al'umma da kare mulkin dimokuradiyya.

Mutanen Turkiyya sun fi fuskantar barazanar labaran kanzon-kurege a soshiyal midiya idan aka kwatanta da dukkan kasashen duniya, a cewar Altun.

"Dalili kuwa shi ne Turkiyya ta dauki hanya mai kyau. Don haka ake watsa labaran karya ta hanyar fakewa da wasu hanyoyi na hana 'yan kasar yin zabin da ya dace da su. Ko da yake muna fama da labaran karya a yau, mun san cewa a baya ma hakan ya faru; lokacin da Turkiyya take samun sauyi na bunkasa rayuwarta da tarihinta.”

"Abin takaici shi ne, tarihinmu yana da alaka da juye-juyen mulki da yin katsalandan a harkokin siyasa da dimokuradiyya. Idan ka yi nazari kan wadannan abubuwa, za ka ga cewa cike suke da watsuwar labaran karya - kafin a yi juyin mulki."

Altun ya jaddada cewa jajircewa wajen tsare gaskiya na cikin manyan dalilan da suka sa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya karbu a fagen siyasa tun da ya soma ta.

TRT World