Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya yi kira ga manyan kasashen duniya su hada kai domin murkushe kungiyar 'yan ta'dda ta Fethullah Terrorist Organisation (FETO), wadda ta yi yunkurin juyin mulki da bai yi nasara ba a kasar ranar 15 ga watan Yuli shekaru bakwai da suka wuce.
“FETO kungiyar 'yan ta'adda ce ta duniya, kuma kamar yadda ake yaki da kungiyoyin ta'addanci, ya kamata kasashen duniya su hada kai domin murkushe ta,” in ji Altun a wani sakon bidiyo da ya gabatar a wata tattaunawa da aka yi kai-tsaye kuma a lokaci daya a biranen Stockholm na Sweden da Berlin na Jamus.
Tattaunawar, mai taken Nasarar Dimokuradiyyar Turkiyya ta 15 ga watan Yuli, wadda Hukumar Sadarwa ta kasar ta dauki nauyin gabatarwa, ta mayar da hankali ne wajen wanzar da Dimokuradiyya da tunawa da ranar Hadin Kan Kasa.
Turkiyya tana tunawa da sadaukarwar da fararen-hula 250 da aka kashe yayin kare dimokuradiyyar kasar suka yi a yayin da suka yi tsayin-daka don murkushe kungiyar wasu 'yan tawayen sojoji da ke samun goyon bayan 'yan ta'adda na FETO.
Dakaru akalla 2,000 ne suka jikkata lokacin da suka yi biyayya ga umarnin Shugaba Recep Tayyip Erdogan domin murkushe masu yunkurin juyin mulkin, wadanda suka zo a cikin motoci masu sulke sannan suka bude wuta da manyan bindigogi kan 'yan kasarsu.
“A matsayinmu na Hukumar Sadarwa, muna bayar da labarin abin da ya faru ranar 15 ga watan Yuli da kuma manyan laifukan FETO a cikin Turkiyya da kasashen ketare,” a cewar Altun.
Ya kara da cewar Turkiyya ba za ta bari 'yan ta'adda da masu goyon bayansu su yi nasara ba.
“Ba za mu bari FETO, wadanda ke aiki kafada da kafada da sauran 'yan ta'adda, da kuma suka so cimma burinsu ta haramtattun hanyoyi, ciki har da da amfani da sojoji, su yi nasara ba,” in ji shi.
Ba tare da ya ambaci sunan wata kasa ba, ya nuna rashin jin dadi game da “gum da baki” da wasu kasashe suka yi kan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba.
“Ko da yake kasar Turkiyya ta yi nasarar wuce wannan mataki da aka gwada rayuwarta da 'yancinta na zama kasa, kasashe da dama da suke ikirarin kasancewa abokan Turkiyya, wadanda suka ce su ne suka mallaki dimokuradiyya da 'yancin dan adam, abin takaici sun gaza cin jarrabawar da aka yi musu a waccan ranar,” a cewarsa.
Altun ya ce Turkiyya ta dade tana yin bakin kokarinta wajen ganin ta kawar da FETO ta kowacce kusurwa.