Altun ya jaddada cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta aika da sako na diflomasiyya ga Amurka da Jamus da Netherlands da kuma Birtaniya game da yadda 'yan kasar Turkiyya suke shan wahala wurin samun bizar Schengen da ta kasar Amurka.  / Hoto: AA

Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya ce “abu ne mai matukar muhimmanci a samu kwakkwaran sakamako” a yakin da ake yi da ta'addanci idan ana so kasarsa ta ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Bashar al Assad na kasar Syria.

“PKK/YPG/PYD da dakarun Syrian Democratic Forces da ke alaka da ita suna yin barazana ga dorewar tsaron kasarmu. Don haka yana da matukar muhimmanci a samu kwararan sakamako wajen kawar da ta'addanci,” in ji Fahrettin Altun a kebantacciyar tattaunawa da ya yi da jaridar Daily Sabah ta Turkiyya.

Da yake tsokaci game da barazanar da kungiyoyin 'yan ta'adda suke yi game da wanzuwa da kuma hadin kan kasar Syria, Altun ya ce Turkiyya na sa rai gwamnatin Assad ta dauki matakai bisa la'akari da abubuwan da ke faruwa a zahiri.

“Muna ci gaba da bin tsarin tattaunawa da gwamnatin ta hanyoyi hudu ba tare da mun gindaya sharadi ba kuma cikin da zuciya-daya. Ya kamata gwanatin Syria ta daui mataki irin namu idan ana son samun sakamako mai kyau," kamar yadda Altun ya bayyana.

Ya ce kasashen biyu suna matakin farko na tattaunawa kan yadda alakarsu za ta kasance.

Altun ya ce janye dakarun tsaron Turkiyya daga Syria a wannan lokaci ba zai zama wani abu mai alfanu ba, yana mai bayyana cewa zaman dakarun a Syria wani tabbaci ne na tabbatar da tsaronta.

Da yake magana game da matsalolin 'yan gudun hijira, ya ce Ankara zai mayar da hankali wurin ganin sun koma gida domin radin kansu cikin aminci da daraja tare da kyautata tsarin siyasa – wanda gwamnatin kasar ta yi wa kutse.

A 2016, Ankara ta kaddamar da hare-hare uku da suka yi nasara kan 'yan ta'adda a iyakarta da Syria ta arewacin kasar domin hana kafa wani dandali na 'yan ta'adda da kuma tabbatar da sake tsugunar da mutane cikin kwanciyar hankali: Euphrates Shield (2016), Olive Branch (2018) da Peace Spring (2019).

A shekaru fiye da 35 da ta shafe tana ta'addanci a kan Turkiyya, kungiyar PKK – wadda Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai suka ayyana a matsayin kungiyar ta'addanci – ta kashe fiye da mutum 40,000, ciki har da mata, kananan yara da jarirai. Tana da reshe a Syria mai suna YPG.

Dangantakar Ankara da makwabtanta

Da aka tambaye shi game da tsarin hulda da kasashen wajen na Ankara, Altun ya ce “ci-gaba shi ne kashin-bayan alakar Turkiyya da kasashen waje.”

Ankara ta shiga sulhu da kasashe irin su Armenia, Israila, Masar, Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya inda suka warware tsamin da dangantakarsu ta yi a baya.

"A yau muna neman karfafa abotarmu da kuma neman mafita game da abubuwan da ke tayar da jijiyoyin wuya,” in ji shi.

Ya ce Turkiyya za ta ci gaba da kyautata dangantaka da makwabtanta bisa dokokin kasashen duniya yayin da kuma take kare hakkoki da muradunta.

Da yake tsokaci kan ziyarar da shugaba Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai wasu kasashen yankin Gulf makon jiya, Altun ya ce Turkiyya tana da dadaddiyar alaka ta tarihi da al'ada da kawayenta na yankin.

“Mun ga yadda huldar cinikayyarmu da yankin Gulf ta karu fiye da sau 12 a shekara 200, inda ta kai ta $22 bn,” in ji shi, yana mai karawa da cewa ziyarar ta bude wasu sabbin hanyoyi na hadin kai tsakanin Turkiyya da yankin Gulf.

Batun biza

Altun ya yi magana game da wahalar da 'yan kasar Turkiyya suke sha wajen samun bizar Schengen da ta Amurka, yana mai cewa cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta aika da sako na diflomasiyya ga Amurka da Jamus da Netherlands da kuma Birtaniya game da hakan.

“Idan ka lura za ka ga cewa wanna matsala ta biza tana ci gaba da karuwa,” in ji shi.

“Ana ci gaba da gaya wa hukumomin kasashen Yamma wannan matsala ta biza, kuma za mu ci gaba da neman mafita game da batun.”

A 2022, an hana kashi 15 na 'yan kasar Turkiyya bizar Schengen, sannan adadin ya karu zuwa kashi 50 a wannan shekarar.

AA