Shekara 30 da suka gabata ne aka kashe sama da mutum 30 a wani kauye da ke gabashin Turkiyya ta mummunar hanyar kai hari da ‘yan ta’addar PKK suka yi. Har yanzu ba a manta da wannan ta’annati ba.
A ranar 5 ga watan Yuli 1993, ‘yan ta’addar PKK dauke da muggan makamai suka kai hari kauyen Basbaglar da ke lardin Erzincan. Sun kashe kauyawa 33 tare da kone gidaje da kayayyakin jama’ar kauyen.
“Yan uwa da abokan wadanda aka kashe a wannan bakar rana sun ki yarda su manta da tunawa da makusantansu.
A kowacce shekara, mutane da dama na ziyartar gidan adana kayan tarihi na Basbaglar don ziyartar wadanda aka kashe din.
Gidan adana kayan tarihin da aka bude a 2013, na dauke da hotuna da tufafi da takalma da wasu kayan amfani na mutanen.
A kowacce ranar 5 ga Yuli, ana gudanar da tarukan tunawa da kisan gillar a gidan adana kayan tarihin, wajen da makusantan wadanda aka kashe suka sanar da junansu irin balahirar da ta afku tare da bayyana bakin cikin rasa ‘yan uwansu.
Kungiyar PKK da Turkiyya. wadda Amurka da Tarayyar Turai suka bayyana a matsayin kungiyar ta’adda ta kasa da kasa, ta kaddamar da hare-haren tare da kashe fararen hula da jami’an tsaro da dama a Turkiyya.
Tare da reshenta na Siriya da ake kira YPG, kungiyar na nufar fararen hula da jami’an tsaron Turkiyya da cikin kasar da kuma Siriya.
A yayin da aka haramta ayyukan kungiyar, gwamnatin Ankara kuma ta bayyanawa duniya damuwarta tsawon shekaru, magoya bayan PKK na ci gaba da taruka da hada kudade a kasashen Turai da suka hada da Swidin.
A lokacin da Turkiyya ke tunawa da cika shekara 30 da wannan kisan kare dangi na Basbaglar, bari mu kalli abun da ya faru a wannan rana.
Bakar rana
A ranar 5 ga Yulin 1993 aka rusa kwanciyar hankalin kauyen Basbaglar, a lokacin da ‘yan ta’addar PKK kusan su 100 dauke da muggan makamai suka kai hari karamin kauyen.
A cikin sama da awa guda, ‘yan ta’addar PKK sun zalunci jama’ar kauyen, suka jera su tare da karkashe su a tsakiyar garin, sannan suka kona wasu da ransu. Har mata ma ba su bari ba.
An shirya kai harin sosai, saboda ‘yan ta’addar PKK sun katse layukan sadarwa da lantarki na kauyen Basbaglar daga layukan kasar.
Babu wanda ya san me ya faru har sai da jama’ar kauyuka makota suka je gane wa idanuwansu.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ‘yan ta’addar na PKK sun fara da yada farfagandarsu ta neman ballewa daga kasar Turkiyya ta hanyar karanta manufofinsu da rera wakokinsu, sannan suka fara harbe mutanen kauyen.
Babbar manufar PKK ita ce su assasa gaba da rikicin mazhabanci a tsakanin jama’ar yankunan da suke zaman lafiya da juna tsawon daruruwan shekaru.
Bayan kashe mutane da dama, ‘yan ta’addar na PKK sun kona gidaje akalla 190 da masallaci da cibiyar taro da ma makaranta.
Bayan shekara guda, kungiyar ta kashe sojoji 33 da ba sa dauke da makamai a Bingol. PKK ce ta dauki alhakin wannan mummunan kisa.
An ci gaba da aikata ta’addanci
PKK da ta jima tana kai hare-haren ta’addanci tun 1980, ta dauki nauyin hare-haren kunar bakin wake da dama.
Ta kafa sansani a kasar Iraki mai makotaka da Turkiyya, inda take yawo ba tare da wata kyara ba sakamakon kawar da gwamnatin Saddam Hussain da Amurka ta yi a kasar.
Haka zalika, PKK da YPG sun hade waje guda a Siriya. Amurka na ci gaba da kallon YPG a matsayin kawa wajen yaki da Daesh duk da damuwar da Ankara ke nunawa.
Amma a ‘yan shekarun nan PKK na guduwa saboda yadda Turkiyya ta samar da manyan makamai da suka hada da jiragen yaki marasa matuka da ke iya tsinkayen mambobinsu a lokacin da suke tafiya, musamman ma a arewacin Iraki.