Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi kira ga Amurka da ta gano "dan ta'addar" da ya kai hari Gidan Turkiyya da ke New York ta kuma "yi abin da ya kamata a kai."
"A Turai, (kungiyar ta'addanci) ta PKK tana ganin abubuwa sun fara lalacewa, sai suka fara kai hari kan masu kada kuri'a. Me ya rage, sun kai hari Gidan Turkiyya a Amurka, wanda ba shi da nisa da inda ginin Majalisar Dinkin Duniya yake a Amurkan, tare da farfasa tagogin wajen," Erdogan.
"A yanzu za mu gaya wa hukumomin Amurka da dakarun tsaro cewa, 'Dole a nemo dan ta'addar nan da gaggawa, kuma dole ku yi abin da ya dace da wuri," ya fada a wajen wani taro a Istanbul.
Ya ce Gidan Turkiyyan yana karkashin amanar hukumomin Amurka ne.
"Dole ku gano waye dan ta'addar da ya fasa tagogi a Gidan Turkiyya ta hanyar amfani da wani karfe."
MDD ta yi Allah wadai
Majalisar Dinkin Duniya ta yi tur da lamarin. A wata sanarwa, ta yi kira ga hukumomi da su gano wadanda suka aikata hakan.
Da safiyar ranar Litinin, wasu bata gari suka far wa Gidan Turkiya inda can ne ake gudanar da harkokin diflomasiyyar Turkiyyan a New York.
'Yan Sanda birnin New York sun zagaye ginin bayan faruwar lamarin, kuma tuni aka kaddamar da bincike.
Maharin ya ragargaza tagogin ne da misalin karfe 3.14 na asubahin ranar Litinin, kamar yadda babban jami'in diflomasiyya na karamin ofishin jakadancin Turkiyya Reyhan Ozgurya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
Lamarin bai shafi zabe zagaye na biyu da 'yan Turkiyya mazauna New York ke gudanarwa ba a Gidan Turkiyyan, in ji Ozgur.
Ozgur ya ce ba wanda aka ji wa rauni amma an lalata tagogi da kofofi 12.
Ya ce maharin, wanda ba a gano ko waye shi ba har yanzu, ya bar karfen a wajen.