Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi gargadin cewa sakamakon da za a gani na hare-haren ƙasa da Isra'ila ke kaiwa Lebanon zai sha bamban da irin abin da ya faru a baya.
"Sakamakon farmakin kasa a Lebanon ba zai yi kama da na wanda Isra'ila ta sha yi aa baya ba," in ji Erdogan a yayin jawabin bude taron shekara karo na 3 na majalisar dokokin Turkiyya na tsawon wa'adi na 28 na majalisar, sa'o'i kadan bayan sojojin Isra'ila da tankunan yaki suka fara shiga makwabciyar kasar Lebanon.
Da yake Allah wadai da ayyukan Isra'ila a yankin, Erdogan yi tur da "kisan kare dangi" da aka kwashe kusan shekara guda ana yi a Gaza da kuma hare-haren ta'addanci na baya-bayan nan da aka kai a kasar Labanon, yana mai cewa gwamnatin Isra'ila na kokarin harzuka kasashen yankin da jefa su cikin rikici.
"A mafarkinta na yaudarar kai da take yi na 'ƙwato ƙasarta ta alkawari", Isra'ila za ta fara hanƙoron ƙasarmu ta gado Turkiyya bayan Falasdinu da Labanon," ya yi gargadi.
Da yake jaddada girman al'amarin, ya ce: "Mamaya da ta'addanci da fin ƙarfi suna nan kusa da mu. Ba da ƙasa mai bin tafarkin doka muke gaba da gaba ba, ƙasa ce ta masu shan jini da kisa duk da sunan mamaya."
Erdoğan ya ce, "Muguntar Isra'ila ba ta ƙyale Turkiyya ba," Erdogan ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta yi adawa da wannan ta'addanci da dukkan hanyoyin da za mu iya don kare al'ummar kasar da 'yancin kai.