Shugaban kasar Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya (TRNC) Ersin Tatar ya ce akwai alaka ta musamman tsakanin kasarsa da Turkiyya. Hoto/AA

Shugaban kasar Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya (TRNC) ya yi maraba da shirin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na zuwa kasarsa a ziyararsa ta farko a kasashen waje bayan ya soma sabon wa'adin mulki.

"Ziyarar da Shugaba Erdogan zai kawo nan ta nuna muhimmanci da kimar da Turkiyya ke kallon TRNC a yayin da duniya ta sanya mana takunkumi da nuna mana wariya," in ji shugaban kasar TRNC Ersin Tatar a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ofishinsa da ke Lefkosa, babban birnin kasar.

A yayin da yake jaddada muhimmancin ziyarar da Erdogan zai kai ranar Litinin, Tatar ya ce balaguron zai aike da sako ga duniya cewa Arewacin Cyprus na Jamhuriyar Turkiyya, TRNC "kasa ce."

Kazalika ya jinjina wa Turkawa bisa sake zaben Erdogan a watan jiya, yana mai cewa nasarar ta nuna cewa al'ummar kasar suna goyon bayan tsare-tsarensa.

Ya kara da cewa Turkiyya da kasar Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya suna da alaka ta musamman, inda ya ce 'yan kasarsa suna kallon kansu a matsayin wani bangare na kasar Turkiyya.

Dangantaka ta musamman

A gefe gudan, Ministan Harkokin Wajen TRNC Tahsin Ertugruloglu ya ce ziyarar da Erdogan zai kai ta tabbatar da muhimmancin dangantaka ta musaman da ke tsakanin Turkiyya dakasar Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya.

A wata sanarwa da ya fitar, Ertugruloglu ya ce ziyarar “ta kara fito da jajircewa irin ta Jamhuriyar Turkiyya wajen kare 'yanci da kimar mutanen kasar Arewacin Cyprus ta Jamhuriyar Turkiyya da kuma bayar da goyon baya ga tsare-tsaren TRNC.”

Erdogan zai gana da Tatar da Firaiministan TRNC Unal Ustunel yayin ziyarar — irinta ta farko bayan an sake zabensa mako biyu da suka gabata, abin da ke nuna dadaddiyar dangantakar da ke tsakanin shugabannin kasashen Turkiyyoyin biyu.

Aana sa rai za su tattauna kan ci-gaban da ake samu a Gabashin Bahar Rum da kuma matakan da za a dauka kan bukatun Cyprus.

Erdogan ya sake yin nasara a zaben shugaban kasar bayan an kada kuri'a a zagaye na biyu ranar 28 ga watan Mayu, inda ya samu kashi 52.18, yayin da mutumin da ke hamayya da shi Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 47.82, a cewar sakamakon da hukumar zabe ta fitar.

AA