Za a ci gaba da wasannin neman gurbin shiga kofin duniya har zuwa Talata 11 ga Yuni. / Hoto: Reuters

Yayin da ƙasashen duniya ke wasannin neman cancantar shiga gasar kofin duniya ta FIFA ta 2026, a Afirka, inda aka yi wasanni 9 a ranar Alhamis, bayan an ɗage da wasa ɗaya tsakanin Nijar da Congo sakamakon saɓanin FIFA da Congo.

A zagayen farko, akwai jerin wasannin ranar Juma'a guda tara, baya ga wassanni tara da aka yi ranar Alhamis, su ma na zagayen farko, kasancewar an dakatar da wasan Nijar da Congo.

Wasannin Juma'a

A Juma'an nan, zuwa yanzu an buga wasanni shida a rukunonin D da G da I. Inda ya rage wasanni uku ciki har da zazzafan wasa tsakanin Nijeriya da Afirka ta Kudu, Maroko da Zambiya, da kuma Ivory Coast da Gabon.

Ga sakamakon wasannin zuwa yanzu:

Zimbabwe 0 - 2 Lesotho (Rukunin C)

Kenya 1 - 1 Burundi (Rukunin F)

Mozambique 2 - 1 Somalia (Rukunin G)

Uganda 1 - 0 Botswana (Rukunin G)

Madagascar 2 - 1 Comoros (Rukunin I)

Angola 1 - 0 Eswatini (Rukunin D)

A Juma'a da dare ne za a buga sauran wasanni uku na rukunonin C, E, da F.

Wasannin Alhamis

Tawagar Masar ta ci gaba da yin kurarin neman gurbin buga gasar Kofin Duniya, bayan da ta ci ƙwallaye biyu cikin mintuna 10 na farkon wasansu da tawagar Stallions ta Burkina Faso, wadda a ƙarshe ta samu ta rama ƙwallo guda aka tashi 2-1

Ɗan wasan gaba na Masar mai buga wa ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya, Mahmoud Ahmed Ibrahim Hassan, wanda ake wa laƙabi da Trézéguet shi ya ci ƙwallo biyu a minti na uku da na bakwai, kafin daga bisani Lassina Traore ya rama guda a minti na 56.

Ga yadda ta kaya a wassanin ranar Alhamis:

Malawi 3 - 1 Sao Tome and Principe (Rukunin H)

Guinea Bissau 0 - 0 Ethiopia (Rukunin A)

Mauritania 0 - 2 Sudan (Rukunin B)

Libya 2 - 1 Mauritius (Rukunin D)

Congo - Nijar [An ɗage] (Rukunin E)

Masar 2 - 1 Burkina Faso (Rukunin A)

Senegal 1 - 1 Congo DR (Rukunin B)

Benin 1 - 0 Rwanda (Rukunin C)

Aljeriya 1 - 2 Guinea (Rukunin G)

Mali 1 - 2 Ghana (Rukunin I)

Bayan kammala wasannin Juma'a, ƙasashen Afirka za su ci gaba da buga sauran wasannin neman cancantar shiga gasar kofin duniya na FIFA ta 2026 har zuwa Talata 11 ga watan Yuni.

Gasar kofin duniya na FIFA ta 2026 za ta gudana ne daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga Yulin 2026, a birane 16 da ke ƙasashen Canada, Mexico, da Amurka.

TRT Afrika