Hukumar Kula da Harkokin Kwallon Kafa a Duniya (FIFA) ta ce ta kaddamar da bincike kan korafin rashin da'a kan tawagar Zambiya a Gasar Kofin Duniya ta Mata, inda ta sha alwashin yin hukunci idan laifin ya tabbata.
FIFA ba ta yi karin bayani ba, sai dai wasu rahotanni sun ce batun ya shafi zargin da ake yi wa Koci Bruce Mwape na taba maman wata 'yar wasa.
"Mun karbi korafi kan tawagar mata ta kasar Zambiya kuma muna ci gaba da yin bincike kan batun," in ji mai magana da yawun FIFA.
"FIFA tana daukar zargin rashin da'a da muhimmanci sosai kuma ta gindaya tsari a fagen kwallon kafa ta yadda kowa zai iya mika mata korafinsa."
An fitar da Zambiya tun a matakin rukuni daga gasar wadda kasashen Australia da New Zealand ke karbar bakunci, kuma tawagar Zambiya ta koma gida.
Zargin cin zarafi a tawagar mata ta Zambiya ya bayyana ne a kafofin sada zumunta a bara, inda Hukumar Kula da Harkokin Kwallon Kafa ta Zambiya ta kaddamar da bincike.
A lokacin hukumar ta ce ta karbi korafi a hukumance, kuma "mun dauki korafin da muhimmanci," in ji hukumar.
An nada Koci Mwape ne a shekarar 2018, kuma an rika tambayarsa a-kai-a-kai kan batun yayin Gasar Kofin Duniya ta Mata.
Sai dai ya musanta zargin, inda ya ce "ba gaskiya ba ne" kuma ya yi watsi da batun cewa zai yi murabus.
Mai magana da yawun tawagar bai amsa sakon da aka aika masa a ranar Juma'a ba.
'Yan sanda a New Zealand, inda tawagar ta zauna yayin gasar, sun ce ba su karbi korafi kan batun ba.
Hukumar FIFA ta ce tana bincike zargin cin zarafi ne a cikin sirri.
"Idan aka samu wanda ya aikata laifi, FIFA tana daukar hukunci mai tsauri, ciki har da dakatar da mutum daga wasannin kwallon kafa har abada. Muna da irin wadannan matakai da muka taba dauka a baya," in ji FIFA.
Zambiya ta sha kashi a hannun Sifaniya da kuma Japan, kafin ta samu nasara ta farko a tarihin Gasar Kofin Duniya ta Mata, inda ta doke Costa Rica da ci 3-1.
A 'yan shekarun nan an samu labaran cin zarafi a tawagar mata ta kwallon kafa na kasashen Gabon da Haiti da Amurka da kuma Afghanistan.