Zambyia za ta shiga gasar kwallon kafa ta duniya ta mata a karon farko. Photo: Zambia WNT/Twitter

Daga Charles Mgbolu

Abin da kowa ke nema shi ne kambun kwallon kafar mata mafi girma, kuma wasu manarzarta na sa ido kan yadda tawagar kasashen Afirka za su nuna baiwarsu idan suka hadu da kasashen da suka fi iya murza leda a Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta FIFA.

Kasashen Nijeriya da Afirka ta Kudu za su yi tarayya ne da kasashe sabbin shiga gasar, wato Moroko da Zambiya, wajen neman daukaka.

Za a fara gasar ne daga ranar 20 ga watan Yuli zuwa 20 ga watan Agusta, a filayen wasan da ke birane a kasar Austireliya da New Zealand.

Gasar da za a yi a shekarar 2023 ita ce gasar kwallon kafar mata ta duniya ta tara, kuma kasashe 33 ne za su fafata.

Tambayar da ke bakin manazarta da magoya baya ita ce: akwai wata tawagar Afirka da za ta kai har karshen gasar?

Fata da kuma nuna damuwa

Afirka ta samu wakilci mai karfi a gasar kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2022, inda Morocco ta bai wa duniya mamaki ta zo ta hudu a gasar da aka yi a Qatar.

Keftin din Super Falcons din Nijeriya Asisat Oshoala ce daya daga cikin kwararrun 'yan wasan da za su murza leda a gasar Photo: Falcons/Twitter

Galibin kasashen za su taka rawar gani, amma da walakin.

"Yana da wuya a iya hasashe a yanzu. Kasashen suna da gwanaye da kuma yiwuwar iya taka rawar gani; sai dai kuma galibinsu na fama da matsaloli masu yawa gabannin gasar.

"Kuma ina ganin wannan zai yi mummunan tasiri kan wasanninsu idan an fara," kamar yadda Victor Okhani, wani ma'aikacin gidan rediyo mai labaran wasanni a Lagos, ya shaida wa TRT Afrika.

Nijeriya ta shiga duk gasar kwallon kafa ta mata ta duniya da aka yi tun shekarar 1991. Hoto: Demehin Blessing/Twitter

Damuwarsa ka iya kasancewa mai tushe. Nijeriya, alal misali, ta sami kanta cikin makonni masu matsala yayin da gasar ke karatowa inda kocin Super Falcons ya nuna damuwa cewa tawagar ba ta samu isashen lokacin sajewa da juna a sansanin shirya wa gasar ba kafin karawarsu da Canada ranar 21 ga watan Yuli.

Kyakkyawan fata

"Wannan na da muhimmanci ga tawagar kasashe domin yana taimaka musu wajen fahimtar aiki da juna," kamar yadda Okhani ya bayyana.

Tawagar mata ta Morocco za ta shiga gasar cin kofin duniya a karon farko . Hoto: FRMF Morocco/Twitter

Yana da kwarin gwiwa a bayanin da ya yi a nazarin da ya yi kan ikon ‘yan wasan Moroko wajen iya bin sawun takwarorinsu maza a gasar mafi girma ta kwallon kafa.

"Ina da kwarin gwiwa game da Moroko. Duk da cewa ba su taba kai wa wannan matakin ba a kwallon kafa, amma sun sami inganci a yanayin murza ledarsu sosai," in ji Okhani.

"Bugu da kari, sun samu horo mai kyau, kuma ba su samu ire-iren matsalolin rashin jituwa da rashin kyakkyawan shirin da wasu kasashen ke da su ba."

Wanann ne lokaci na biyu da Afirka ta Kudu ta shiga gasar cin kofin duniya ta mata. Hoto: Banyana Banyana/Twitter

Lotan Salapei, dan jaridar Kenya ya daga tutar fatansa ga tawagar Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu.

"Suna da kwarewa da kuma ‘yan baiwa masu tasowa da yawa a tawagar, kuma ina ga za su fito da daga cikin rukuninsu," in ji shi tare da farin cikin mutum mai kwarin gwiwa.

"Idan za su iya yin nasara a wasa daya su kuma tashi canjaras a sauran wasannin, to ina ganin za wuce matakin rukuni-rukuni."

Tsauni mai tsayi

Salapei yana damuwa game da Nijeriya duk da arzikin kwararru da tawagar kasar ke da shi.

"Na yi takaicin irin rukunin da suke ciki. Yana da matukar wahala. Moroko ma tana cikin rukuni mai wahala. Dole Nijeriya ta dogara da kwarewar kwararrun ‘yan wasan da suka cike tawagarta domin iya wucewa," in ji shi .

"Nijeriya tana da Asisa, wadda take wasa a Barcelona, tare da sauran ‘yan wasan masu baiwa, amma a gaskiya, za su bukaci wani abin al’ajabi kafin su tsira.

"Za su kara da Austireliya, wadda ke shaukin nasara kuma sun yi imanin cewa za su iya nuna wa duniya wani abu game da kwarewarsu, tare da Canada, kuma ka san kwarewar kasashen arewacin Amurka."

Zambiya za ta yi wasanta ta farko a gasar kwallon kafa ta mata ta duniya . Hoto: Zambiya WNT/Twitter

Zambiya ma tana da wani babban kalubale a gabanta. Wanan ne karon farko da kasar ke wasa a matakin wannan gasar, kuma dole su wuce Sfaniya da Japan, wadanda suka kasance zakarun shekarar 2011 da kasar da ta za yi ta biyu a shekarar 2015.

Amurka ta yi nasara a Gasar Cin Kofin Duniya ta mata a Faransa a shekarar 2019.

Rukunonin

Rukunin A: New Zealand (daya daga cikin kasashen masu karban baki) da Norway da Philippines da kuma Switzerland.

Rukunin B: Australia (daya daga cikin kasashen masu karban baki) da Ireland da Nijeriya da kuma Canada.

Rukunin C: Spain da Costa Rica da Zambia da kuma Japan.

Rukunin D: England da Haita da Denmark da kuma China.

Rukunin E: Amurka da Vietnam da Netherlands da kuma Portugal.

Rukunin F: Faransa da Jamaica da Brazil da kuma Panama

Rukunin G: Sweden da Afirka ta Kudu da Italiya da kuma Ajantina.

'Yan Tawagar Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu sun sami matsalar biyan kudi gabannin gasar. Hoto: Banyana Banyana/Twitter

Yayin da tawagar kakashen Afirka ke tafiya gasar ta duniya, masu sharhi da yawa sun ce za su iya taka rawar gani idan kasashensu da magoya bayansu suka ba su goyon bayan da suke bukata, yayin da su kuma suka yi iya kokarinsu wajen kishin kasa da son nahiyar.

TRT Afrika da abokan hulda