Nuna wariyar launin fata a harkokin kwallon kafa na neman ya zama ruwan dare a duniya, abin da masana ke cewa zai shafi fagen tamaula/ Hoto AP

Wariyar launin fatar da aka nuna wa dan wasan Real Madrid Vinicius Jr. a kwanakin wani abu ne da yake ci gaba da yaduwa a dukkan matakan kwallon kafa a duniya, daga ‘yan kallo zuwa tarayyar kwallon kafa, kuma hakan na nuna bukatar sake zage damtse don wayar da kan jama’a kan illar wannan batu.

Kazalika hakan ya kara fito da bukatar aiwatar da tsattsauran hukunci ga masu nuna halayyar nuna wariya.

Yadda aka rataye hoton daya daga cikin ‘yan wasan kwallon kafa bakake na duniya a gadar Madrid, na tuni da yadda wariyar launin fata ta yi kamari a kwallon kafar Turai.

Kasashen da ake nuna wa bakaken-fata wariya

Bari mu soma da Italiya, inda a watan Afrilu 'yan kallo suka rika kiran wani dan wasa bakar-fata biri bayan ya jefa kwallo a raga.

A Ingila, masu goyon bayan ata kungiyar kwallon kafa sun jefa bawon ayaba a yayin wasa a arewacin Landan, bayan dan wasa bakar-fata ya ci kwallo a bugun fenareti.

A Faransa, wajen da aka dinga zagin ‘yan wasan kwallon kafa na kasa maza bakar-fata saboda ba su lashe gasar kwallon kafa ta duniya ba a shekarar da ta gabata.

Ruwan dare, game duniya

A Australia, 'yan kallo sun rika dariya cikin muryar irin na birrai da kalaman nuna wariya a wasan karshe na gasar Australia Cup.

Haka a Kudancin Amurka, a lokacin wasannin gasa mafi girma a nahiyar ta Copa Libertadores, an dinga rera kukan birrai.

A arewacin Afirka ma, ‘yan wasa da suka fito daga kasashen bakar-fata na Afirka na kokawa da yadda Larabawa ke yi musu kukan birrai idan suna buga kwallo.

Hakan na nuna cewa wariyar launin fata babbar matsala ce ta zamantakewa da aka shafe shekaru da dama ana yinta a fagen a kwallon kafa amma kafafen sadarwa na zamani suna kara ingiza ta.

Shekaru 11 da suka gabata Sepp Blatter, a lokacin yana shugaban FIFA, ya musanta cewa akwai nuna wariyar launin fata a gasar, inda ya ce za a warware duk wani laifi ko cin fuska ta hanyar gaisawa da musabaha.

Dan wasa bakar-fata da ya fuskanci nuna wariya mafi muni a tarihi shi ne Vinicius Junior, dan kasar Barazil mai shekaru 22 da ke taka leda a Real Madrid, kungiyar da ta fi kowacce samun nasara a Turai.

Mutum-mutuminsa aka yi tare da rataye shi a jikin wata gada da ke kusa da filin atisayen Real Madrid a watan Janairu.

Makonni biyu da suka gabata kuma, Vinicius ya zubar da hawaye yayin tunkarar wani dan kallo da ya yi masa kukan biri.

Vinicius ne ke jagorantar bakaken-fata wajen yaki da nuna wariyar launin fata, wanda ke ci gaba da gurbata wasa mafi shahura a duniya.

Ya wallafa sako a shafinsa na Twitter cewa “Ina da manufa a rayuwa. Zan ci gaba da gwagwarmayar yakar wannan mummunar dabi’a ta yadda nan gaba ba za a fuskanci wannan matsala ba. Na shirya tsaf.”

Babban abin da ke damun Vinicius shi ne yadda mahukuntan wasannin kwallon kafa na Sifaniya ba sa daukar mataki don magance wannan matsala.

Tabbas, hukumomin wasanni a duniya suna tafiya hawainiya wajen daukar matakan da suka kamata don hukunta masu nuna wariya, duk da damar da FIFA ta ba su tun shekarar 2013.

Matakin da ya zama dole a dauka

Ko hakan ya yi? A rufe filin wasa na wani dan lokaci? Yaya batun tsauraran matakai kamar su zabge maki da kora daga gasa? An ware wadannan ne don laifukan almubazzaranci da kudade, ba wai nuna wariyar launin fata da zagi ga ‘yan wasa ba.

Wannan sakamakon ya zama yanayin gaza katabus ga ‘yan wasa bakar-fata. Da aka tambaye shi kan abin da yake tsammani bayan zagin Vinicius, kocin Real Madrid Carlo Anceletti ya ce “Ba komai. Saboda hakan ya faru a lokuta da dama kuma babu abin da aka yi."

Mutane suna jinjina wa masu gangami na kyamar nuna wariyar launin fata a kwallon kafa, amma ana yi wa hakan kallon wani abu mara muhimmanci, musamman yadda ba a cin tarar ‘yan kallo da suka ci fuskar ‘yan wasa.

Kwararru sun ce dole a dauki mataki kan masu nuna wariyar launin fata idan ana so kwallon kafa ya ci gaba da zaman abin soyuwa a zukatan mutane.

Wariyar da aka nuna wa Venicius ta sosa zukata a Brazil, inda har aka yi zanga-zanga a kofar Ofishin Jakadancin Sifaniya da ke Sao Paulo.

Jacco van Sterkenburg, Farfesa a harkokin tsere, a Jami’ar Erasmus a birnin Rotterdam an fi bari a nuna wariyar launin fata a Sifaniya da kudancin Turai.

Ya ce “A matsayin kungiyar kwallon kafa, idan ba ku dauki kwakkwaran mataki ba, ba za ku daina ganin wannan abu ba, kuma idan ba kwa maimaita hana hakan lokaci zuwa lokaci, zai ci gaba da afkuwa.”

Kwallon kafa na bukatar tallafi daga waje ta yadda za a kakkabe nuna wariyar launin fata.

Dadadden al'amari

Samuwar kafafen sada zumunta na da ta ingiza nuna wariyar launin fata a kwallon kafa.

A yanzu mutane kan aike da sakon nuna wariya, yin zagi da cin fuska ta wayoyin hannu ba tare da an san waye ya yi hakan ba, sannan sun makala su a kasan shafukan ‘yan wasa, kamar yadda aka yi wa Vinicius.

Karin ilmantarwa da tsauraran hukunci na da matukar muhimmanci wajen yaki da nuna wariyar launin fata, in ji wani tsohon wanda ya lashe Gasar Cin Kofin Duniya da ya taka leda a Sifaniya.

AP