Manchester City ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai bayan ta lallasa Real Madrid da ci 4-0 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Etihad ranar Laraba.
Hakan na nufin City za ta kece raini da Inter Milan a wasan karshe ranar 10 ga watan Yuni a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.
Bernardo Silva ne ya zura kwallaye biyun farko a minti na 23 da minti na 37 kafin a tafi hutun rabin lokaci.
Daga bisani Eder Militao da Julian Alvarez kowanne ya zura kwallo daya a ragar Real Madrid.
Ba ma shirin daukar fansa a kan Real Madrid - Guardiola
Sau biyu Real tana fitar da City daga gasar a zagayen dab da na karshe amma a wannan karon yaran Pep Guardiola ba su yi kasa a gwiwa ba wajen nuna kwarewarsu ta murza kwallon kafa.
City ta kama hanyar lashe Kofuna uku: Zakarun Turai, Gasar Firimiya - idan ta yi nasara a gida a wasan da za su yi da Chelsea ranar Lahadi - da Kofin FA, inda za su gwabza da Manchester United a wasan karshe a Wembley.