Manchester City ta yi nasarar lashe Kofin Gasar Firimiya karo na uku a jere bayan Arsenal ta sha kashi a hannun Nottingham Forest a wasan da suka yi a yau Asabar.
Arsenal ta kwashe galibin kakar wasa ta bana tana bayan City da maki hudu inda take da sauran wasa daya bayan Forest ta doke ta da ci 1-0.
Yaran Pep Guardiola sun lashe Kofin sau biyar a cikin kakar wasa shida da suka gabata.
Manchester City ta dauki fansa a kan Real Madrid
Baya ga wannan, City na da damar daukar karin Kofuna biyu a kakar bana: Kofin FA da kuma na Gasar Zakarun Turai a watan gobe.
Manchester United kadai ta taba yin irin wannan bajintar a kakar wasa ta 1998-99, kuma za ta fafata da ita a Wembley ranar 3 ga watan Yuni don neman daukar kofin FA, sannan ta gwabza da Inter Milan mako daya bayan haka a Istanbul domin neman lashe gasar Zakarun Turai karon farko.
Gobe Lahadi 'yan wasan City za su yi bikin daga Kofin nasu bayan sun fafata da Chelsea.