Kocin Paris Saint-German, Christophe Galtier, ya tabbatar cewa Lionel Messi zai buga wasansa na karshe a kungiyar ranar Asabar.
Cikin ‘yan makonnin nan an yi ta rade-radi kan makomar dan kasar Ajentina inda wasu rahotanni ke cewa zai koma Saudiyya da taka leda.
Messi ya koma PSG ne daga Barcelona a shekarar 2021 kuma ya taimaka wa PSG ta lashe gasar Ligue 1 sau biyu.
"Na samu gatan kasancewa kocin dan wasan da ya fi kwarewa a tarihin kwallon kafa," a cewar Galtier.
"Wannan ne wasansa na karshe a filin wasan Parc des Princes kuma ina fatan za a tarbe shi da hannu bibiyu."
PSG ta kara tsaro a gidan Messi da gidan dan wasan gaba Neymar da kuma dan wasan tsakiya Marco Verratti da ma na Galtier a watan jiya bayan zanga-zangar magoya bayan kungiyar.
Wannan ya faru ne bayan kashin da suka sha a hannun Lorient da kuma dakatarwar da aka yi wa Messi ta mako biyu bayan ya tafi Saudiyya ba tare da izinin PSG ba. Daga baya ya nemi afuwar ‘yan wasan kulob dinsa.
Messi neya ja goranci tawagar kwallon kafar Ajentina a nasarar da ta yi ta daukar Kofin Duniya a 2022, kuma bayan ya dawo daga gasar ya yi kamar zai ci gaba da zama a PSG.
Bangarorin biyu sun amince cewar zai tsawaita zamansa a PSG da shekara daya amma daga bisani sun sauya shawara.
Messi ya zura kwallaye 21 a raga a kuma ya taimaka wajen zura kwallaye 20 a raga wa PSG cikin dukkanin gasa a wanna kakar