Kocin Barcelona, Hansi Flick ya koka kan yadda alƙalan wasa ba sa "ba da kariya" ga taurarin 'yan wasan Barcelona da na Real Madrid, wanda ke bai wa 'yan wasan baya lasisin yin ƙeta.
Hansi Flick ya yi kira ga alƙalan wasa su ringa ba da tsaro ga 'yan wasa kamar Lamine Yamal na Barcelona, da Vinicius Jr na Real Madrid, ta hanyar ɗaukan mataki kan masu mugun wasa.
Kocin yana magana ne kan alƙalan wasa na gasar La Liga, inda ya nemi su tabbatar sun ba da kariyar, ta hanyar daina barin 'yan wasan baya suna ƙeta wajen ƙwace ƙwallo ba tare da an hukunta su ba.
Alƙalanci a gasar LaLiga ya zama wani batu da ke samun suka a 'yan kwanakin nan, inda ƙungiyoyi kamar Real Madrid, Alaves, Real Sociedad, Rayo Vallecano, da Leganes suka fitar da sanarwa don nuna rashin gamsuwarsu da ingancin alƙalancin.
Duk da Flick a baya ya goyi bayan alƙalan, inda ya nemi ba su kariya, yanzu ya nuna damuwarsa kan kula da lafiyar 'yan wasa.
Duka 'yan wasa
Alƙaluma daga StatMuse suna nuna yadda 'yan wasa kamar Vinicius da Yamal suke cikin waɗanda aka fi yawan yi wa ƙeta a LaLiga, inda aka yi wa Vini ƙeta sau 50, Yamal kuma ƙeta sau 43.
"Ba muna cewa ne a bai wa Lamine, Vini, ko Raphinha kariya ta musamman ba, amma kowane ɗan wasan ya samu kariya," in ji Flick, kamar yadda shafin Goal ya faɗa.
"Idan ƙwace ƙwallon da ganganci a ciki, to a ba da yalon kati, idan ba haka ba abin zai ci gaba da maimaituwa. Su (alƙalai) na buƙatar su yi haka. Abin lura shi ne kai ɗan wasan baya ka san cewa nan gaba kar ka sake yin ganganci".
Kocin na Barcelona yana kaka ta farko a ƙungiyar, inda wasa yake masa kyau saboda a yanzu Barca ta ɗare kan teburin Laliga, kuma a gasar Zakarun Turai suna samun tagomashi, inda za su kara da Benfica a zagayen 'yan-16.