A jadawalin da aka fitar, za a kammala gasar ta UEFA ta kakar 2024-2025 a ranar 31 ga Mayun 2025. / Hoto: Getty Images

Ƙungiyar Real Madrid za ta kara da abokiyar hamayyarta Atletico Madrid a matakin sili-ɗaya-ƙwale a Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai ta UEFA.

An tsara yadda zagayen na ‘yan 16 da zagayen dab da na kusa da na ƙarshe da zagayen dab da ƙarshe da kuma zagayen ƙarshe za su kasance a ranar Juma’a a Nyon.

.

A jadawalin da aka fitar, za a kammala gasar ta UEFA ta kakar 2024-2025 a ranar 31 ga Mayun 2025.

Ga yadda jadawalin zai kasance:

Zagayen ‘yan 16:

1- PSG da Liverpool

2- Club Brugge da Aston Villa

3- Real Madrid da Atletico Madrid

4- PSV Eindhoven da Arsenal

5- Feyenoord da Inter Milan

6- Bayern Munich da Bayer Leverkusen

7- Borussia Dortmund da Lille

8- Benfica da Barcelona

AA