Haramcin bai shafi wasan da Real Madrid za ta buga da Manchester City a gasar Zakarun Turai ba yau Laraba. / Hoto: AFP

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya ta samu ɗan wasan Real Madrid Jude Bellingham da laifin cin zarafin alƙalin wasa, a wasan da Real Madrid da Osasuna suka yi ranar Asabar da ta gabata, inda aka ba shi jan kati.

Bellingham ya furta kalaman zagi ne ga alƙalin wasan Jose Luis Munuera Montero, wanda ya sallame shi nan take, kamar yadda rahoton bayan wasa da alƙalin ya bayar ya bayyana.

Bayan da hukumar ƙwallon Sifaniya ta bincika laifin, a yanzu ta yanke hukuncin haramta wa ɗan wasa buga wasannin biyu saboda abin da ta kira 'halayyar raini' ga alƙalin wasa.

Ɗan wasan ɗan asalin Ingila, ya musanta aikata laifin da ya aikata a wasan da aka tashi kunnen doki 1-1 a filin wasa na El Sadar sansanin Osasuna.

Sassaucin hukunci

Kocin Real Madrid, Carlo Ancelotti ya goyi bayan ɗan wasan kan cewa ba a fahimci kalamansa ba ne, inda ƙungiyar ta nuna hujjar bidiyo don neman kariya ga Bellingham.

Tun da fari, Real Madrid ta nemi da a warware hukuncin jan katin, amma sai kwamitin ladabtarwa na hukumar ƙwallon ya yi hukuncin rage haramcin buga wasa da yawa, kan ɗan wasan, zuwa wasanni biyu kacal, maimakon 4 ko sama da haka.

Hukuncin ya ce, "Duba da bambancin bayanan da aka samu game da abin da ya faru, ya dace a saka takunkumin hana wasa, wanda shi ne mafi ƙarancin hukunci".

Bellingham mai shekaru 21 ba zai halarci wasan da Real Madrid za ta buga da Girona ranar 23 ga Fabrairu ba, da kuma wasansu da Real Betis ranar 2 ga Maris.

TRT Afrika