John Stones ɗan wasan baya na Manchester City zai yi jinyar har makonni 10, bayan raunin da ya samu makon jiya, kamar yadda kocin ƙungiyar Pep Guardiola ya tabbatar.
Ɗan wasan wanda ɗan asalin Ingila ne, ya samu rauni a cinyarsa yayin wasan da suka buga da Real Madrid a gasar Zakarun Turai, inda suka yi rashin nasara da ci 1-3.
Yanzu dai ta tabbata cewa Stones zai yi jinyar sama da wata biyu, wanda hakan zai zama ƙarin matsala ga ƙungiyar da kuma kocinsu Guardiola, wanda ya ce ba za a yi wa ɗan wasan tiyata ba.
Ana fatan ɗan wasan da yake buga wa tawagar ƙasar ta Three Lions, zai murmure cikin makonni takwas zuwa 10.
Raunin da Stones ya samu na zuwa ne a lokacin da City ke fama da jerin masu jinya a manyan 'yan wasanta, ciki har da mai tsaron baya Manuel Akanji, wanda ake sa ran zai dawo fili nan kusa bayan shi ma an masa tiyata a baya.
Tawagar Ingila
Ita ma tawagar Ingila labarin bai mata daɗi ba kasancewar Stones zai rasa wasan neman cancantar shiga gasar Kofin Duniya da za su buga da Albania da kuma Latvia, inda sabon koci Thomas Tuchel zai fara jagorantar su.
Yayin da John Stones zai tafi doguwar jinya, kocin Man City ya bayyana cewa ɗan wasansu Oscar Bobb yana dab da komowa, bayan daɗewa yana jinya.
Bobb mai shekaru 21 yana murmurewa daga raunin karaya a ƙafa wanda ya samu yayin atisaye a watan Agustan bara, wanda ya sa shi jinyar kusan watanni 7.
Shi ma gwarzon ɗan wasan gaba na Manchester City, Erling Haaland yana nuna alamun murmurewa don buga wasansu na gaba a gidan Tottenham.
Haaland ɗan asalin Norway ya rasa wasanni biyu da City ta buga saboda rauni a gwiwa yayin wasan City da Newcastle a farkon watan nan.