Za a buga wasan karshe na Gasar Zakarun Turai tsakanin kulob din Manchester City na Ingila, da kulob din Inter Milan na Italiya a filin wasa na Atatürk a birnin Istanbul ranar Asabar din nan.
Sai dai masoya kwallon kafa a birnin sun riga sun fara bukukuwansu a farfajiyar Yenikapi Park da ke daura da tekun Marmara.
Mazauna birnin Istanbul suna dokin cewa birninsu ne masaukin wannan babban wasa na shekarar 2023, wanda zai samu halartar dubban masoya tamola daga fadin duniya.
Wasan karshen da za a fafata tsakani Manchester City da Inter Milan, zai gudana a babban filin wasa na Atatürk Olympic Stadium ranar Asabar.
Sai dai shagulgulan masoya kwallo tuni suka fara a filin shakatawa na Yenikapi Festival Park, wanda ke daura da gabar teku.
Bikin Zakarun Turai na UEFA Champions yana gudana ne daga Alhamis zuwa Lahadi. Mahalarta bikin za su kalli bukukuwan da suka hada da damar daukar salfi, kade-kade, da raye-rayen da suka shafi tamola.
Tom Nicholson manaja ne na wasan gwaf a Dubai, kuma ya iso Istanbul tare da dan uwansa Alex don kallon wasan karshen.
An haifi Nicholson ne a garin Manchester, kuma ya bugawa kulob din Manchester City Academy har ya kai shekara 16.
"Bikin nan babba ne. Mun sauka ne da safiyar Alhamis, yanzu mun dan fito shawagi ne. Mutanen garin nan suna da son jama’a. Yanayin gari a garin shi ma ya yi kyau," in ji shi.
Ya bayyana al’adar kallon kwallo a garin Manchester da cewa “tana da karfi matuka”.
“A baya ba ma yawan cin wasanninmu, har mun saba zuwa wasa a ci mu. Ba ma yin kuri."
Ya yi amanna cewa lashe wannan kofin zai yi matukar kayatar da kulob din.
“Ina ganin kowane kulob zai so ya lashe Kofin Zakarun Turai, kuma idan Pep Guardiola ya ciyo mana kofin, da ma shi ne abin da muke ta buri."
Mahalarta wasan karshen za su samu damar ganin hamshakin Kofin Gasar ta Zakarun Turai a wajen bikin. “Ya birge ni, na jin dadin zuwa kusa da kambun”, in ji Alex.
An girke wani babban kofin da ya yi kama da na zakarun Turai a dandalin Taksim na Istanbul.
'Wasan zai kayatar’
Bikin wasan ya janyo maziyarta daga dubban kilomita nesa da Turkiyya.
Shi ma Hector "Caramelo" Chavez, dan shekara 60, masoyin kwallon kafa ne daga kasar Mexico. Ya zo Istanbul tare da dansa don kallon wasan.
"Na san wasan zai burge saboda akwai wani dan wasa mai suna [Erling] Haaland. Na tuna wani tauraron ma a Mexico a shekarun kofin duniya na 1970, wato Pele. Shi daya daga cikin manyan ‘yan kwallon duniya. A shekarar 1986, akwai Maradona.
Sannan yanzu, za mu iya cewa akwai Haaland zai zamo babban tauraro," in ji shi.
Caramelo ya halarci filin wasa na Estadio Azteca don kallon wasan karshe na Kofin Duniya na 1986, a birnin Mexico City, lokacin da Argentina ta doke West Germany 3-2.
Ya ce, "Ina sha’awar tafiye-tafiye. Na je kallon wasannin olamfik, lokacin da muka ci lambar zinare a London shekarar 2012, kuma zan je gasar CONCACAF Gold Cup".
'Wasa mai zafi’
Shagalin yana ci gaba ranar Juma’a, inda za a yi wasan kwallo tsakanin mashahuran tsofaffin ‘yan wasa da suka hada da Luis Figo, da Roberto Carlos, da Clarence Seedorf, da Kaka da kuma Patrick Vieira.
Gabriel Dodson dan shekara 30, wanda yake zaune a jihar Virginia ta Amurka. Ya yi tafiyar dubban kilomita zuwa Istanbul don ganin wasan karshe na zakarun Turai a karon farko.
Shi babban masoyin kungiyar Inter Milan ne saboda asalinsa daga Italiya yake.
Ya ce, "Na zo nan don na kalli fafatawar Inter Milan da Manchester City. Ina cikin murna. Mun ci nasarar a karawarmu da Milan bara, don haka ina farin cikin kasancewa a nan don rako su Istanbul".
“Wasan zai yi zafi sosai. Manchester City tana kan ganiyarta a bana. Amma ina ga muna da ‘yan wasan gaba masu kyau."
Dodson yana annashuwar kasancewa a bikin.
“Bikin ya yi armashi. An shirya komai yadda ya dace. Wannan ne karona na farko, ina mararin kallon bikin wasan, na fito ne don tattaki na sayi abinci da kayayyakin kwallo."
Inter Milan ta ci kofin Italiya na Coppa Italia a jere, kuma ta kammala kakar bana a mataki na uku a teburin Serie.
Manchester City tana neman daukar kofi na uku a bana, ranar Asabar din, sakamakon cewa ta riga ta ci kofin Firimiya da na FA duka a Ingila.
An shirya Istanbul ta karbi bakuncin wasan karshe na a shekarar 2021, amma sai aka mayar da wasan Portugal saboda annobar Covid.
Real Madrid ta Sifaniya ita ta fi cin kofin da kofuna 14, wanda ninki ne na kulob din da ke biye mata, AC Milan, na Italiya.
Kungiyar Liverpool ta Ingila, da Bayern Munich ta Jamus, su ke mataki na uku, suna da kofuna shida.