Jude Bellingham ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya taba kasancewa keftin din Borussia Dortmund/Hoto:Reuters

Real Madrid ta sayi dan wasan tsakiyar Ingila, Jude Bellingham, daga Borussia Dortmund a yarjejeniyar shekara shida.

Kungiyar ta Sifaniya za ta biya Yuro miliyan 103 kan dan wasan mai shekara 19, baya ga wasu hanyoyin samun kudi.

Idan hanyoyin samun kudin suka tabbata, yarjejeniyar za ta iya kai ga Yuro miliyan 133.9.

Za a gabatar da Bellingham, wanda ya fara taka ledarsa a Birmingham City, a matsayin dan wasan Real Madrid ranar Alhamis.

Dan wasan ya ce: "ina gode wa kowa a BVB [Dortmund] da kuma magoya bayana kan abubuwan da suka faru cikin shekaru ukun da suka wuce."

"Saka jasinku a lokuta da yawa ta kasance abin daraja gare ni.

"Duk da cewa hankali na ya koma inda na nufa, ba zan taba mantawa da rawar da na taka a nan ba. Idan ka taba kasancewa dan Borussia, za ka ci gaba da zama dan Borussia ne."

Bellingham ne ya dan wasan ya fi iya taka leda a kakar bana ta gasar Bundesliga/Hoto:Reuters

Bellingham na cikin ‘yan wasan da suka taka rawar gani a gasar cin Kofin Duniya ta bara kuma ya samu lambar yabo ta dan wasan da ya fi iya taka leda a kakar bana ta gasar Bundesliga yayin da Dortmund ta kasa daukar kofin gasar a karon farko cikin shekaru 11.

Kudin da za a fara biyansa zai sa ya zama dan wasa na biyu dan Ingila da ya fi tsada bayan Jack Grealish, wanda Manchester City ta biya Aston Villa fam miliyan 100 dan sayensa a 2021.

Har ila yau Bellingham shi ne dan wasan Real Madrid na biyu da ya fi tsada, bayan sayen Eden Hazard kan Yuro miliyan 115 daga Chelsea a 2019.

Bellingham ya yi suna a Dortmund inda a watan Oktoban bara ya kasance dan wasa mafi karancin shekaru da ya zama kyaftin din Borussia.

TRT Afrika da abokan hulda