Cristiano Ronaldo ya yi sujjada bayan ya zura kwallo a ragar kungiyar kwallon kafa ta Al Shabab a Gasar cin Kofin Kwararru da ake yi a Saudiyya.
Ana yin sujjada ne domin nuna godiya da girmamawa ga Allah.
A fafatawarsa ta mako na 28 ranar Talata, Ronaldo ya ci wa Al Nassr kwallo ta uku a minti na 59 sannan ya yi sujjada a filin wasa na KSU da ke Riyadh, kuma nan take ‘yan kallo suka barke da sowa da murna bisa abin da ya yi.
Ronaldo ya kure tarihin da ya kafa na wadda ya fi taka leda
‘Yan wasan Al Nassr Anderson Talisca da Abdurrahman Garib kowane ya zura kwallo daya, yayin da Cristian Guanca ya ci wa Al Shabab abin da ya sa aka tashi da ci 3-2.
Yanzu Al Nassr tana da maki 63, inda take bayan Al Ittihad FC, wadda ke ta daya, da maki uku a saman teburin babbar gasar kwallon kafa ta Saudiyya.