Galatasaray ta ci gasar Super Lig ta Turkiyya, ta doke Ankaragucu da ci 4-1

Galatasaray ta ci gasar Super Lig ta Turkiyya, ta doke Ankaragucu da ci 4-1

Wannan ne karo na 23 da kungiyar ta Galatasaray ke daukar kofin Super Lig na Turkiyya
Yadda 'yan wasan na Galatasaray ke murna bayan sun ci kofi. Hoto/AFP

Kungiyar kwallon kafa ta Galatasaray ta doke Ankaragucu da ci 4-1 inda ta ci kofin Turkish Super Lig karo na 23.

Galatasaray ta samu wannan nasarar ne a ranar Talata inda tun da farko Mauro Icardi ya ci kwallon farko a minti na 17 tare da taimakon Milot Rashica a filin kwallon Eryaman da ke Ankara.

Bayan minti shida sai Ankaragucu ta rama cin da aka yi mata a lokacin da Felico Milson ya zura kwallo a kusurwar ragar Galatasaray inda ya yi amfani da kafar hagu.

A cikin minti na 38 sai Galatasaray din ta sake zura wa Ankaragucu kwallo inda Icardi ya kara ci da kai tare da taimakon Kerem Akturkoglu.

A minti na 73 kuwa Baris Alper Yilmaz shi ma ya bayar da mamaki inda ya yanke golan Ankaragucu wato Gokhan Akkan sa’annan ya zura kwallo a raga.

Hakan ya sa kungiyar ta Istanbul ta ci kofin a karon farko tun bayan 2019.

Ta samu maki 82 a wasanni 32 wanda hakan ya sa kungiyar take gaban Fenerbahce da sauran wasanni biyu.

Wasa na karshe na Galatasaray an shirya shi ne da ATAKAS Hatayspor amma kungiyar ta fita daga gasar bayan girgizar kasar da aka yi a kudu maso gabashin Turkiyya.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi wa Galatasaray murna kan nasarar da ta samu.

A lokacin da magoya bayan Galatasaray suke murnar cin kofinsu na gasar 2022-2023 a Istanbul. Hoto/AFP

Kaddara

Galatasaray za ta yi murnar samun nasararta a ranar Lahadi a lokacin wasan adawa da kulob din zai buga da Fenerbahce, wadda ba ta ci kofin ba tun 2014.

“Galatasaray na wasa a duk shekara domin ta zama zakara. Mun ce watan Mayu namu ne. Na samu nasara a gasar kwallon Turkiyya a nan shekara 30 da suka wuce. Za mu kira wannan kaddara,” in ji kocin Galatasaray Okan Buruk bayan kammala wasan.

“Ana samun ‘yan wasa masu kyau, amma abu ne mai wahala hada kansu. Duk sun yi abin da ya kamata.”

Buruk mai shekara 49 ya gode wa ‘yan kungiyar sakamakon nishdantar da magoya bayan kungiyar.

“Daraja ce gare mu matuka mu ci wannan kofin a Ankara a lokacin da Turkiyya ta cika shekara 100 da samun ‘yancin kai.”

Golan kungiyar Fernando Muslera, wanda ya ci gasar Super Lig sau shida a kulob din, ya ce kulob din ya fusknaci kalubale matuka a kakar bara.

“Da zuwan Dursun Ozbek da Erden Timur, mun shiga wani babi na daban. Ina tunanin koya zai iya nasara.

Magoya baya sun taka rawar gani a wannan,” in ji Muslera, inda yake magana kan shugaban kulob din da mataimakinsa.

Zuwan Icardi da Torreira a kakar da ta gabata ya kara wa kulob din karsashi.

Sun kuma sayi dan gaban Belgium Dries Mertens, da dan wasan tsakiya Sergio Oliveira da dan wasan tsakiyar Italiya Nicolo Zaniolo.

TRT World