Ramos ya buga wa kasarsa wasa 180, fiye da kowanne dan wasa a tarihi. / Hoto: Reuters FIL

Paris Saint-Germain [PSG] ta ce tsohon dan wasan Sifaniya Sergio Ramos zai bi sahun Lionel Messi don su bar kungiyar a karshen kakar wasa ta bana.

"Muna so mu nuna matukar godiyarmu ga Sergio Ramos bisa kwashe shekara biyu tare da mu," in ji wata sanarwa da shugaban PSG Nasser Al Khelaifi ya fitar ranar Juma'a.

"Shugabanci irin na Sergio, da kwazonsa a tsakanin 'yan wasa da kwarewarsa da ta kai kololuwa, sun sa ya zama gagarabadau a fagen kwallon kafa kuma mun yi murnar aiki da shi a Paris."

Al Khelaifi ya kara da cewa "Dukkanmu da ke kungiyar nan muna yi masa fatan alheri."

Ramos, mai shekara 37, ya tafi PSG ne a 2021 bayan ya samu gagarumar nasara a Real Madrid.

An fitar da sanarwar ce kasa da awa 24 kafin PSG ta buga wasan karshe na cin Kofin Ligue 1 inda za ta fafata da Clermont.

Ramos zai bi sahun kyaftin na Argentina Lionel Messi domin barin Parc des Princes yayin da wasu rahotanni ke cewa shi ne dan wasan Brazil Neymar zai bar kungiyar.

Tsohon dan wasan nan Sevilla ya lashe Ligue 1 sau biyu a Paris, inda ya buga wasa 57 kuma kwangilarsa za ta kare a kungiyar ranar 30 ga watan Yuni.

"Gobe rana ce ta musamman, gobe zan yi bankwana domin bude wani babi na rayuwata, sai wata rana @psg," in ji Ramos a sakon da ya wallafa a shafinsa na soshiyal midiya.

TRT Afrika da abokan hulda