Morocco ta ci gaba da tsayawa a matsayinta na kasar da ta fi kwarewa a fagen kwallon kafa a Afirka, kamar yadda hukumar FIFA ta bayyana./Hoto: AFP      

Kasar Maroko wanda ta kai wasan kusa da na karshe a Gasar Kofin Duniya na 2022, ita ce kasa ta daya a fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka kuma ita ce ta 13 a duniya.

A jadawalin hukumar FIFA na baya-bayan, kasar Senegal tana a mataki na biyu ne a Afirka kuma ta 18 a duniya.

Aljeriya ce ta uku a Afirka kuma ta 33 a duniya, yayin da kasar Masar take ta hudu a Afirka kuma ta 34 a duniya.

Nijeriya ta zo ta biyar ne a Afirka kuma ta 39 a duniya. Kamaru tana mataki na shida ne a Afirka kuma ta 43 a duniya, Mali (ta bakwai a Afirka, kuma 50 a duniya), Burkina Faso (ta tara a Afirka, ta 55 a duniya), sai Ghana (ta 10 a Afirka, ta 59 a duniya).

Afirka ta Kudu ta zo matsayi na 11 a Afirka kuma 62 a duniya, daga nan sai Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo (ta 69 a duniya), Guinea (ta 80 a duniya), Zambiya (ta 84 a duniya), Gabon (ta 85 a duniya).

Equatorial Guinea (ta 91 a duniya), Uganda (ta 92 a duniya), Benin (ta 93 a duniya), Mauritaniya (ta 99 a duniya), Kenya (ta 105 a duniya), jerin matsayin kasashen Afirka 20 kenan a fagen kwallon kafa.

Kasashen da suke gaban Maroko

Wadannan ne kasashen da ke gaban Maroko:Argentina wacce ta zo ta daya a duniya, Faransa ta zo ta biyu ne a duniya, daga nan sai Brazil da Ingila da Belgium da Croatia da Netherlands da Italy da Portugal da Spain da USA da kuma Switzerland wadda ta zo matsayi na 12.

Maroko ta kafa tarihi a shekarar 2022, inda ta zama kasar Afirka ta farko da ta kai matakin wasan kusa da na karshe a Gasar Kofin Duniya na Maza.

Kasar ta yi rashin nasara ne a hannun Faransa da ci 2-0 a wasan kusa da na karshe a gasar wadda aka yi a kasar Qatar.

Kafin ta kai matakin wasan kusa da na karshen, Maroko ta doke kasashen Belgium da Spain da kuma Portugal (a wasan gab da na kusa da na karshe).

Yayin wasansu da Belgium, Maroko ta doke ta ne da ci 2-0, kuma a wasansu na gaba, kasar Afirkan ta doke Spain da ci 3-0 a bugun fanarati bayan sun tashi wasa kunnen doki.

Yayin wasan da suka buga da kasar Portugal a wasan gab da na kusa da na karshe, Maroko ce ta yi nasara da ci 1-0 wanda ya sa ta kai wasan kusa da na karshe, wannan ne karon farko da wata kasar Afirka ta kai wannan matsayi a tarihin gasar.

A tsohon jadawalin da hukumar FIFA ta fitar a watan Disambar, Maroko ta zo mataki na 11 ne bayan nasarar da kasar ta yi a gasar cin kofin duniya a Qatar.

TRT Afrika