Fitaccen dan wasan Ghana Asamoah Gyan ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa yana da shekara 37, abin da ya kawo karshen tarihin kwallon kafa na daya daga cikin zakakuran 'yan wasan Afirka.
Ya buga wa kasarsa wasa sau 109 ciki har da wasannin da ya buga na cin Kofin Duniya a 2006, 2010 da kuma 2014. Ya taimaka wa tawagar kwallon kafar kasar Black Stars wajen zura kwallo 51.
Gyan ya sanar da yin ritaya ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Talata.
"Lokaci ya yi…na dade ina shirin yin haka, don haka na yanke shawara, lokaci ya yi. Lokaci ya yi da zan ajiye jesi da takalin kwallo cikin mutunci domin na sanar a hukumance cewa na yi ritaya daga murza tamaula," in ji Gyan.
Ya ce zai yi amfani da "kwarewarsa a fannin horar da kwallon kafa da sana'ar ta kwallon kafa".
Gyan ya murza leda a kungiyar Rennes ta Faransa amma daga bisani ya tafi Ingila inda ya murza leda a Sunderland a 2010 a kakar wasa biyu.
Kazalika ya buga wasa a Al Ain, Shanghai SIPG, Kayserispor da North East United.