Falasɗiniya kana Ba’amurke Hebah Kassem kenan a harabar Masallacin Al-Aqsa a ziyararta ta farko zuwa Falasdinu a wannan bazarar (Hoto daga Will Allen-DuPraw).  

Daga Hebah Kassem

A tsawon shekaru da dama, ni da mahaifina mun yi ta burin kai ziyara ƙasarmu ta haihuwa – Falasdinu – don mu sa da zumunci da al'ummarmu, tare da zuwa ƙauyenmu a Safa (wanda a yanzu ake kiransa da Safed), da kuma kai ziyara ɗaya daga cikin wurarenmu mafi tsarki, wato Masallacin Ƙudus.

Tushen danginmu da bishiyoyi, da tarihinmu duk suna binne a cikin zukatanmu, duk da cewa an tilasta wa 'yan'uwanmu barin gidajensu.

Amma ban taba tunanin tafiyata ta farko zuwa ƙasa ta za ta kasance cikin yanayin kisan kiyashin da ake nuna wa kai tsaye a faɗin duniya ba.

A yayin da nake rubuta wannan labari hawaye ne yake gangarowa kan kumatuna, Falasdinawa a Gaza suna kan jure ɗaya daga cikin mafi munin yanayi na kisan kiyashi da ake kan yi.

Duniya ta shaida irin wahalhalu da hare-haren bama-bamai da Falasdinawa ke fuskanta a Gaza, ga kuma al'ummar Lebanon a yanzu.

Hotunan sun kasance masu ban tsoro musamman na baya-bayan nan inda aka kona Falasdinawa da ransu a wani harin bam da Isra'ila ta kai asibitin Shahidai na Al-Aqsa da ke Gaza.

A wannan bazarar, bayan shafe tsawon watanni ina kallon wannan mumunar yanayin a kan wayata, na yanke shawarar tafiyata ta farko zuwa Falasdinu.

Hebah Kassem zaune a gaba tare da direban bas kan hanyarsu ta zuwa Jerusalem a karon farko (Hoto daga Will Allen-DuPraw)

Na yi rajista a lokacin da na samu labarin wata tawaga mabiya addinai da dama za ta ke Falasdinu. Ni da wani abokina, dukkanmu Musulmai kuma Falasdinawa, mun bi tawagar Kiristoci, da Yahudawa,da 'yan Hindu, da dai sauransu, tare muka tsallaka zuwa Falasdinu da aka mamaye ta hanyar taimako.

Wannan ƙungiyar ta kristoci Faladinawa tana ƙarfafa rashin tashin hankali da juriya a birnin Kudus, kuma tana goyon bayan Falasdinawa.

Mun ketare gadar King Hussein da Allenby daga Jordan tare da tawagar, wanda ne karo na farko da na taba bin hanyar a matsayina ta Bafalasdiniya 'yar Falasdinu.

Ba ni da wata shaida na Falasdinu a cikin ƙasar kuma ba ni da wani dangi da ya rage a wurin.

Wannan ita ce ƙasar da ke zaune cikin zukatan dangina, wadda na daɗe ina ji suna marmari da yekuwarta a tsawon rayuwata.

Sun yi gudun hijira na dindindin tun lokacin ''bala'i'' na Nakba a shekarar 1948 da aka kai wa Falasdinawa hari kana aka tilasta musu karfi tare da tilasta mus yin gudun hijira.

Faladinu tana zukatanmu

Shiga cikin Falasdinu da kuma ziyarata a daidai lokacin da ake yaɗa yadda mafi munin kisan kare-dangi da kuma kai hare-hare a kan Falasdinawa a yankin Yammacin Kogin Jordan da 'yan ta'adda masu tsatsauran ra'ayi da sojojin Isra'ila suke aikatawa ya kai kololuwa. Ina tuna iyayena.

Dukansu 'yan gudun hijirar Falasdinu ne, sun fi sauran danginmu sa'a kuma sun sami damar zuwa Amurka inda suka fara tara iyali. An haife ni kuma na girma a Dearborn, na jihar Michigan.

Sai dai ita ma Amurka ta kasance kasar da ke ci gaba da ba da tallafi ga zaluncin da ake kan aikatawa a kan 'yan ƙasa ta.

Bisa ga kididdigar masu ra'ayin mazan jiya, Amurka ta kashe akalla dala biliyan 22.76 tsakanin 7 ga watan Oktoba, na 2023 zuwa 30 ga Satumba, 2024 kan tallafa wa hare-haren sojin Isra'ila da kuma wasu kudade da ke da alaka da hakan.

Kisan kare-dangi da ake yi a Gaza ya fallasa Isra'ila a matsayin kasar da ke nuna wariyar launin fata da kuma Amurka wajen gina ta.

A yayin zantawa ta da Falasdinawa a wurin, sun shaida min yadda rayuwa ta yi tsanani tun lokacin da aka fara yaki a Gaza.

Wata mata ta faɗa min cewa, "Su (Isra'ila) sun sa ku kewar yadda suka mamaye ku kafin fara yakin a Oktoba."

Ku ainihin 'yan ina ne?

Sunana na farko da na karshe yana kan fasfo ɗina na Amurka - Hebah Kassem. Saboda sunana kawai, na sha tambayoyi daban- daban daga jami'an tsaron Isra'ila fiye da sauran abokan tafiyata.

Sun sha tambayata asalin inda na fito, iyayena 'yan ina ne, ko shin ina da abokai da dangi a Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye, ko kuma ina da wasu takardu shaidar zama a Lebanon, sannan a ina nake zama a can ɗin, ina ta shaida musu cewa ni Ba'amurkiya ce kuma ina kan hanyar zuwa Birnin Ƙudus ne.

A mashigar, na ga yadda Isra’ilawa suke kallona da kuma yadda ake nuna wa Falasdinawa wariya tare da sanya su jure danniya da bin matakan “tsaro” na son rai.

Kyamararorin tsaro na Isra'ila (Hoto daga Will Allen-DuPraw)

Kasuwancin Falasdinawa a birnin Kudus da Yammacin Gabar Kogin Jordan da aka mamaye ya fuskanci koma baya sosai la'akari da yanda zuwan masu yawon buɗe ido ya ragu sosai tun watan Oktoba.

Hare-haren da Yahudawa 'yan kama-wuri-zauna ke kaiwa kan Falasdinawa da adadin Falasdinawan da aa kashe ya karu sosai a cikin shekaru biyun da suka wuce.

Isra'ila na kara kwace wa Falasdinawa filayen tare da rusa gidajensu kamar yadda muka ga an rusa wasu a Silwan, wata unguwar Falasdinawa da ke gabashin Kudus da aka mamaye.

Hoton Silwan a Gabashin birnin Kudus da aka mamaye, inda aka rusa gidajen Falasdinawa (Hoto daga Will Allen-DuPraw).

Anan, kashi 80 cikin 100 na gidaje an sanarwar da mutanen ciki kan su tashi, wata dabarar Isra'ila na rusa su ɗaya bayan ɗaya.

Sojoji sun mamaye garurwa da dama tare da sansanonin 'yan gudun hijira a Yammacin Kogin Jordan kana suna kan tsare kananan yara da matasa wadanda basu yi komai ba tun daga ranar 7 ga watan Oktoba kawo yanzu.

Da nake Falasdinu, sojojin Isra’ila sun harbe wata Baturkiya kuma Ba’amurkiya Aysenur Ezgi Eygi 'yar gwagwarmaya a kai, a lokacin da take zanga-zangar nuna rashin amincewa da mamayar matsugunan da aka yi musu ba bisa ka’ida ba.

Kazalika, ta kaddamar da wani gagarumin farmaki a yammacin gabar kogin Jordan da ta mamaye, inda ta yi ta kai hare-hare da jiragen sama tare lalata kayayyakin more rayuwa a Jenin, da Tulkarem, da Nablus, da kuma Tubas.

Rikici a wuraren bincike

Tafiyata zuwa ƙasata ta asali ta ba ni taƙaitaccen bayanai game da yadda rayuwar Falasɗinawa take kasancewa a kullum. Sannan ina jin zafin raɗaɗin fitowata daga Falasdinu har yanzu.

Hebah Kassem ta shaida harin da aka kai ta sama a Gaza daga motar bas yayin da take tafiya zuwa kan iyaka fita da garin (Hoto daga Will Allen-DuPraw).

Ina bukatan bin jirgi daga Amman ranar litinin. Amma a ranar Asabar, an rufe gadar zuwa Jordan, wani hukuncin gama-garı da Isra'ila ta yanke bayan Oktoba. Sannan zuwa safiyar Lahadi wani dan ƙasar Jordan ya kai wani hari a kan gadar King Hussein/Allenby, lamarin da ya yi sanadin rufe duk wata hanyar shiga Jordan.

An tilasta min zama har zuwa ranar Litinin, bayan nan ne na yi kokarin bi ta kan gadar King Hussein/Allenby wuri mafi kusa da birnin Kudus wanda kuma bude wa Falasdinawa kawai.

A kan tafiyarmu ne, na samu labarin cewa an rufe hanyar don haka muka yi tafiya ta sa'o'i biyu a arewa zuwa Mashigar Kogin Sheikh Hussein/Jordan wanda ke buɗe ga 'yan wasu ƙasashe da 'yan Isra'ila kawai.

Hebbah Kassem in Beit Jala overlooking the occupied West Bank/Bethlehem (Photo by Will Allen-DuPraw).

Na dawo Amurka yanzu ina ƙoƙarin ci gaba da gudanar da rayuwa ta. Amma ba zan iya cire hotuna ko abubuwan da suka faru daga Falasdinu daga kwakwalwata ba kuma ba na so. Idan kuwa har kuwa akwai wani abu, zan fi kowa son yin gwagwarmayar kwato wa jama'ata yancinsu.

Shekaru 76 na mamaya - wannan ne mafi muni

Gwamnatin Biden da Harris ta yi yunƙurin neman goyon bayan al'ummarmu a zaɓe mai zuwa yayin da suke ci gaba da ba da tallafin wariyar launin fata, da ba da damar kisan kiyashi da wadata Isra'ila da bama-baman da ake jefa wa kan mutanen Falasdinu, da Labanon, da Siriya, da kuma Yemen.

Kamar yadda na rubuta a baya a cikin watan Maris, muna sane da haɗarin da ke cikin watan wannan Nuwamba. ‘Yan jam’iyyar Democrat sun kasa ji, balle su iya biya mana buƙatunmu na kawo karshen radadin da Falasdinawan ke ciki.

Kazalika Trump ya sha alwashin "kammala aikin da aka soma" a Gaza. Shekaru 76 ke nan da ake kana mamayar mutane nan kuma ina ji tamkar wannan ita ce shekarar da ta fi kowace muni ta fuskar wahala da zubar da jini.

Mun bai wa mataimakiyar shugaban ƙasa Harris duk wata dama don ta banbanta kanta da manufofin Shugaba Joe Biden da kuma matsawa ga kawo karshen wahalar da Falasdinawa ke ciki, amma har yanzu tana ci gaba da yin kasa a gwiwa.

Amma za mu ci gaba da kokari har sai an ji muryoyinmu ta hanyar bayyana buƙatunmu da kauracewa kamfanonin da ke goyon bayan Isra'ila, da kuma goyon bayan 'yan takara masu neman tsagaita wuta da sanya takunkumi kan makamai.

Za mu iya kuma za mu ci gaba da jajircewa wajen gina ƙawancen domin fafutukar kwato 'yancin Falasɗinawa.

TRT World