Falasdinawa kenan yayin duba wata makaranta da harin isra'ila ta sama ya ruguza inda mutanen da suka rasa gidajensu ke zama a ciki a Gaza, 10 ga Agusta, 2024 (REUTERS/Abed Sabah). / Hoto: Reuters

Daga Sundos Hammad

A shekarar 2000, ina 'yar shekara tara a lokacin Intifada ta biyu, na fahimci babbar alakar da ke tsakanin ilimi da rayuwa karkashin mamaya.

A kowacce safiya, zuwa makarantar firamare a garin al-Bireh ya zamar min abin da nake bijirewa.

An jibge tankokin yakin isra'ila a kofar shiga makarantarmu, kuma idan aka tashi da yamma yara kanana iri na na jefa duwatsu kan sojojin Isra'ila da suka yi wa unguwar ƙawanya.

Sojojin na mayar da martani da harsashai na gaske. Ina komawa gida a firgice, na yi tambayar me ya sa mu Falasdinawa muke fuskantar wannan hatsari kullum, amma a kullum mahaifiyata tana fada min cewa "Ilimi ba zabi ba ne, dole ne, shi ne makomarki, makomar al'ummarki."

A yau, wannan makoma ba ta da daɗi.

A cikin sama da kwanaki 335, an hana sama da Falasdinawa miliyan biyu hakkin rayuwa da wanzuwa a ban kasa a yayin da suke fuskantsar hare-hare daga Isra'ila ba ƙaƙƙautawa.

A yayin da ake aikata kisan kiyashi a Gaza, dalibai a kasashen duniya kuma ke shirin komawa makaranta, tsarin ilimi a Falasdinu ya zama ciwo na yaki.

An dinga harar makarantu da bama-bamai a Gaza, inda aka kuma tsugunar da jama'a. Har yanzu dai duk da ana cikin wannan mawuyacin hali, jakar makaranta ta zama jakar neman tsira.

Ina iya tuna kallon wani gajeren bidiyo na wannan yarinya karama da ta dauki litattafanta a jaka a yayin da take guduwa daga gidansu, tana fadin cewa "Na kubutar da litattafaina."

Mun gina wadannan jami'o'i da tantuna, baya ga tantuna da kuma taimakon abokanmu. za mu sake gina su.

A watan Mayun wannan shekarar, jami'o'in Gaza sun fitar da sanarwa suna tabbatar da wanzuwarsu da kuma kudirinsu na dawowa karatu a cibiyoyinsu na Gaza, duk da rusau din da dakarun Isra'ila suka yi wa manyan makarantun.

Yayin nuna bijirewa wannan kisa da ake yi wa ilimi, sun ce "Mun gina wadannan jami'o'i da tantuna. Kuma daga tantunan, tare da goyon bayn abokanamu, a mu sake gina su a karo na biyu."

Nakasasshen tsarin koyo da koyarwa

Tun 7 ga watan Oktoban 2023, Isra'ila ta kashe a kalla Falasdinawa dalibai 10,490, tare da jikkata wasu 16,700, kamar yadda Ma'aikatar Ilimi Mai Zurfi ta Falasdin ta bayyana.

Sama da malaman kananan makarantu da jami'o'i 500 ne aka kashe, inda aka hana yara 'yan firamare da sakandire 600,000 zuwa makaranta, da kuma wasu 88,000 'yan jami'a.

An kassara manmyan makarantu 17 a Gaza, ko an lalata wani bangare nasu, ko an ruguza su baki daya da harin bama-bamai, kuma kashi biyu cikin uku na makarantun Gaza sun fuskanci hare-hare inda a yanzu mutanen da aka tsugunar suke fake a ciki.

A yayin da hakan ke faruwa, a Yammacin Kogin Jordan kuma, ana ci gaba da mamayar yankunan Falasdinawa, inda aka tirsasawa manyan makarantu 34 koma wa bayar da ilimi daga nesa tsawon watanni saboda karuwar keta hakkoki, hana zirga-zirga da rikicin 'yan kama wuri zauna.

Dalibai da malaman manyan makarantu na Falasdinna yawan fuskantar hare-hare daga sojojin Isra'ila, ko a Gaza. ko a Yammacin Kogina Jordan da aka mamaye, Gabashin Kudus ko sansanonin 'yan gudun hijira.

An bayyana ayyukansu a matsayin manyan laifuka, an hana su maotsi yadda ya kamata, ana kai wa jami'o'insu hare-hare, kuma ana tauye 'yancinsu.

Sama da dalibai 2,500 na jami'ar Birzeit a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye sun shiga kurkuku tun 1982, inda sama da 140 daga cikinsu har yanzu suke daure.

Sama da 70 daga cikin wadannan dalibai sun shiga hannun Isra'ila ne bayan 7 ga Oktoban 2023, cikin su har da dlibai mata shida, da malaman jami'a da ma'aikatan manyan makarantu. Mafi yawancinsu na karkashin dauri ba tare da an kai su kotu ba.

Jahilci a matsayin abokin tafiya

Wannan ya kawo mu ga tambayar: me ya sa ake kai hari da durkusar da ilimi a Falasdin?

Idan aka zo maganar batun kama-karyar da 'yn kama wuri zauna ke yi a Falasdin, jahilci ne ka zama babban abokin aiki, sai a dinga aiki da labaran dokin mai baki. gefe guda kuma ilimi ya zama babban jigon nuna tirjiya.

Ci gaba da ruguza tsarin ilimi na Gaza na bayyana tsanantar wannan danyen aiki, wanda a yanzu malamai suke kira da "kisan kiyashi ga ilimi." Wannan kalma da farfesan Jami'ar Oxford Karma Nabulsi ya samar a yyin hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza a tsakanin 2008/2009 na nugin rusa cibiyoyin ilimi da gan-gan a Falasdin.

Wannan dabara, wani bangare na mnufofin mulkin danniya, ba wai iyakacin gine-gine kawai ke rusa wa ba, har ma da nakasta habakar ilimin kwakwalen jama'a.

Ana rusa ilimin ne saboda ya zama wani nau'i na tirya a wajen Falasdinawa. Ta hanyarsa ne Falasdinawa ke iya kalubalantar labaran wadanda dawakansu ke da gudu, suke kare tarihinsu da asalinsu, da kuma gina matasansu masu taso wa.

Sake farfadowa

Duk da hare-hare da ake kai wa tsarin ilimi, Falasdinawa sun kasance masu neman ilimi a koyaushe.

A lokacin intifada ta farko a 1988, a lokacin da aka rude Jami'ar Birzeit da wsauran manyan makarantu byn umarnin sojoji, Fallasdinawa sun nemi mafita don neman ilimi. An yi azuzuwan karkashin kasa a gidajen dalibai d malamai, cibiyoyin jama'a da ma wasu wuraren.

A wajen Falasdinawa, akwai labarai iri biyu idan aka zo batun ilimi. A gefe guda, wani yunkuri ne na nuna tirjiya. Ba wai yakin kwatar 'yancin koyo d koyarwa ba ne, har ma da gwagwarmayar wanzuwa.

Falasdinawa sun ci gaba da yin amanna kan karfin kawo sauyi da ilimi ke da shi. Juriyarsu, ta sanya ake kiran su da Samudawa, kuma ita ce ta sanya su suke ci gaba da matsawa gaba. Ilimi babban jigo ne ga asalin Falasdinawa, wanda ke da alaka ta kai tsaye da yunkurin samun kai.

A gefe guda, an mayar da ilimi wani makami ta hanyar mamayar da ake yi doon zalunta da karfa-karfa a kan Falasdinawa. Wannan na kara karfafa gwiwar Falasdinawa da dabbaka manufofinta na mulkin mallaka.

A yau, rusa ilimi ba wai rusa gine-gine kawai ba ne. Hari ne kan cigaban tunani, kayan gado na tarihi, da shugabanci na nan gaba.

Mamayar ba Falasdinawa kawai take nufa ba, tana kuma da manufar ruguza makomar al'ummarmu ta hanyar rufe bakunan wadanda za su yi jagoranci gobe. Amma hakan ba zai kashe mana gwiwa ba wajen gwagwarmaya.

A Gaza, rushe makarantu da manyan cibiyoyin ilimi, ba yana nufin rusa gine-gine ba kawai, har da ma yunkurin dakile cigaban kwakwalwa na tsawon shekaru. Kisan malaman kananan makarantu da jami'o'i, na nuni da yadda hare-haren ke rusa ilimi sosai.

Mamayar ba Falasdinawa kawai take nufa ba, tana kuma da manufar ruguza makomar al'ummarmu ta hanyar rufe bakunan wadanda za su yi jagoranci gobe

Duk da haka, a yayin da ake fuskantar wannan muzantawa, jama'ar Falasdinawa na ci gaba da farfadowa.

A yayin da Falasdinawa ke ci gaba da gwagwarmayar neman hakkokinsu, yana da muhimmanci kasashen duniya su bayar da gudunmowa ga kokarin na Falasdinawa, su kara daga muryoyinsu, sannan su nemi a yi gaskiya kan laifukan yaki da ake aikatawa a kan su. Matakin Falasdinawa ba iyakacin neman tsira suke yi ba, har ma da tsira ta hanyar samun ilimi.

TRT World