A makon da ya gabata, Shugaban Nijeriya kuma shugaban ECOWAS Bola Ahmed Tinubu ya aika tawaga zuwa Yamai babban birnin Nijar, karkashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya Abdulsalam Abubakar da Sarkin Musulmai Muhammad Saad Abubakar, wanda masarautarsa ce ke kula da Nijar kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.
Manufar ita ce a janyo ra'ayin jagororin juyin mulkin Nijar su sauka daga kan mulki.
Amma kuma wannan yunkuri na diflomasiyya bai samu karbuwa ba. ECOWAS ta sanya takunkumai na yanke Nijar daga huldar biyan kudade da tsarin hada-hada tsakanin kasashe mambobin kungiyar.
Kungiyar yankin ta ma yi barazanar amfani da karfin soji idan 'yan juyin mulkin na Nijar suka ki dawo da aiki da kundin tsarin mulki zuwa ranar Lahadin 7 ga Agusta.
Wasu masu nazari na bayyana cewa babu wani abu da zai faru a Nijar kuma komai zai ci gaba da tafiya daidai, saboda an samu juyin mulki a Sudan da Guinea da Mali da Burkina Faso amma ba abun da aka yi.
Amma kuma, abun da suka gaza fahimta shi ne yadda a boye ake samun kyamar Faransa da Turai a yankin sakamakon rashin kyakkyawan shugabanci tsawon shekaru, wadanda da su ne Amurka da Faransa suka dinga amfani wajen tabbatar da wanzuwarsu a yankin.
Faransa na samun kaso 15 cikin 100 na ma'adanin Yuraniyom da Nijar ke fitarwa, da kuma samun kaso 68 na makamashi gigawatt 3.6 da take fitarwa zuwa Turai tana samun Yuro biliyan uku.
Nijar ce kasa ta 27 a duniya wajen fitar da zinare da ya kai tan 34.5, kamar yadda Majalisar Cinikin Zinare ta Duniya ta bayyana, kuma Faransa ake kai wannan zinaren.
Kaso 50 na lalitar Nijar da sauran kasashe rainon Faransa na ajiye a baitilmalin Faransa, wanda abu ne da tsawon lokaci ya bayar da ta'azzara talauci a tsakanin 'yan kasar Nijar su kusan miliyan 26, inda kiyasin kudin kowanne dan kasar a shekara ya kama dala $1,330, inda aka kuma samu tashin farashi da kaso 29.
Abu da ake iya gani karara shi ne Yammacin Afirka na zama fagen gwajin kwanjin Rasha da China a bangare daya, a daya bangaren kuma na Faransa da Amurka.
Kasashe da dama a yankin Sahel da suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da Nijar da Nijeriya sun fuskanci hare-haren ta'addanci daga kungiyoyi masu alaka da Al Qa'eda.
Faransa ta kai dubban sojoji zuwa kasashen da ta yi wa mulkin-mallaka don yakar 'yan ta'adda tare da sojojin kasashen, kuma sansaninsu na karshe yana kasar Nijar bayan da ta kwashe sojojinta daga Mali da Burkina Faso.
Sai dai kuma, akwai zarge-zargen cewa sojojin Faransa ba su da gaskiya a yakin da ake yi da 'yan ta'adda a yankin, inda wasu ma ke zargin Faransa na kara rura wutar rikicin ne.
A ko yaushe Faransa ta dinga bayyana cewa tana kokarin ganin an hana yaduwar 'yan ta'addar a yankin.
A gefe guda, akwai kuma batun kutsawar dakarun Wagner na Rasha zuwa Yammaci da Tsakiyar Afirka. Wannan ya janyo gaba tsakanin Rasha da Yammacin duniya.
Wannan juyin mulki ya sake ta'azzara wannan adawa, inda Faransa ta harzuka bayan da dubban 'yan Nijar suka kwarara kan tituna suna goyon bayan 'yan juyin mulki, suna kuma daga tutar Rasha da rera wakokin goyon bayanta.
A yayin da Rasha ta soki juyin mulkin, ya bayyana karara cewa ba shi da kyau a yi amfani da karfi wajen dawo da kasar kan turbar dimokradiyya.
Sai dai kuma, Faransa na goyon bayan matakan da ECOWAS ke dauka. Wadannan matakai sun hada da yiwuwar amfani da karfin soji idan har 'yan juyin mulkin suka ki su dawo da aiki da kundin tsarin mulki.
Za a iya fahimtar damuwar Faransa saboda shugaban Nijar da aka hambarar Mohamed Bazoum ne kadai shugaban wata kasa a yankin Sahel da ke da kyakkyawar alaka da Faransa, wadda tuntuni ta babe da Mali da Burkina Faso bayan sojoji sun kwace mulki a kasashe.
Bututun iskar gas
Wani batu da ya shafi tattalin arziki kuma shi ne shirin babban aikin shimfida bututun iskar gas. Aikin shimfida bututu na 'The Trans-Sahara' zai kai albarkatun iskar gas na Nijar zuwa Aljeriya, daga nan zuwa Tekun Bahar Rum zuwa Italiya, sannan sauran kasashen Turai.
Bututun mai nisan kilomitoci da yawa zai hade gas din Nijeriya da bukatar gas ta Turai, wanda wannan mataki ne da Rasha ba za ta so ba, saboda ta san me ta yi asara sakamakon takunkumin da Turai ta saka mata kan bututan Nord Stream na I da na II sabod ayakin da take yi da Yukren.
Tare da yanayin da ake ciki a yanzu a Nijar, wannan aikin bututun zai zama batun adawa tsakanin Rasha da Kasashen Yamma.
Gaba da gogayyar manyan kasashen duniya na da illa babba ga yankin. Idan aka samu gasar ayyukan soji tsakanin manyan kasashe a yankin Sahel, to lamarin tsaro a yankin na iya tabarbarewa inda masu dauke da makamai za su ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Hakan za ta tabbata ne yayin da makamai suka ci gaba da yadu wa, kuma za a dauke hankalin kasashen daga kan 'yan ta'addar.
Duba da yadda manyan kasashen kawai sun damu da me za su samu ne kawai, ba wai Yammacin Afirka ne ya dame su ba, to dole kasashen Yammacin Afirka su sake tunani su kuma yi aiki don cigaban yankin.
Lamarin Nijar ya zama mai rauni a yayin da ECOWAS ke barazanar ga 'yan juyin mulki ta hanyar kakaba wa kasar takunkumai. Kungiyar yankin ta nace kan sai an dawo da kasar turbar dimokradiyya.
A yayin da yake da matukar muhimmanci a nace kan dabbaka dimokuradiyya, akwai kuma bukatar kula sosai don kar a bar wasu daga wajen yankin su shiga su dagula al'amura.
Akwai bukatar tattaunawar sulhu cikin gaggawa da hadin kan yankin, kuma a sanya bukatar yankin a kan gaba.
Kelvin Ayebaefie Emmanuel masanin tattalin arziki ne da ke Abuja, Nijeriya.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta gabatar ba sa wakiltar ra'ayoyi da manufofin TRT Afrika.