Yadda za a rika bai wa yara damar baje basirarsu don ci-gaban kimiyya a Afirka

Yadda za a rika bai wa yara damar baje basirarsu don ci-gaban kimiyya a Afirka

Galibi yara suna shaukin neman sani, sai dai akwai wadanda ba haka suke. Amma kuma yawancinsu suna da hazaka.
Akwai bukatar a kara bunkasa tsarin ilimi a kasashen Afirka da dama. Hoto: Reuters

Daga Elsie Eyakuze

Kirkira. Basira. Rashin jin tsaro. Dabarun kasuwanci. Wadannan kalmomi da ake yi wa masu neman aiki kuma saboda yadda ake yawan maimaita su kalmomin sun fara rage kimarsu.

Wannan wani abu ne da ake yawan amfani da shi a fadin duniya: a wannan zamani da ake yawan amfani da fasaha, wadannan su ne abubuwan da kamfanoni da dama suke ganin su ne za su kawo musu ci-gaba.

Akwai wata matsala daya: galibi tsarin karatu da hukuma ke tsarawa ba ya samar da yanayi na wanzar da kirkira da basira da sauransu wadanda suke kawo gagarumin ci gaba a fannin kimiyya.

Kafar yada labarai ta TRT Afrika ta mayar da hankali kan mutanen da suka gano ko kirkiro manyan abubuwa a fannin kimiyya kamar su Erasto Mpemba wanda ya rasu a watan Mayu.

Ya yi fice ne dalilin Mpemba Effect wato shi gano cewa ruwan zafi ya fi ruwan sanyi saurin daskarewa.

Mutane da yawa sun yi nazari a kan haka kuma wannann makala ta yi duba ne kan manyan bincike-binciken kimiyya.

Wasu dalibai makafi yayin da suke amfani da wata manhaja wadda ke taimaka musu yin karatu a wata makaranta a Legas. Hoto: Reuters

Abu biyu ne suka fi yin fice:Erasto Mpemba ya gano abin ne yana da shekara 13 a duniya kuma ya kwashe sauran rayuwarsa wajen bincike-binciken kimiyya.

Basirar da ba a amfana da ita

Wasu suna ganin haka ne yayin wasu kuma suke ganin akasin haka ne, amma makomar karamin yaron wanda ba ya gajiya da bincike-bincike da kuma neman ilimi abu mai dadin ji.

Erasto Mpemba bai zama masanin kimiyya ba a karshe. Na samu damar magana da shi.

Ya yi ritaya a lokacin kuma daga nan ne ya tafiyar da rayuwarsa cikin sauki, duk da cewa ya yi suna a tsakanin masana kimiyya na duniya.

A matsayinsa na yaro a shekarun 1960, da gani babu tambaya ya yi tsayuwar daka wajen gano abin da ya gano har kuma aka yi amannar cewa haka ne, ba kuskure ba ne.

Duka wadannan sun faru ne a karkashin tsarin karatu mara karfafa gwiwar masu neman ilimi.

Erasto Mpemba ya rasu ne a watan Mayun shekararg 2023 amma ba za a iya manta da ayyukansa ba. Hoto: TRT Afrika.

Ina ganin wannan matsalar duniya ce, idan kana son magance talauci a Tanzaniya hanya daya ita ce magance matsalar Erasto Mpembas wato yara masu basira da ake haihuwa, su rayu kuma har su mutu ba tare da yin amfani da dimbin basirarsu ba ta hanyar da sauran jama'a za su amfana.

Sai dai babu shakka akwai kasashe da tsarin karatunsu yake iya zakulo hazikan dalibai, masu basira da fikira.

Nagartattun cibiyoyin ilimi

Ra'ayin shahararren masani kan ilimi Dokta Ken Robinson ya ce akwai danganta tsananin samar da 'yan kasa wadanda za su kasance masu aiki tukuru kuma masu biyayya ga kasarsu.

A daya bangaren kuma akwai batun dakile masu basira da gwaurayuwar mutane mabambanta.

Yara suna daukar darasi a fannin robotics a Kenya. Hoto: AA

Abu ne mai wuya ka toshe kunnenka daga surutai kuma ka koma kan gaskiya game da rayuwar dan Adam.

Yayin da muke magana kan irin aikace-aikacen da fasaha za ta iya yi masu dimbin yawa, wasunmu suna da fatan za a iya amfani da kimiyya da fasaha wajen magance talauci da yunwa da kuma samar da ingantaccen kiwon lafiya.

Mutum nawa ne a cikinmu suke masani kan abin da ake bukata lafin hakan ya yiwu? Nagartattun jami'o'i da kwararrun malamai da dalibai masu hazaka ake bukata.

Ko da yake, idan muka koma batun Mpemba wanda a shekara 13 ba tare da taimakon kowa ba, bai samu karatu mai inganci ba, ya gano wani abu kuma ya rike shi kamam.

Irin Erasto Mpembas yawa muke da su? Danka yana cikinsu? To idan haka ne, to ya kamata mu rika sauraren basirar yara da wadanda suke daban da saura. Wannan ita ce hanyar karfafa musu gwiwa.

Marubucin, Elsie Eyakuze, wani kwararre ne a fannin yada labarai kuma mai wallafa labarai a intanet wanda yake zaune a birnin Dar es Salaam a Tanzaniya.

A kula: Wannan ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT Afrika ba ne.

TRT Afrika