Jirgin TCG Anadolu, shi ne babban jirgin yakin Turkiyya kuma shi ne jirgin ruwan yaki na farko a duniya da yake daukar jirage marasa matuka (UCAV), ya koma tashar jiragen ruwa ta Sarqyburmu bayan kammala zagayensa a kogin Bosphorus a birnin Istanbul, a Turkiyya ranar 23 ga watan Afrilu. Hoto: AA

Daga Ibrahim Karatas

Jirgin ruwan Anadolu zai iya tafiyar kilomita 16,000 ba tare da yada zango ba, kuma yana iya gudun kusan kilomita 40 a awa daya, zai iya daukar jirage marasa matuka 41 ko jirage masu saukar ungulu 29 (ko jirage marasa matuka 11 ko jirage masu saukar ungulu 10 a fadin murabba'in mita 5.440, ko kuma jirage marasa matuka 30 ko jirage masu saukar ungulu 19) tare da dakarun soji 1,223.

Haka zalika, zai iya jigilar motocin soji 27 da manyan tankokin yaki guda 30. Har ila yau za a iya mayar da jirgin ruwan asibiti don duba marasa lafiya lokacin wani bala'i a kasa.

Tun da farko an kera jirgin TCG-Anadolu don ya zama wajen saukar jiragen yaki wanda sojin ruwan Turkiyya za ta rika amfani da jirage marasa matuka da jiragen yaki.

Daga bisani, sai aka sauya shirin, injiniyoyin Turkiyya suka mayar da shi mai daukar jirage marasa matuka, irinsa na farko a tarihin sojin ruwan kasar.

Jirgin Anadolu zai iya kai farmaki ta amfani da jirage marasa matuka kamar Bayraktar TB-3 da Akinci da Kizilelma da kuma kananan jiragen yaki kamar Hurjet. Jirgi mara matuki na TB-3 zai tashin farko a farkon shekarar 2024.

Jirgin TCG-Anadolu ya fita daban ta fuskoki da dama kuma zai kara wa sojin Turkiyya karfi.

Kodayake yana kama da jirgin ruwan kasar Spain mai suna Juan Carlos I, the catapult, wanda shi ma jirage marasa matuka da kananan jiragen yaki za su iya tashi a kansa.

Kwarin gwiwa da karsashi

Yayin da aka tanadi wurin da jirage masu saukar ungulu za su iya sauka, a jirgin Anadolu an tanadi karanin titin jirgin sama don jiragen da suke bukatar hakan.

Irin wannan ci gaban da aka samu ya zaburar da sojin ruwan kasashen Amurka da China da kuma Japan, inda suke kokarin sun samar jirgi kamar Anadolu.

Idan suka kwaikwayi salon sojin Turkiyya, to za a iya cewa Turkiyya kawo wani sabon abu a fanni sojin ruwa a duniya. Jirgin yakin ya kara bunkasa karfin sojin Turkiyya a fuskar jiragen ruwa bayan gwamnatin kasar ta gina wannan katafaren jirgin.

Shugaba Erdogan ya ce za su ci gaba da kera jirgin ruwa babba maibdaukar jiragen sama.

Kamfanin kera jiragen ruwa na kasar Spain ya taimakawa wajen samar TCG-Anadolu, ya ce babban jirgin da za a kera nan gaba za a samar da shi daga gida.

Wannan ya sa, abu mafi muhimmanci ga Turkiyya ita ce fasahar kera wadannan jiragen.

Masu kera jiragen 'yan Turkiyya za su rika kera wa kwastomominsu na ketare, abin da zai sa kwarewarsu ta kawo kasar kudin shiga.

Sharar fage

Bugu da kari, sojin Turkiyya za su iya amfami da wasu jiragen sama a kan jirgin ruwan. Hakan yana nufin maimakon kai wa abokan gaba hari da jiragen ruwan yaki, jirage marasa matuka za su iya tashi daga kan jirgin Anadolu kuma su kai hari a wuri mai nisan kilomita 1,000 daga inda jirgin ruwan yake.

Bayan kai wa abokan gaba hari da jirage marasa matuka da ke tashi a kansa, jirgin zai iya kasancewa sansanin sojan sama a teku.

Kuma za a iya tsara ayyuka soja daga wurare masu nisa. Misali, idan da a ce an tsara aikace-aikacen sojin Turkiyya a Libya, to da sakamakon ya kasance cikin sauri kuma kamar yadda aka tsammata.

Turkiyya tana kewaye da tekuna uku ne saboda haka akwai yiwuwar za ta fi fuskantar babbar barazanar tsaro ne daga teku.

Iya karfin sojan ruwan iya yadda za su zama cikin shiri. Jirgin ruwan TCG-Anadolu zai yi jigilar dakaru da jirage da makamai da sauransu daga wata teku zuwa wata da adadi mai yawa kuma tare da kashe kudi sosai ba.

Bisa la'akari da wannan gudunmuwar ga sojin Turkiyya, wannan sabon jirgin zai bude hanya ga nasarori q siyasance.

Babban makami a tarihi

Da farko, tun yanzu za a iya tura da dakaru da makamai masu tayin yawa.

Turkiyya tana kara karfafa karfin fada ajinta a yankin. Jirgin TCG-Anadolu kamar wani sansanin sojin tafi da gidanka ne wanda zai iya aiki daga kowace irin teku.

Mutum zai iya ganinsa kusa da gabar ruwan kasar Libya ko kuma a tekun Red Sea ko Baltic.

Shakka babu wannan zai karfafa gwiwa ga kawayen Turkiyya (misali wadanda suke kungiyar NATO) kuma hakan zai jawo damuwa ga kasashe abokan gabar Turkiyya.

Zai iya ma sanya wadanda suke takaddama da Turkiyya warware matsalolin cikin ruwan sanyi.

Za a iya cewa Anadolu babban makami ne da zai ssmar da yanayin da zai kawo karshen takaddama.

Gaba daya za a iya cewa jirgin ruwan TCG-Anadolu shi ne babban makamin yakin da Turkiyya ta taba samarwa kuma zai yi tasiri a siyasa da tattalin arziki a yankin.

Ya tabbatar da batun nan da ake cewa manyan ayyukan da aka yi su a lokacin da ya dace suna kara kimar shugaba da kasarsa da sauransu.

Jirgin ruwan TCG-Anadolu ba abu ba ne kawai da ya jibanci sojoji amma babban aiki da ke nuni da burin da Turkiyya ke da shi da himmarta da kuma tsare-tsaren da kasar ke da shi a shekaru masu zuwa.

Marubucin, Dokta Ibrahim Karatas, mai sharhi ne kan harkokin siyasa kuma dan jarida ne wanda ya kware a harkokin manufofin kasashen wajen Turkiyya da Gabas ta Tsakiya da kuma tsaro.

A kula: Wannan makala ta kunshi ra'ayi da fahimtar marubucin ne, amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT Afrika ba ne.

TRT World