Daga Johnson Kanamugire
Yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya shiga shekara ta biyu, ‘yan watanni da suka gabata.
Yakin na ci gaba da haifar da wahalhalu ga masu amfani da kayayyakin waje da ke cikin kasashen nahiyar Afirka.
Hakan na zuwa ne yayin da matakan da gwamnatoci suka dauka na rage radadin yakin kan samar da abinci, yake fuskantar tarnaki.
Nahiyar Afirka tana shigo da kayayyaki da suka kai na dala biliyan 45 duk shekara, duk da cewa nahiyar ce ke da kashi 60 cikin 100 na kasar noma a duniya, kuma take da matasa masu jini a jika.
Lokaci kawai ake jira kafin matsalar samuwar abinci sakamakon yakin Ukraine ta fara shafar Afirka, wadda a baya aka danganta da annobar Covid.
A zahiri, kasashe kadan ne a nahiyar aka samu suna da adadin abincin da zai rage barazanar matsalar samar da abinci.
Bayan wucewar annobar Covid, duniya ta fada cikin kalubalen tarnakin kasuwancin duniya, wanda ya shafi samar da man fetur da gas da hauhawar farashin kayayyaki.
Harkokin noma da kiwo a Afirka sun dogara matuka kan kayayyakin da ake shigowa da su, kamar takin zamani da sinadaran hadi.
Wannan ya haifar da karuwar kudin sarrafa komai, daga abinci har zuwa kayan masarufi.
Hakan yana cutar da masu amfani da kayayyakin, musamman wadanda suke da karancin samun kudi, da rukunin mutanen da ke da’irar talauci.
Wannan ya bude kofar rashin tsaro wajen samar da abinci a cikin gida, musamman ya nuna a fili karancin tasirin alwashin zuba kudi a harkokin noma da kiwo, da batun inganta samar da abinci a cikin gida.
Gaba daya yanayin da ake ciki yana nunar da damuwar da aka dade da ita, game da gazawar shugabannin Afirka wajen cika alkawari da suka yi karkashin Shelar Malabo ta 2014.
Shelar ta kunshi amincewa da kuduri a fadin nahiyar, na zuba jarin kashi 10 cikin 100 na kashe kudin gwamnati zuwa harkokin noma da kiwo, a kokarin magance yunwa da talauci cikin shekaru 10.
Kokarin bai wadatar ba
A halin yanzu shekaru tara bayan wannan shelar, kasa daya ce kawai - Rwanda - take kan turbar cimma wannan manufa zuwa shekarar 2025.
Karin kasashe uku da suka kasance suna cimma wannan manufa har zuwa shekarar 2019, sun kasa, a cewar rahoton shekara bibiyu wanda Tarayyar Afirka ta wallafa a Maris din 2022.
Rahoton ya samu ne sakamakon wasu dabarun hadin gwiwa na kungoyin da ke nahiyar, don bibiyar cigaban da kasashe mambobi suka samu wajen zartar da Shelar Malabo.
Duk da sun samu cigaba, Rwanda da Zimbabwe da Ghana sun samu matakin goman farko cikin kasashe, wadanda suka samu hauhawar farashin abinci a duniya, bisa gwajin Bankin Duniya na baya-bayan nan. Rwanda ta samu hauhawa da ta kai kashi 30 cikin 100.
Duka-duka, bisa dalilan kalubalen baya da kuma matsalolin yanzu, yunkurin gwamnatoci a nahiyar ba ya samar da wani kyakkyawan fata kan magance talauci da yunwa cikin shekaru kadan masu zuwa.
Sai dai fa idan gwamnatocin sun mai da hankali kan kara zuba jari a harkar noma da kiwo, da tallafawa samar da kayayyaki a cikin gida, da kasuwancin kayan noma tsakanin kasashe.
Tasirin yakin Rasha da Ukraine yana shafar mutane miliyoyi a fadin nahiyar, bayan shekara daya da fara yakin.
Matsalolin da ake da su yanzu suna lahanta ikon kasa na samar da abinci don ciyar da al’ummominta.
Nahiyar tana da daya cikin uku (miliyan 283) na al’ummar duniya miliyan 850 da ke fama da yunwa.
Shugabannin Afirka da suka taru wajen taron kolin da aka yi wa lakabi da “Ciyar da Afirka: ‘Yancin Samar da Abinci da Juriya”, wanda aka yi a Dakar babban birnin Senegal, sun gano cewa adadin zai iya tashi idan aka bar shi sakaka.
Taron kolin ya taimakawa nahiyar tara dala biliyan 50 domin maganin matsalar samar da abinci.
Kawo daukin da gwamnatoci a nahiyar suka yi ya mayar da hankali ne kan tallafin man fetur, da takin zamani, da man girki, da hatsi, da sauran kayayyakin da ake bukata a harkar noma da kuma kayayyakin hadi na masana’antu.
Sannan akwai neman hanyoyin maye gurbin kayayyakin da ake shigowa da su.
Amma duk da haka, wannan bai kawo wani babban sauki ba ga wahalhalun da mutane ke sha yayin siyan kaya a kasuwa.
Tattalin arzikin kasashen Afirka yana kara fuskantar wahalar ci gaba wajen biyan tallafi, sakamakon cewa ba za a iya fadada tallafin zuwa duka kayayyaki ba, wadanda farashinsu ke tashin gwauron zabi.
Wahalhalun na dada kazancewa sakamakon munin yanayi, kamar na karancin ruwan sama, da fari, wadanda ke shafar noman damina a sassa da yawa na nahiyar.
Dole ‘yan siyasa su bar neman hanyoyin gaggawa wajen warware matsalar samar da abinci ko abinci mai gina jiki. Ya wajaba su fitar da mataki mai dorewa don ceto lamarin, sannan su gina tsari mai juriya daga sauran matsalolin.
Ya kamata dabarun su mayar da hankali kan tallafawa shirye-shirye na cikin gida wadanda za su tunkari matsalar samar da abinci ta yau da ta gobe, musamman hanyoyin da za su karfafa samar da hatsi da dabbobi.
Cibiyoyin harkar noma
Bugu da kari, dole su cire tarnakin kasuwanci tsakanin kasashe, domin a bayar da dama ga manoma da kuma yankunan noma su iya hada-hadar kayan abinci cikin sauki.
Kasuwancin cikin gida da ke gudana a Afirka karkashin tsarin kasuwancin bai-daya na (AfCFTA), wani mataki ne da ya dace.
Shirye-shirye kamar shirin samar da cibiyoyin masana’antun noma cikin yankunan Afirka, wanda Tarayyar Afirka take jagoranta don inganta samar da muhimman kayayyakin goma, zai iya sauya akalar nahiyar zuwa kan turbar ciyar da tarin al’ummominta masu karuwa.
Haka nan, tamkar alwashin da aka dauka a Shelar Malabo, aiwatar da wadannan shirye-shirye sun dogara ne kan karfin halin daidaikun kasashen.
Shin akwai yiwuwar kalubalen da matsalolin ke janyowa ga miliyoyin mutane a nahiyar, zai sa ‘yan siyasarmu su yi hankali a wannan karon?
Marubucin dan jarida ne mai rubutu kan batutuwan al’umma a kafofi daban-daban