'Yan kasar Burkina Faso yayin zanga-zanga tare da daga tutar Rasha bayan juyin mulkin soji a kasar/ AA

Hare-haren sojojin Rasha da takunkumi da Kasashen Yamma suka kakaba mata ya kawo tsaiko ga harkokin kasuwanci da tattalin arzikin yankin Afirka.

Amma duk da haka, ba nan kadai gizo ke sakar ba.

Kusan shekara daya bayan Rasha ta fara abin da ta kira da "hare-haren sojoji na musamman" a Ukraine a 24 ga Fabrairun bara, kugin tankoki da radadin yakin yana kai wa har a Afirka.

Yakin ya zo ne a lokaci mafi tsanani ga yankin Afirka, wanda shi ne mafi yawan mutane na biyu a duniya.

Yanki ne da yakin ya zo masa a daidai lokacin da yake farfadowa daga masassarar da annobar Covid-19 ya jefa shi.

Babu alamar yakin ya kusa karewa. Haka shi ma tabarbarewar tattalin arzikin Afirka- wanda ya fi ta'allaka da abincin da ake shigowa da shi da kuma makamashi.

Hauhawar farashin iskar gas da man fetur saboda yakin, ya jawo hauhawar farashin sauran kayayyakin masarufin, wanda hakan ke nuni da cewa tabarbarewar tattalin arzikin zai cigaba da lallasa Afirka na tsawon lokaci.

Hauhawar farashin fetur

Kasar Uganda tana cikin kasashen Afirka da har yanzu suke cikin tsanani saboda yakin, wanda aka fara kimanin wata daya bayan kasar ta dage dokokin kullen annobar Covid-19.

Yakin ya kuma jawo hauhawar farashin fetur a wasu kasashen Afirka/Photo AP

Abin da yakin ya fara shafa shi ne farashin man fetur- wanda lita daya da ya ke dala 1.2 ya koma dala 2 tun daga watan Maris zuwa Dismban 2022.

Duk da cewa farashin man ya koma Dala 1.5, amma har yanzu 'yan Uganda suna dandana zafin hauhawar farashin.

Kasar Uganda ba ta kayyade farashi kamar kasashen Kenya da Rwanda saboda yanayin dokokinta na tattalin arziki masu sauki.

Wannan ya hana gwamnatin kasar saka baki a batun farashin man. Sai dai tsarin ya taimaka wajen hana karancin man da bunburutunsa.

Wasu 'yan siyasa a Afirka sun alakanta wahalar da 'yan Afirka suke fuskanta da takunkumin da kasashen Yamma suka kakaba wa Rasha.

A kasar Kenya, yakin na Ukraine ya shafi harkokin shigowa da fitar da kayayyakin kasar musamman bayan takunkumin da aka kakaba wa Rasha din.

Wannan ya jawo hauhawar farashin fetur, wanda shi kuma ya jawo hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayayyaki da ake hadawa a cikin kasar.

Hana fitar da kayayyaki daga kasar, wanda aka kiyasta ya kusa Ksh biliyan 10 (Dala miliyan 7.5) a shekara, sannan aka dakatar da shigowa da fitar da kwantena na wucin gadi daga Rasha saboda takunkumin.

Kimanin wata biyu bayan fara yakin Ukraine, kasar Kenya ta sha fama da karancin man fetur. Matsalar ta sa gidajen mai da dama suka rufe, sannan farashin kayayyakin abinci ya tashi.

A watan Yuni, masu masana'antun Kenya sun koka da yadda Dala ta yi tsada saboda rashinta, wanda shi ma aka alakanta da yakin na Ukraine, wanda ya jawo asara a asusun kasar wajen kasar.

Matsalar abinci

Yankin Afirka, kamar sauran yankunan duniya, yana matukar dogaro da Rasha da Ukraine wajen fulawa.

Yakin Ukraine da kuma takunkumin da aka kakaba wa Rasha ya jawo tsaiko wajen raba fulawar, wanda hakan ya jawo karancinta a kasashe da dama.

Kasar Kenya-wadda take shigo da kashi 30 na fulawarta daga Rasha da Ukraine- ta sha fama da karancin fulawa saboda boye ta da aka rika yi.

Wasu kasashen na Afirka da dama suma suna dogara ne da fulawar da ake shigowa da ita. Kamaru da Djibouti da Burundi da Togo da Senegal da Jamhuriyar Dimokradiyar Kongo (DRC) da Tanzania da Rwanda da Togo da Libya da Mauritaniya da Namibiya duk suna shigo da kashi 50 zuwa kashi 70 da fulawar da suke amfani da it's ne.

Su kuma Madagascar da Masar suna amfani da kashi 70 zuwa 80 na fulawar da aka shigo da ita ne.

Somalia tana shigo da sama da kashi 90 ne na fulawa. Sannan Eritrea ce ta fi shiga tasku, domin daga Ukraine da Rasha ne take shigo da hatsin da ake amfani da shi kasar baki daya.

Wani abun ban mamaki shi ne yadda Eritrea din ta kasance cikin kasashe biyar kacal da suka kada kuri'ar yin watsi da yunkurin Shugaban Rasha, Vladimir Putin na manaye wasu yannkuna hudu na Ukraine.

Habasha ba ma ta shiga zaben ba. Sai washegari ne Firayi Ministan kasar, Abiy Ahmed ya ce rikici a kasarsa ya nuna yadda garuruwa da iyalai da hanyoyin samun abinci suka shiga tasku saboda yakin.

"Duk da cewa za a iya maye asarar dukiya da aka yi a yaki, yadda mutane za su dawo hayyacinsu shi ne fargabar kasashe," inji Abiy.

Samar da abinci yana da muhimmanci ga 'yan Afirka, sannan karancinsa wanda yaki ke jawowa ba karamar matsala ba ce da kasashen da a yanzu ma fama suke da matsalolin sauyin yanayi, da yaki da kuma matsalolin da aka shiga saboda annobar Covid-19.

Tunda kasashen Afirka da dama suna dogaro da noma, yakin Ukraine ya shafi shigo da takin zamani daga Rasha. Misali Ghana na shigo da kashi 50 na takin zamani ne daga Rasha.

Daukin gaggawa ta hanyar diflomasiyya

A bara, Kungiyar Samar da Abinci ta duniya, wato World Food Programme (WFP) ta samar da agajin abinci da sauran tallafi ga kasashen Afirka da yakin ya fi shafa.

Rasha da Ukraine sun tallafa wa sama da mutum miliyan biyu da suke fama da yunwa a Habasha/Photo Reuters

Sai kuma yarjejeniyar diflomasiyyar da kasar Turkiyya ta shiga tsakani, inda a 22 ga Yulin bara Rasha da Ukraine suka tallafa wa sama da mutum miliyan biyu da suke fama da yunwa a Habasha.

Bisa kokarin Turkiya, sama da tan 23,000 na hatsi aka kai kasar ta Habasha wanda Kungiyar WFP ta kai.

Haka ita ma Kungiyar Agaji ta Red Cross and Red Crescent Societies (IFRC)) a wani gangaminta na samar da abinci a Afirka, mai suna Pan-Africa Zero Hunger Initiative, ta tallafa wa wasu kasashen da yakin ya illata, ciki har da kasar Senegal.

Kasar Senegal tana shigo da sama da kashi 50 ne na hatsin da ake amfani da shi a kasar da fulawa daga Ukraine da Rasha.

Wannan yakin ya nuna bukatar da ke akwai na karfafa tattalin arzikin Afirka maimakon mayar da hankali a kan bangaren tsaro kawai.

Lokaci ya yi da masu ruwa da tsaki a Afirka za su karfafa diflomasiyyar yankin da karfafa kungiyoyin yankin irinsu Tarayyar Afirka da Kasashen ECOWAS da sauransu domin habaka tattalin arzikin yankin.

Har yanzu ana cigaba da yakin Ukraine, sannan kasashen Afirka na cigaba da fama da tsadar rayuwa. Wannan lamari zai cigaba da hana cigaba a kasashen yankin da dama.

TRT Afrika