TCG Anadolu / Photo: AA

Ra'ayi: Daga IBRAHIM KARATAS

Jirgin da aka yi wa lakabi da TCG-Anadolu yana iya tafiyar mil 9,000, kuma zai iya gudu da saurin knot 21.

Yana dauke da jiragen yaki marasa matuka UCAV 41, da jirage masu tashin ungula 29. Yana kuma daukar jami’an soji har 1,223.

Jirgin yana iya daukar jiragen UCAVs guda 11 ko masu saukar ungulu 10, a kan farfajiyarsa mai fadin murabba’in mita 5.440, tare da jiragen UCAV 30 ko masu saukar ungulu 19 a rumfar ajiyar jirage.

Wani abin burgewa da jirgin shi ne yana iya jigilar motocin yaki da ke iya shiga ruwa, har guda 27, da kuma tankokin yaki 30. Haka nan ana iya amfani da jirgin a matsayin asibiti a lokacin bukata.

Da fari, an gina jirgin ruwa na TCG-Anadolu a matsayin farfajiyar saukar jirgi, wanda Sojin Ruwan Turkiyya suka shirya zuba jiragensu masu saukar angulu da jiragen yaki.

An sauya shirin, sannan injiniyoyin Turkiyya suka sauya fasalinsa zuwa jirgin jigilar jiragen sama na yaki marasa matuki. Wannan jirgi shi ne na farko a tarihin sojin ruwa na kasar.

Jirgin na Anadolu zai iya aiki da jiragen yaki kirar Bayraktar TB-3, da Akanci da drones din Kizilelma, da kuma jirgin Hurjet mara nauyi. Jirgin TB-3 zai fara tashi daga kan TCG-Anadolu a farkon shekarar 2024.

TCG-Anadolu fitacce ne a fannoni da yawa, kuma zai karfafa kaimin sojin Turkiyya. A fasahance, jirgin Anadolu yana da kira irin ta jirgin Sifaniya na Juan Carlos I, mai harba jirage marasa matuki da kuma kananan jiragen yaki.

Duk da irin wannan jirgin ruwan ana gina shi don saukar jirage masu saukar ungulu ne, a kan jigin Anadolu ba don kawai jirgi mai tashin ungule aka yi shi ba, har da jiragen da ke bukatar gajeren filin tashi.

Wannan fasalin na jirgin ya janyo sojojin ruwan wasu kasashen suna kwaikwayar Turkiyya, inda sojin ruwa na Amurka da China da Japan aka ruwaito suna shirin mallakar irin wannan jirgi.

Idan suka bi wannan matakai na sojin Turkiyya, kenan a karon farko Turkiyya ta fito da sabon salo ga sojojin ruwa a duniya.

Jirgin ruwan yaki na TCG-Anadolu zai bai wa masana’antar gina jirgin ruwa ta Turkiyya da ma gwamnati kwarin gwiwar gina manyan jiragen ruwa.

Shugaba Erdogan ya riga ya ambata cewa Turkiyya za ta fara gina manyan jiragen ruwa masu daukar jiragen yaki na sama.

Yayin da kamfanin Sifaniya na Navantia ya samar da musayar fasahar gina jirgin, da zayyanarsa da muhimman bangarorin jirgin TCG-Anadolu, jirgi na gaba da za a gina za a yi shi ne da fasahar cikin gida.

Sakamakon haka, daya daga cikin gajiyar da Turkiyya za ta samu shi ne fasahar gina irin wannan jirgin ruwa. Akwai yiwuwar masu gina jirgi a Turkiyya su fara samar wa da sauran kasashen waje don samun kudin shiga.

Har ila yau, rundunar sojin Turkiyya za ta yi amfani da wasu daga jiragenta don aikin sojin sama da sojin ruwa.

Wannan na nufin kai farmaki ga abokan gaba ta jirgin ruwan yaki zai yiwu har zuwa kilomita 1,000 daga jirgin ruwan.

Baya ga kai farmaki yayin da jirgin ke daure, jirgin ruwan ya kara zangon da jiragen yaki marasa matuka zai iya cimmawa, saboda kasancewarsa filin jirgi da ke kan ruwa.

Kasancewar tekuna uku ne suka zagaye Turkiyya, barazanar tsaro ga kasar an fara tunanin za ta zo ne daga teku. Kenan karfin sojin ruwan kasar zai taimaki tsaron kasar.

TCG-Anadolu zai yi jigilar mayaka, da kayan yaki, da jiragen sama, da makamai, daga teku zuwa teku ba tare da kashe kudi masu yawa ba.

Bisa la’akari da gudunmowa ga sojin Turkiyya, sabon jirgin ruwan yakin zai kawo cigaban siyasa. Da farko, sakamakon karfi jigilar sojoji da kayan yaki, hakan zai daukaka matsayin Turkiyya a yankinta.

TCG-Anadolu tamkar wani sansani soji ne amma wanda yake tafiya, kuma ake jibge su a kan teku. Za ka iya gano shi kusa da gabar Libiya ko Bahar Maliya ko Tekun Baltic.

Wannan zai nuna karfin Turkiyya kuma ya kara mata karfin gwiwa cikin abokanta da kawaye (misali wadanda suke cikin NATO). Kuma zai saka damuwa a zukatan makiyanta.

Jirgin zai iya sa wa wadanda ke hamayya da Turkiyya su nemi maslaharsu da ita cikin lumana. Wato dai, Anadolu, wani mataki ne na nuna karfi da zai sauya yanayin abubuwa da rikice-rikice.

A takaice dai, TCG-Anadolu shi ne mafi girman makamin da Turkiyya ta taba samarwa. Kuma zai yi tasiri a siyasa da tattalin arziki da zamantakewar yankinta.

Hakan wata shaida ce ta cewa manyan ayyuka idan aka yi su sanda suka dace a kan bukatun da suka dace, suna iya inganta tagomashin shugaba da kasarsa, baya ga sauran alfanu.

TCG-Anadolu ba ci gaba ne na soji kadai ba, wani babban kadarko ne mai nuna burin Turkiyya da kokarinta da kuna dabarunta na cigaba.

Togaciya: ra’ayoyin da marubucin ya gabatar a nan ba lallai su nuna ra’ayi ko mahangar editocin TRT World ba.

TRT Afrika