Bayan sanarwar yarjejeniyar, an gudanar da wani biki a Mogadishu babban birnin Somalia. Daruruwan mutanen da suka halarci bikin ne dauke da tutocin Turkiyya da Somaliya. / Hoto: AA  

Daga Ibrahim Alegoz

Ministan harkokin tsaron Turkiyya Yasar Guler da takwaransa na Somaliya sun gana a Ankara a kwanan nan, inda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da hadin gwiwar tattalin arziki.

A ranar 21 ga watan Fabrairun shekarar nan ne majalisar ministocin kasar Somaliya ta amince da yarjejeniyar, wadda za ta taimaka wajen kafa rundunar sojin ruwa ta hadin gwiwa, inda Turkiya ta yi alkawarin kare ruwan Somaliya na tsawon shekara goma, tare da taimaka mata wajen ciyar da albarkatun ruwan kasar gaba.

Ba kawai yarjejeniyar ta tsaya a iya samar da wata dama ta musamman ga haɓaka hanyoyin tattalin arziki da dabarun tsaro na Somaliya ba ne, har da tasirinta ga yankin, sannan akwai bukatar masu ruwa da tsaki a duniya su goyi bayanta a kan hakan.

Albarkatun kasa da kasa ba su da iyaka, sannan ɗorewarsu ba shi da iyaka na tsawon lokaci.

Mene ne ya kamata a yi tsammani daga yarjejeniyar, kuma ta yaya za ta taimaka wajen samar da tsaro a yankin da kuma kyautata jin dadin jama'a da zarar an aiwatar da ita?

An dade ana kallon yankin kusurwar Afirka a matsayin wani yanki mai matukar muhimmanci a fagen harkokin siyasa manyan kasashe a lokacin yakin cacar-baka saboda inda yake, ta hanyar zama yankin da ke tsakanin mayan kasashe biyu.

Sai dai muhimmacinsa ya ragu bayan kawo ƙarshen yakin cacar bakar, ya sake sabunta matsayinsa ne a tsarin da ake kira yakin duniya kan ta'addanci.

Yankin ya hada gabar Tekun Bahar Maliya da Tekun Aden, da ke maƙwabtaka da hanyoyin ruwan Saudiyya da Yemen, sannan hanya ce da ke kaiwa zuwa tekun indiya da mashiga ce mai matukar muhimmaci wacce ke zuwa ga tekun Bahar Maliya.

Kusurwar Afirka ya ga wasu daga cikin yaƙe-yaƙe mafi muni a ƙarni na 20, kamar yaƙin Habasha da Somaliya na shekarar 1977 zuwa 78 da rikici kan iyakar Habasha da Eritriya na shekarar 1999 zuwa 2000 a farkon karni na 20.

Ko da yake, ba a taɓa samun wani al'amari na siyasa a yankin ba da ya samar da sauyi mai kyau kamar yadda aka samu wargajewar ƙasar Somaliya a 1991 ba.

Abin da ya biyo baya ya gabatar da kalubale guda biyu ga tsarin tsaron duniya: bullar ayyukan ta'addanci bayan tsoma bakin sojojin Habasha a Somaliya a karshen shekarar 2006 da kuma barazanar 'yan fashin teku a gabar Tekun Somaliya da Mashigin Tekun Aden.

Wadannan al'amura guda biyu sun yi nuni cewa, a cikin daya, tashin hankalin da ba a iya kayyade shi ba, yana da alaƙa da yadda ake amfani da karfin tuwo wajen tabbatar da zaman lafiya a tsaron kasa .

Kasashen duniya sun kashe daruruwan biliyoyin daloli a shirye-shiryen gina kasar Somaliya tun daga shekarar 1991 tare da kashe makudan kudade wajen magance ayyukan ta'addanci da kuma fashin teku a mashigin tekun Aden.

Ba shakka, aiki ne mai matukar wahala da ke tafe da kalubale, Sau tarim yunƙunrin cikin gida yana tafiya kafada da kafada da hanyoyin da ake bi na waje, kuwa akwai yiwuwar samun nasara da akasin hakan a koyaushe.

Duk da ƙalubalen da ke ƙasa, duka suna koyarwa zuwa ga shirye-shiryen gaba. Wataƙila yanzu ne lokacin da za a bincika wasu hanyoyin da za su ciyar da Somaliya gaba.

Neman kwanciyar hankali a yankin Kusurwar Afirka

A shekarar 2011, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Mogadishu babban birnin kasar bisa ga gayyatar da shugaban kasar Somaliya na lokacin Sheikh Sharif ya yi masa, a wani yanayi na fari da bala'o'in jin kai da suka shafi miliyoyin rayuka a kasar ta Somaliya.

An dangana ziyarar a matsayin wani sauyi ga Somaliya, domin ita ce ziyara ta farko da wani shugaba na wata kasa da ba Afirka ya taba kaiwa kasar tun shekarar 1991.

Tabbas, a ranar 21 ga Fabrairu, 2024, Shugaban Somaliya Mahmoud ya yi wata sanarwa bayan taron majalisar ministocin kan cewa, “Somaliya tana da kawaye da abokai da yawa waɗanda suka goyi bayan yunƙurin farfadowarta.

Kuma, ɗaya daga cikin abokan da suka cancanci girmamawa ta musamman ita ce Turkiyya. Turkiyya ta goyi bayan Somaliya wajen kawar da bala'in yunwa a shekarar 2011, kuma ziyarar Firaminista Erdogan a lokacin na da matukar muhimmanci."

Ziyarar ta bude wani sabon babi na dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, tun daga karni na 16.

Tun daga shekarar 2011, Turkiyya ta gudanar da shirye-shiryen diflomasiyya na jin kai musamman ta hanyar ba da gudumawar gaggawa ga bukatun jin kai na mutanen Somaliya, kamar abinci da lafiya da kuma matsuguni.

Taimakon jin kan ya biyo bayan tallafin fasaha da ayyukan haɓaka ilimi don ɗaga hanyoyin ƙasar Somaliya a sassa daban-daban.

Alal misali, a cikin watan Satumban 2017, an kaddamar da sansanin horas da sojoji na TURKSOM a Somaliya a matsayin wani bangare na matakan tsaro, daya daga cikin muhimman matakan gina kasa.

TURKSOM na bayar da horo ga sojojin Somaliya, wadanda ke shirin karbe ikon harkokin tsaron kasar daga hannun dakarun Tarayyar Afirka.

Jakadan Turkiyya a Mogadishu Mehmet Yilmaz - wanda ya yi aiki tsakanin 2018 zuwa 2022 - ya bayyana cewa Turkiyya na kan hanyar horar da kusan kashi uku na sojojin Somaliya, wato kimanin jami'ai 15,000 zuwa16,000.

A bara ne dai aka bude ofishin jakadancin Turkiyya mafi girma a Mogadishu babban birnin kasar a lokacin mulkin shugaban Somaliya na yanzu Mahmoud.

Manyan matakai uku da suka yi fice a shirye-shiryen Turkiyya a yakin na kusurwar Afirka.

Hukumomin gwamnati da masu zaman kansu na Turkiya sun danganta tallafin jin kai da suke bayarwa ga ayyukan haɓaka ilimi, inda suke ba da gudummawa ga tsaron gabar tekun Somaliya bisa ga kudurin kwamitin sulhu na MDD a matsayinta na fitacciyar mamba a kungiyar tsaro ta NATO, ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da sauye-sauye a fannin tsaron Somaliya, tare da kiyayewa da kuma daidaita dabarun hadin gwiwa tsakanin kasar da kasashen yankin kusurwar Afirka tun daga kan batun tsaro zuwa tsaro da kasuwanci.

Za a iya fahimtar sabuwar yarjejeniya tsakanin kasashen biyu idan aka kwatanta da tarihin dangantakarsu daga shekaru 13 da suka gabata.

Muhimmiyar riba ga Somaliya da yankin

Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Turkiyya da Somaliya na da fa'ida ta kai tsaye da kuma akasain hakan ga tattalin arzikin Somaliya, da tsaron gabar teku, da ma yankin baki daya.

Akwai yiwuwar ta bude kofa ga wasu tsare-tsare masu muhimmaci, wadanda suka hada da tsaron bakin teku da albarkatun ruwa da na fannonin kamun kifi da ci gaban zamani da raya tashoshin jiragen ruwa da sufuri da kayayyaki da kuma fannin yawon bude ido, da kuma musamman kan batun 'yan fashin teku a gabar tekun Somaliya.

Mashigar tekun Somaliya ita ce mafi tsayi a nahiyar Afirka, mai tsawon kilomita 3,898 daga Djibouti a arewa zuwa Kenya a kudu, sannan tana da wasu albarkatun halittu a yammacin tekun Indiya.

Kazalika Somaliya tana da yankin tattalin arziki na musamman na kusan murabba'in kilomita 1,000,000 wanda ya kai nisan mil 200 na ruwa daga teku.

Amma duk haka, har yanzu ba ta kai ga cimma albarkatu tattalin arzikinta na cikin ruwa ba, Manyan dalilan da suka sanya hakan sun hada da rashin isassun ababen more rayuwa na bangaren kamun kifi da ayyukan jigilar kayayyaki, bugu da kari da kuma batun da ya shafi gine fannonin tsaro daban-daban.

La'akari da bakin teku mafi tsayi da yalwar albarkatun ruwa a nahiyar Afirka, yankin tekun Somaliya na yawan fuskantar matsalar kamun kifi ba bisa ka'ida ba, wanda ba cika ba da rahoto kan shi ba da kuma wasu laifuffuka masu alaka.

Somaliya na asarar dala miliyan 300 a kowace shekara saboda kamun kifin da ake yi ba bisa ka'ida ba - kazalika albarkatun ruwa na cikin gida suna lalacewa sakamakon jiragen ruwa na kasashen waje da ke bi ta kansu, kazalika suna shafar rayuwar masunta na cikin gida.

Duk da yake har yanzu ba a samu wani ci gaba ba, fannin kamun kifi na kasar yana da matukar muhimmanci domin yana samar da abinci tare da taimaka wa walwalar rayuwa da samun kudaden shiga da guraben aikin yi ga sama da ƴan Somaliya 400,000 wadanda ke gudanar da ayyuka daban-daban kai tsaye ko a kaikaice a bangaren kamun kifi da sauran hidimomi masu alaka.

Duk da haka, a cewar wani bincike da Cibiyar tsare-tsare ta Heritage da Jami'ar Mogadishu City suka gudanar, fannin kamun kifi na samar da dalar Amurka miliyan 135 a duk shekara, kwatankwacin kashi biyu cikin dari na yawan abin da ake samu a Somaliya.

Don haka, fannin kamun kifi na da karfin samar da dala miliyan 500 a duk shekara a wani mataki na haɓaka tattalin arzikin Somaliya. Sannan, idan har ta kai ga matakin dorewarta, kasar za ta iya girban sama da tan 200,000 na kifin a duk shekara.

Ko da yake , bayanan gwamnati sun nuna cewa a shekarar 2022, masuntan kasar sun kama kusan metric ton 6,000 na kifaye.

Sabanin haka kuma, jiragen ruwa na masana'antun kasashen waje suna girbi kimanin tan metrik ton 13,000 a shekara.

A matsayin wani bangare na hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Somaliya, ana bukatar a yi amfani da kudaden shiga da ake samu daga zuba jari a bangaren sojin ruwa da na teku don samar da horo da kuma siyo kayan aiki ga masunta na Somaliya, tare da inganta ababen more rayuwa, da samar da sabbin ayyuka na kare albarkatun ruwa, hakan kuma na nufin samar da wasu hanyoyi da za su kara albarkatun kasar.

Bugu da kari, yarjejeniyar za ta iya bunkasa fannin kamun kifi ta hanyar jawo jarin kasashen waje don samar da kudaden shiga na ketare mai dorewa.

A cewar dandalin tattara bayanai na Statista, hare-haren masu fashin teku a cikin ruwan Somaliya ya kai kololuwa a shekarar 2011, inda aka samu rahotanni 160, wanda ya karu zuwa 358 a shekaru biyar tsakanin 2010 da 2015.

Wannan adadi ya ragu zuwa takwas a cikin shekaru bakwai tsakanin 2016 da 2022. Duk da mahimmancin alkalumman, a wasu lokutan ba sa ba da cikakken bayanan.

A cewar wani rahoto na 2010 zuwa 2012 na Majalisar Wakilai, “Ana kashe kusan dala biliyan biyu a ayyukan sojin ruwa a gabar tekun Somaliya a duk shekara.

Matsalar ita ce, waɗannan kudade suna magance ‘alamomin cutar' ce kawai sannan ba sa yin komai don magance tushen matsalar.” Jimlar farashin satar fasaha, ya tashi zuwa kusan dala biliyan 7 a shekarar 2011 tare da ƙarin hanyoyin kashe wasu kuɗade.

Yana da kyau, a jaddada yiwuwar sake bayyanar cuta idan ba a magance tushen abun da ke haifar da ita da kyau ba.

Akwai bukatar yarjejeniyar ta ba da gudummawa sosai ga kokarin kasashen duniya da ake ci gaba da yi ta hanyar tabbatar da tsaro a gabar tekun Somaliya da kuma bude hanyoyin tattalin arziki na kasashen dake gabar teku.

Tana da damar sake farfado da tashar jiragen ruwa da samar da kayayyakin aiki, da na fannin sufuri da samar da ingantacciyar hanya mai fa'ida ga yankin wajen inganta kasuwanci, harkokin sufuri, da damar tattalin arziki idan har suka samar da hanyoyin kwarewa wa al'ummar yankin.

Marubucin, Dokta Ibrahim Alegoz, yana aiki ne tare da Jami'ar Ibn Haldun, a sashen kimiyyar siyasa da huldar kasa da kasa. Ya rubuta wasu littattafai biyu: “Foreign Intervention and Radicalization in Somalia: How and when does conflict evolve into violence” da “Türkiye’s Humanitarian Diplomacy Policy in Somalia: Methods and Instruments.”

Bangaren da ya fi mai da hankali akai sun hada da rikice-rikicen siyasa da tarzoma da kuma tsoma bakin soji da dangantakar Turkiyya da Afirka musamman kan Somaliya.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika