Daga Fuat Sefkatli
Daga kasancewa daya daga cikin masu bayar da goyon baya daga waje ga hare-haren Khalifa Haftar da ba su yi nasara ba a Tarabulus a 2019 a yakin basasa mai rikitarwa na Libiya, Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi kwana babba tare da sauya akalar manufarta game da Libiya.
Tun bayan da aka nada Gwamnatin Hadin Kan Kasa (GNU) karkashin jagorancin Abdulhamid Dbeibeh a watan Maris din 2021, ana yawan yin muhawara da tambaya game da matsayin Hadaddiyar Daular Larabawa a Libiya.
Domin fahimtar yadda Hadaddiyar Daular Larabawa ta sauya manufa da ra'ayinta a yankin tun bayan shiga sha'anin Libiya a 2016, ya zama dole a dan yi duba zuwa abubuwan da suka faru a baya-bayan nan.
Jim kadan bayan kama mulki, Firaminista Dbeibeh ya ziyarci Abu Dhabi, inda ya yi tattaunawa da Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Zayed, sun mauar da hankali kan rawar da Hadaddiyar Daular Larabawa za ta iya taka wa wajen sake gina Libiya.
Haka kuma, a watan Yulin 2022, Hadaddiyar Daular Larabawa ta shiga tsakani wajen cimma yarjejeniyar karba-karba a mulki tsakanin Dbeibeh da bangaren gabashi na Haftar, wand ata taka rawa sosai wajen nada Farhat Ben Gadara a matsayin shugaban Kamfanin Mai na Kasa na Libiya.
A wannan lokaci, Hadaddiyar Daular Larabawa ta janye kashe kudade ga mayaka 'yan asalin Afirka a gabashin Libiya, wand ake nufin karaya ga kawancen Haftar-Wagner, kamfanin sojojin haya na Rasha da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Dadin dadawa, rahoton da wata kungiya mai alaka da gwamnati ta fitar ya a 2022 da 2023, an dinga nuna bukatar hade babban bankin kasa waje guda, aiwatar da zabe, da dakatar da arangama ta siyasa, wanda hakan na nuni da sauya akalar manufar Hadaddiyar Daular Larabawa a Libiya.
Tubalan sauyi mai muhimmanci
Da fari dai, sauyin gwamnati da aka samu a Amurka daga trump zuwa Biden ya janyo takun saka tsakanin Saudiyya da sauran kasashen Gulf ciki har da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Sakamakon yadda gwamnatin Biden ta dauki matakin ba sani ba sabo ga halayyar wasu kasashe a wasu yankunan ne ya sanya Hadaddiyar Daular Larabawa fara neman kawaye d aabokan hulda a yankuna.
Wani abu mai muhimmanci d aya taka rawa sosai wajen sauya akalar shi ne yarjejeniyar Abraham ta watan Nuwamban 2020, wadda ta kawo sasantawa da Isra'ila wadda ke nufin sake kulla alaka da hada kai a yankin.
Abun na biyu da ya biyo bayan hakan shi ne fara kusantar Turkiyya, wanda ya sanya Hadaddiyar Daular Larabawa sakkowa game da sha'anin Libiya.
Wani babban abu ma shi ne dakatar da kashe kudade ga maykaan Wagner da sojojin haya na Sudan da Chadi a Gabashin Libiya.
Za a iya kallon wannan mataki a matsayin wata dabara ta kaucewa cin karo da Turkiyya, kasar da ke da karfin ikon siyasa, tattalin arziki da zamantakewa a yammacin Libiya.
Kari kan hakan, kulla kyakkyawar alaka da gwamnatin Hadin Kan Kasa na nufin sauyawar Hadaddiyar Daular Larabawa daga matakin yaki zuwa na tabbatar d ahadin kai a Libiya.
Abu na biyu shi ne, kasancewar Libiya kasar a ke zama mahadar Saharar Afirka da kahon Afirka zuw atekun Bahar Rum, ya sanya ta zama mai muhimmanci ga Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ba hanyoyin kasuwanci ta ke iya samun iko da su ba, har ma da fadada karfin ikon soji.
Wannan yanayi ya sanya Libiya zama karfen kafa ga Hadaddiyar Daular Larabawa saboda burinta na zama matattarar kasuwancin China da Yammacin duniya.
A wannan yanayin siyasa da ake ciki, gabashin Libiya, da mafi yawancinsa ke karkashin ikon Haftar Khalifa, na baiwa Hadaddiyar Daular Larabawa babbar damar zama mai karfi a yankin.
Ana bayyana hakan da kasancewar ta kusa da tekun Bahar Rum, mallakar tashoshin jiragen ruwa da kuma damar iya shiga tsakani a kasashen Afirka da dama.
Musamman, tsarin safarar kayayyaki da aka kafa a yankin na da matukar muhimmanci go Sudan da Chadi, kasashen da Hadaddiyar Daular Larabawa ke da iko na kai tsaye a sha'aninsu.
Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi kokarin tabbatar da matsayinta a yankin ta hanyar aiki da tsare-tsaren sojin Yammacin duniya (irin su Amurka, Faransa, Ingila) da Kungiyoyin kasa da kasa (MDD NATO) da suke Libiya.
Wannan yanayi ya samarwa da Hadaddiyar Daular Larabawa damar bayyana ikonta da albarkatunta ga kawayen Yamma. Sai dai kuma, matsalolin da ake samu sakamakon hana fitar da albarkatun man gabashin Libiya ya wajabta sake komawar Hadaddiyar Daular Larabawa yankin.
Wannan sauyi ya samu ne bisa karfin ikon kasashen duniya, musamman Amurka da kasashen Turai, wadanda suka tsinci kansu a yanayi na dole su kawo mafita ga rikicin makamashi a duniya.
Dadin dadawa, kyakawawan motsi na diplomasiyya tare da gwamnatin Dbeibeh d akasashe da MDD ke yi, gami da yarjeniyoyi a bangaren makamashi da gine-gine da aka kulla da Gwamnatin Hadin Kan Kasa, duk sun rigayi yunkurin Hadaddiyar Daular Larabawa na sauya akalarta a manufofin da take dabbaka wa a Libiya.
Wani batu na uku da za a kalla shi ne sauyi na karara da ake iya gani a matsayin Hadaddiyar Daular Larabawa wajen mayar da martani ga juyin juya halin Libiya. A matakan juyin juya halin, wasu na fadin cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta ayyana ayyukan 'Yan Uwa Musulmi a Libiya a matsayin barazana gare ta a kasar.
Hadaddiyar Daular Larabawa ta fahimci cewa matsakaicin ra'ayin Musulunci a tsarin dimokuradiyya ne matakan da za su agaza wajen mayar da Larabawa turbar dimokuradiyya daban-daban.
Wannan fahimta ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa ga taimakawa Haftar, wanda ya kaddamar a hare-hare kan kungiyar addini a yammacin Libiya inda ya fake da sunan 'wanda suke yarda da raga gwamnati da addini'. Sai dai kuma, wasu sauye-sauye na yanki da kasa da kasa, hade da manufofin Haftar na kawo rikici sun bakantawa gwamnatin Abu Dhabi.
Bayan haka, yadda Haftar ya bar hadin kai da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar ya sanya kasashen neman sabbin kawaye a Libiya.
Aiwatar da karfin iko: Dabaru a sauyawar al'amuran tsaro
A yanayin sauyawar al'amuran tsaro a Libiya, dabarun Hadaddiyar Daular Larabawa sun bayyana karara ta bakin wakilinta a Majalisar Dinkin Duniya, Mohamed Abushabab, a yayin Taron Kwamitin Tsaro a watan Afrilun 2023.
Abushabab ya yada da yunkurin jami'in diplomasiyyar Sanagal Abdoulaye Bathily wanda kan batun goyon bayan MDD a Libiya ya shirya taron hadin kan soji na 5+5, wand aya hada da kwamandojin soji daga Tarabulus da Benghazi.
Haka kuma, Abushabab ya jaddada tsananin bukatar da ke akwai na fara raba mayaka da makamai, kwashe su da smaar da shirin shigar da su cikin al'umma da manufar hade kan bangarorin soji da suke rarrabe a gabashi da yammacin Libiya.
Wannan shaida ta sauyin manufa daga matsayin Hadaddiyar Daular Larabawa na farko, ya bayyana matsayar mayar da hankali ga runudunar soji kwaya daya mai karfi a Libiya.
Za a iya cewa Hadaddiyar Daular Larabawa na iya daukar babban nauyi wajen raba mayaka da makamai da sake shigar da su cikin al'umma musamman ma a gabashin Libiya.
A karshe, bayanan da aka fitar a watan Disamban 2023 ya bayar da shawarar kwashe dukkan mayakan kasashen waje da ke Libiya a lokaci guda.
Wannan mataki ya bayyana cewa Hadaddiyar Daular Larabawa a nan kusa da nesa ba za ta dawo da aiki da sojoji a kasar ba.
Yana da muhimmanci a fahimci cewa wanzuwar sojin Turkiyya a yankin, da ke da amfani wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, na kuma kawar da duk wasu masu son kawo rikici a Libiya.
A yanayin da ake ciki na yau na sasanta alaka tsakanin Turkiyya da Masar, ana sa ran Hadaddiyar Daular Larabawa za ta sassauta ra'ayinta tare da kuma zage damtse wajen neman hadin kan siyasa da na soji a Libiya.
Marubucin wannan makala Fuat Emir Sefkatli, mai bincike ne kan nazariyyar Arewacin Afirka a Cibiyar Bincike Kan gabas ta Tsakiya (ORSAM) da ke Ankara.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.