Daga Ganna Khalil
Akwai wani mai sana'ar zana gidaje Hassan Fathy da ke rayuwa a tsakiyar kasar Masar, inda tsohuwar sahara da yashi suke tashi sama, ana bayar da labaran fir'aunoni da dauloli.
Labarinsa da ayyukansa na da kayatarwa sosai, kuma abubuwan da ya assasa cikin lokaci za su yi ta yin shuhura, suna bayar da darussa da za su taimaka wajen habakar Afirka cikin gaggawa.
Ayyukan sana'ar zane na Fathy sun faro ne a lokacin da Masar ta tsinci kanta a lokacin da kasashe ke zamantuwa. Bayan shekaru da dama na mamayar Ingila, kasar ta yi gwagwarmayar sake fasalin kamanninta. Fathy ya nemo wadannan kamanni ta hanyar fasahar zanen gine-gine.
Masamar tarihi da dama na Masar, da suka hada da fasahar zane ta gidaje ta Coptic da Nubian ne yake amfani da su wajen tsarinsa. Yana yin zanen gine-gine duba da ilimin da yake da shi salon gidajen gargajiya da dabarun hada su.
Ya lura da amfanin da aiki da kayan da ake da su a kasar ke da shi, misalin bulon kasa, wanda suke da sauki kuma ba sa gurbata muhalli, ya so ya samar da tsarin gidaje masu rahusa da suka dace da al'adu da yanayin yankin.
Sakamakon haka, an saka masa sunan "mai zanen gini na talakawa" saboda yadda ya mayar da hankali wajen zana gine-ginen da ke kama da na zamanin da ko kauyuka, da talakawa masu karamin karfi za su iya mallaka.
Ya yi tunanin ya kamata zanen gidaje ya karfafi mutane wadanda ba su da karfin smaun kyawawan wuraren zama.
‘Zana gidaje don talaka'
A 1945 gwamnatin Masar ta baiwa Hassan Fathy aikin tsara kauyen da za a gina wa mazauna Gourna, wajen da ke yammacin gabar kogin Nil, kasa da tsaunukan Thedan da ke daura da Luxor.
Garin na da talakawa da yawa da suke sace tsaffin kaburbura a Wadin Sarakuna. Saboda mamayar wannan waje da jama'a suka yi ne ya sanya aka samar da Sabon Gourna.
A yayin da yake tunkarar irin wannan aiki, Fathy ya kudiri niyyar samar da birnin da zai amfana d ainganta rayuwar 'yan kasa. A yayin da Fathy ke kokarin cimma manufarsa, ya sanya jama'ar Gourna sun zama kamar wasu sabbin zuwa.
Misali, a yayin tsara gidajen, ya tsara tsakar gida ya zama wajen shakatawa ga mazauna gidajen. Ba a amfani da tsakar gida a irin wadannan wurare na Masar, inda ake amfani da su din ma, sun zama wuraren gudanar da ayyuka, ba wai wajen shakatawa ba.
Sakamakon haka, mutanen Gourna suka ki koma wa sabbin gidajensu, sai Fathy kawai ya hakura da wannan aiki bayan shekara uku.
Duk da aikin bai samu nasara ba, Sabon Garin Gourna ya zama wajen da har yanzu ake nazari a kansa. Garin na bayar da ilimi game da zanen gidaje a duniya wajen gama kayan zamani da na gargajiya waje guda.
Ya yi ta kokarin tabbatar da karfafa wa mutane masu karamin karfi su shiga harkokin tsara gidaje a matsayin babbar manufa.
"Mai zanen gidajen talaka", ayyukan da Fathy ya yi kan ayyukan tsara gidaje irin nasa, na da matukar muhimmanci a yau, a bangaren kare muhalli da kula da habakar birane.
Kyakkyawar gamayya
Ku yi tunanin a ce tunani da dabarun Fathy wani iri da aka shuka ba da jima wa ba, yanzu kuma sun fara hayayyafar rassan manyan bishiyu na fahimta. Wannan ilimi na taimaka mana wajen kula da kalubalen da ke damun mu a harkokin tsara birane, a yayin da suke sauya wa cikin sauri.
Biranen Afirka na habaka sama da na ko'ina a duniya. Nan da 2035, kusan rabin jama'ar Afirka za su dinga rayuwa a birane da garuruwa.
Wannan na nufin dole birane su fara tunanin samar da tsarin sufuri, makamashi da gidaje yadda ya kamata ga al'umma.
A biranen Afirka da ke habaka cikin hanzari, dabaru da ilimin zanen gine-gine na Hassan Fathy na zama wata fitila na hikima da muhimmanci. Tunanin Fathy ba ya tsaya ga kawai kula da muhalli da snaya jama'a su sauke nayin da ke kawunansu ba ne kadai.
Ya ga gina gidaje a matsayin abu da yake sama da harkar gini, aiki ne na hadin kai, inda jama'a suke taka rawa wajen tsari d akuma ginin kansa. Ta hanyar baiw amutane damar gina gidajensu, Fathy ya yi kokarin ba su damar su ji su mamallakan yankin ne, tare da kakkarfar al'ada da ingancin yanayin rayuwarsu.
Kare muhalli
Wannan ya mayar da hankali ga shigar da jama'ar yankin bai zama mai gurbata muhalli ba, kuma tare da baiwa jama'a damar su ji su ke da mallakin inda suke zama.
Wani abu mai jan hankali kuma, tsarin Fathy wanda da farko ya shafi amfani da hanyar gargajiya wajen samar da gidaje, a yanzu hakan ya yi daidai da habakar gidaje cikin sauri da Afirka ke samu. Dabararsa ta shigar da jama'ar yankunan cikin tsarin na dada smaun karbuwa.
Baiwa 'yan kasar damar bayar da gudunmowa wajen gina wa da tsara garuruwansu, zai magance kalubalen da ake fuskanta a lokaci guda.
Ta hanyar yin hakan, garuruwa za su iya kirkirar yanayin rayuwa tare da samar da damarmakin gudanar da kasuwanci, abun da ake bukata cikin gaggawa domin hanzarta habakar birane.
Duba ga wannan, tunani da dabarun Fathy sun sauya daga tsohuwar hanya zuwa amsar da ake bukata don magance kalubalen muhalli a yau.
Ta hanyar gwamutsa tunani daban-daban, dorewar muhalli, ingantuwar al'adu da saka hannun 'yan kasa a ayyuka, hanyar d ayake bi don tsara gine-gine ta dace da yadda biranen Afirka ke sauya wa a yau.
A yayin da birane ke aiki don kula da yadda ake habaka cikin gaggawa, a su iya amfani da koyarwar Fathy don neman daidaito tsakanin fasahihin baya da sabon cigaban kere-kere da ke tafe, ana kitsa labaran da za su inganta rayuwar jama'a, tare da kare muhalli.
Marubucin Ganna Khalil, dalibin Zane Gine-Gine da Tsara Birane ne a Jami'ar Qatar ne.
Togaciya: Ba lallai ra'ayin da marubucin ya bayyana ya yi daidai da ra'ayi, mahanga da manufofin buga labari n TRT Afirka ba.