Daga Yahya Habil
Kamfanonin fasaha na Afirka suna bunkasa tare da kara tasirinsu a nahiyar yayin da adadinsu ke ci gaba da ƙaruwa.
Sai dai kananan kamfanonin na Afirka suna fuskanatar tarin kalubale na mummunan yanayin yadda ake yi wa nahiyar kallo da kuma hanyoyin sake fasalin wadannan tunani.
Wadannan 'yan kasuwa sun kasance wani bangaren mai muhimmaci da ke taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka da dama, tare da kara tabbatar da tasirinsu wajen ciyar da nahiyar gaba ta fuskar tattalin arziki.
Ba wani abin mamaki ba ne, rawar da wadannan kamfanoni ke taka wa la'akari da yawan al'ummar Afirka, wadanda kusan kashi 60 cikin 100 daga cikinsu matasa ne masu shekaru kasa da 25 wadanda ke da ƙwazon kasuwanci dake nuna al'ummar da ake da su a wannan zamanin masu ilimin fasaha.
Muhimmin tasiri da ribar da kananan 'yan kasuwa a Afirka suke samu daga tattalin arzikin nahiyar a 'yan shekarun nan ya bayyana ne ta irin ci gaban da masana'antar yawon bude ido na yanki ya ke samarwa.
Karin da aka samu na shigowar baki 'yan kasuwa zuwa nahiyar na da nasaba da tasirin 'yan kasuwa masu tasowa suka samar tare da karfin gwiwa da ake samu daga masu son zuwa yawon bude ido da dama.
Habaka harkar yawon bude ido da kamfanonin 'yan kasuwa masu tasowa suka yi ya kara samar da wasu karin 'yan kasuwa a masana'antar, musamman wadanda ke da alaƙa da harkar tafiye-tafiye.
Shafin Hotels.ng a yanar gizo da ke zama mafi girman shafin neman dakin kwana na otel a Nijeriya, shi ne misali daya na irin wadanan kanfanonin 'yan kasuwa masu tasowa.
A shekarar 2018, Shugaban Kamfanin Hotels.ng Mark Essien ya bayyana cewa masana'antar tafiye-tafiye na cin gajiyar ƙaruwar yawan kamfanonin fasaha na 'yan kasuwa masu tasowa.
Wani karin misali na kamfanonin 'yan kasuwa masu tasowa da ya samu karfin gwiwa daga yawan tafiye-tafiye shi ne babban dandalin yanar gizo na Mauritius Ojimah.
Manufar da kafar ta sa a gaba shi ne daidaita tsarin tafiye-tafiyen Afirka ta hanyar hada matafiya da sauran fitattun kamfanoni a masana'antar tafiye-tafiye a duniya.
An kaddamar da kamfanin ne a lokacin bullar annobar coronavirus a shekara 2020, tun daga lokacin kamfanin ya ke ta kara samun ci gaba.
A cewar daya daga cikin shugabanin da suka samar da kamfanin Ojimah, Golden Chika-Okafor, kamfanonin da ke tasowa ''tsari ne na samar da mafita wanda aka kirkiro don magance matsalolin tafiye-tafiye a duniya a wannan zamani tare samar da yanayin cudeni-na- cudeka tsakanin yan'kasuwa da matafiya da kuma wuraren da ake kai ziyara a Afirka.''
Kamfanin Ojimah ya samu hadin gwiwa da hukumar kula da yawon bude ido ta Majalisar Dinkin Duniya (UNWTO) don samar da ingantattun bayanai da kuma hanyoyin fasaha da za su iya farfadowar da harkokin yawon bude ido a Afirka bayan barkewar annobar coronavirus.
Shafin yanar gizo na Ojimah yana hada mutane da kamfanonin jiragen sama fiye da 350 da sama da otal miliyan 1.2 da kuma wasu ayyuka sama da 200,000.
Yayin da ake kara samun kamfanoni masu tasowa, ana sa ran masana'antar yawon bude ido na Afirka ta ci gaba da bunkasa, ta hanyar habaka ayyukan 'yan kasuwa da kuma harkar yawon bude ido.
Kasa da makwanni biyu da suka gabata, ma'aikatar yawon bude ido ta Afirka ta Kudu ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta hadin gwiwa da kamfanin Google domin tallata kasar a matsayin babbar cibiyar yawon bude ido.
Ana sa ran kamfanoni masu tasowa su taka muhimmiyar rawa wajen ba da gudunmawa a wannan bangare na yawon bude ido a Afirka ta Kudu yayin da ita kuma Google ke shirin ba su tallafi ta hanyar horo kan yadda ake yin talla da zai taimakawa wajen tantance wuraren yawon bude ido a yankin.
Da kuma samarwa kananan ‘yan kasuwa a fannin damar cudanya da sauran makamantan kamfanoni a duniya a matsayin wani bangare na hadin gwiwa.
Ma'aikatar yawon bude ido ta Afirka ta Kudu ta yi hasashe kan cewa adadin bakin da za su shigo kasar zai zarce mutum miliyan 10 da aka samu a shekarar 2019 ya zuwa karshen watan Maris na shekara mai kamawa.
Yanayin ya nuna sakamako mai kyau da aka samu a farfadowar masana'antar yawon shakatawa daga annobar COVID-19.
A bangaren arewacin nahiyar, taron GITEX Africa 2024 ya zama manuniya kan yadda fannin yawon bude ido ke ci gaba da bunkasa nahiyar, kuma hakan ba ya rasa nasaba da irin gagarumin gumudumawar da kamfanoni masu tasowa suke bayar wa.
Taron, wanda za a gudanar a Marrakech a watan Mayu 2024, tabbas zai ba da gudummawa ga harkokin yawon bude ido la'akari da cewa yawancin masana'antun fasahohi za su ziyarci kasar Maroko don halartar taron.
Yarjejeniyar Afirka ta Kudu da Google da kuma taron GITEX na Afirka a Maroko, na zama abubuwa biyu dake nuna yadda masana'antar yawon bude ido take a mafi karancin nahiyar a duniya.
Kamar yadda aka bayyana a baya, habaka da samun ci gaban masana'antu ya haifar da dimbin masu yawon ziyara, tare da samar da wani tsari mai fa'ida da zai yiwa tattalin arzikin Afirka hidima sosai. .
Marubucin, Yahya Habil, ɗan jarida ne mai zaman kansa a Libya da ke mayar da hankali kan harkokin Afirka. A yanzu yana aiki ne da wata ƙungiyar bincike a Gabas ta Tsakiya.
Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.