Daga Firmain Eric Mbadinga
Littafin Illusions perdues na marubucin Faransa Honoré de Balzac, na dauke da babi guda da ya sadaukar ga abin a ya kamanta da "prodigious cumulative effect" ma'ana kurkuku a halayyar dan adam.
"Mutanen da aka tsare," in ji shi "Suna fusata sosai a daren su na farko a kurkuku."
A wajen daure mutane da ke tsakiyar kauyen Baporo da ke lardin Sanguie a Burkina Faso, an samar da wannan gidan kurkuku budadde da manufar gyaran hali ba wai daure fursunoni ba, kuma kurkukun na sanya mazaunansa su manta da jin ba su da wata makoma mai kyau, kamar yadda Balzac ya bayyana a littafinsa.
Manufar ita ce a bai wa fursunoni damar koyon darussa daga kura-kuran da suka yi, kuma su koyi wasu dabaru da sana'o'i da za su taimaka musu yin rayuwa mai kyau.
Duba ga wasu ka'idoji, fursunonin na samun horo kan kasuwanci da ya shafi noma da kiwo, don su samu damar dawowa cikin al'umma daga kurkuku.
A Afirka, Burkina Faso na daga kasashe na farko da suka fara aiki da tsarin sauya halaye da dabi'un mutanen da aka daure na wani lokaci ko aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai.
A 1986, a tsakiyar Baporo, cibiyar ayyukan noma, marigayi tsohon shugaban kasar Burkina Faso Thomas Sankara ya gina gidan kurkukun a waje mai girman hekta 100.
A tsawon lokaci, cibiyar tsare mutanen ta samu koma baya a karkashin gwamnatoci daban-daban a kasar da ke Yammacin Afirka. Labari mai dadi shi ne yadda gwamnati mai ci ke ta kokarin farfado da wajen ta hanyar farfado da ayyuka a cibiyar.
A ranar 6 ga Disamban bara, Sabila Sawadogo, darakta janar na Hukumar Kula da Gidajen Yarin Burkina Faso ya bayyana cewa ayyukan noma da fursunoni ke yi a gidan gyaran hali na Baporo, na samar da tan da dama na kayan marmari da kayan miya a 2023.
Ana noma a kusan hekta hudu na gidan kurkukun da ya kasance a bude, inda ake noma ayaba da sauran kayan miya d ana marmari, baya ga kiwon shanu ta hanyar amfani da dabarun zamani.
A yayin da manufar da ake a ita, ita ce a koyar da sana'o'i ga fursunoni, wanda da zarar sun fita za su samu ayyukan yi a tsakanin jama'a.
Ana amfani da amfanin gonar da suke samarwa don ciyar da fursunonin Burkina Faso, sannan a kai suaran kasuwa a sayar. Ana saka kudaden a asusun gwamnati, in ji Sawadogo, a wajen taron watan Disamba.
Romaric Ndembi Moussoiami, likitan halayyar dan adam kuma dan kasar Gabon na kallon gyaran halin a matsayin shirin tallafa wa al'umma da ke da daraja.
A matsayin sa na kwararre kan sanin halayyar dan adam, koyaushe yana karfafa gwiwar a kula da mutane yadda ya kamata, kuma a koya musu sana'o'in da suke so a gidan kurkukun budadde.
Moussaoimi ya shaidawa TRT Afirka cewa "Dole ne a lura da irin halin da fursunoni ke cik a irin yadda suke ji a ran su, a kuma kare martaba da mutuncinsu. Hatsarin shi ne kar a ce kawai za a yi amfani da su ne kamar wasu leburori, duba da yanayin da suke ciki. Ko rufaffe ko budadden gidan kurkuku, dole ne ya zama ya cika sharuddan kawo mutane a tsare su. Idan ba haka ba, to shirin ba zai yi nasara ba."
Masanin halayyar dan adam din ya kuma ce baya ga koya musu sana'o'in da za su ba su kudade, shirye-shiryen koyar da rubutu da karatu, wasanni da kwasa-kwasan kasuwancin zamani kamar su girke-girke da hada kayan kwalan da makulashe, za su karfafa horon da ake bayarwa a cibiyar a ke Baporo.
Muhimmin wajen gyaran hali
Kwararru na cewa nasarar duk wani wajen gyaran hali ta ta'allaka ne a kan kyakkyawar niyyar da ake da ita da kuma shirin da masu ruwa da tsaki kan harkar suka yi - fursunoni da ma'ikatan kurkuku - wajen kawo canjin da ake bukata.
"Kawai misalai da dama na tsaffin 'yan kurkuku da suka sake sbauwar rayuwa bayan gyara halayensu tare da shigar da su cikin jama'a. Wadannan mutane sun saje da jama'a tare da samun abubuwan yi." in ji Moussaoimi.
Shugaban gwamnatin soji ta wucin gadi a Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore, ya gamsu da ayyukan cibiyar gyaran halin, kuma ya zama babban jigon karfafa musu gwiwa.
An rawaito Traore na cewa "Ya dogara kan me kowane fursuna zai iya yi, za mu ba shi damar yin wannan abu. Za su samar da abubuwan da za su amfani al'umma."
A wajen wani taro da aka gabatar a watan Disamba Sawadogo ya shaida cewa cibiyar na bukatar halin samarwa da fursunoni da ma'aikatan da ke kula da su kyakkyawan yanayin rayuwa.
Ya ce "Cibiyar na bukatar dakunan kwana. Wadanda ake da su ba za su dauki sama da fursunoni 44 ba. Muna kuma bukatar kayan aikin noma ga gonakinmu. Muna bukatar sake gina cibiyar bayar da ruwa, wadda idan damuna ta yi take nutsewa a cikin ruwa. Sannan kuma ba ma iya kubutar da amfanin gonarmu idan ana fama da matsalar fari."
Mahukunta na fatan za su fara kiwon kifi nan da wani dan lokaci, a wani bangare na kokarin fadada sana'o'in da suke yi a gidan kurkukun Baporo.
Haka kuma samar da kayayyakin ilmantarwa da shigar da fursunoni cikin al'umma a dukkan gidajen kurkukun kasar na daga cikin shirin da ake da shi.
F Ollo Obiang, mataimakin sakatare janar na fursunonin SOS da ke Gabon, ya yi kira da a samar da tsarin da ya haura na gyara hali kawai a gidajen kurkuku.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Baya ga kokarin da ake yi a kasashe irin su Burkina Faso, muna bukatar shigar al'umma sosai cikin wannan aiki, ta yadda za a tabbatar da mutanen da aka sauya wa hali aka koya wa sana'a a kurkuku sun narke a cikin jama'a cikin sauki da sauri."