Maroko dai na daga cikin kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka inda ta samun 'yancin kai a 1956 /Hoto/AP

Daga Martin Jay

A ‘yan kwanakin nan aka bayar da rahoton cewa sojojin haya na Wagner suna yi wa gwamnatin Burkina Faso aiki, kamar yadda wata kafar watsa labarai ta Faransanci ta bayyana.

Hakan ya soma razana Yammacin Afirka, musamman gwamnatin Ghana wadda take daukarsu a matsayin barazana, inda Birtaniya da Amurka ke ganin Faransa tana rasa ikon da take da shi a kasashen da ta mulka, inda ake ganin Rasha za ta maye gurbinta.

Suna da gaskiya da suka shiga damuwa. Hakan na faruwa a hankali, idan aka ga halin da Mali ta shiga da kuma yadda Rasha ke karkata da bayar da agaji ga Burkina Faso.

A yanzu dai kallo ya koma ga wannan kasar da ke Yammacin Afirka inda ake son ganin ko kasar za ta yanke hulda da gwamnatin Faransa, duk da wasu za su yi shakkar cewa hakan bai faru a hukumance ba, amma ta faru ta hanyoyi da dama.

Ta bi sahun makwafciyarta Mali wadda sojojin da ke jagorantar kasar suka samu sabani da Macron tun a ranar farko; an haramta kafar watsa labaran Faransa ruwaito labaran inda daga baya aka kori sojojin Faransa daga kasar.

Ta bangaren Mali, an fara ne da sojojin Faransa sannan kafafen watsa labarai sai kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

A Burkina Faso kuwa, akwai kungiyoyi masu zaman kansu da kuma dakarun Faransa kalilan, sai dai sakamakon barazanar da gwamnatin mulkin soja a kasar take ganin tana fuskanta, sojojin na ganin Faransa na goyon bayan tsohon shugaban kasar.

Ana fargabar nan da lokaci kalilan Ouagadougou za ta bi sahun Mali.

Kashi 50 na gwal a taskar Paris?

Idan hakan ta faru, za a buga labarin Burkina Faso a CNN da BBC kan cewa gazawar Afirka wajen kasa rabuwa da mulkin soji wurin gudanar da gwamnati bayan samun ‘yancin kai.

Duk da cewa wannan gidan talabijin din mai magana da harshen Faransanci na Afirka ya bayar da rahoto jim kadan bayan an ga wani gajeren bidiyo na Firaiministan Italiya inda take cewa Faransa ce ta dauke kashi 50 cikin 100 na gwal taskar gwal din Burkina Faso.

Kuma sakamakon hakan, ta mayar da kasar baiwa inda take samar da ‘yan ci-ranin da kullum suna cikin kwale-kwale domin neman mafaka a Italiya. Sai dai batun da Firaiminista Giorgia Meloni ta yi ba gaskiya bane.

Faransa ba ta da wani gwal na kasar Burkina Faso, sai dai tana rike da wani sashe na tattalin arzikinta – kuma kasashe da dama na Yammacin Afirka masu magana da harshen Farana – ta hanyar kudin da Faransa ta samar.

A yau ana kallon matakin a matsayin wata igiya ta ragowar mulkin mallaka da take zagaye a wuyan kasashen.

Duk da cewa maganganun da Meloni ta yi ba daidai suke ba, amma dai suna kan hanya.

Idan wadannan kasashen za su iya katsewa daga sarkar da Faransa ta daure su da ita da kuma dangantakar da suke da ita ta mulkin mallaka, za su iya samun dama ta samun ci gaba ta fannin siyasa da tattalin arziki.

Idan Burkina Faso ta dauki mataki na gaba na korar sojojin Faransa daga kasarta da kuma neman agajin Rasha, lallai akwai babbar barazana sakamakon sauran kasashen Afirka renon Faransa za su bi sahu, inda Faransa da kasashen yamma za su rabu da akalla rabin Afirka.

Irin wannan ficewar za ta zama abin da bai taba faruwa ba kuma za a kalli lamarin a matsayin wani babban ‘sake daukar saiti’ da muke ta ji.

Sai dai akwai masu nasara da wadanda za su yi rashin nasara. Amma shin kasashen yamma za su yarda an ci su da yaki kan wannan lamarin?

Hadin Maroko

A nan ne Maroko ta shigo. Ba da jimawa ba, Macron ya tura minista zuwa Rabat domin ya yi aiki da ‘yan Maroko da kuma shirya ziyararsa ga sarkin kasar a watan Janairu.

Hannun riga da aka yi tsakanin Macron da Maroko, ana ganin ya samo asali ne sakamakon tsauri da kasar take da shi kan masu shigar kasar.

Amma a gaskiya, hakan ya faru ne sakamakon rashin daukar mataki mai kwari da Macron din bai yi bane kan ikirarin mallakar Yammacin Sahara da Marokon ta yi.

Kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa an gyara dangantaka tsakanin kasashen biyu bayan da ministocin harkokin wajen kasashen suka dauki hoto suna gaisawa suna murmushi inda suka sanar da komai ya dawo daidai.

Amma ba wannan bane asalin labarin. Maganar gaskiya ita ce ‘yan bokon Maroko sun gaji da ita kanta Marokon da Faransa.

A manta da batun Burkina Faso da Mali. Babu wadanda a duk Afirka suka gaji da Faransa kamar ‘yan Maroko sakamakon dangantakarsu ta musamman da gwamnatin Faransa a karshe ba ta haifar da komai ba sai ciwon kai da takaicin da kullum da shi suke kwana su tashi.

Ba kamar Burkina Faso ba, wadda har yanzu ta dogara ne kan taimakon Faransa, ‘yan Maroko sun kwana da sanin irin jarin da Faransa ta zuba a Casablanca wanda hakan ya sa suka zama hanta da jini da Paris ko suna so ko ba su so.

Taron sasancin Maroko da Faransa

A taron watsa labaran da suka yi a Rabat, ga wadanda suka fahimta, Ministan Harkokin wajen Maroko Nasser Bourita ya yi wani abin da ba a saba ba; ya yi jawabi da harshen Darija, wanda hakan ya sa dole baki su sa a yi musu tafinta.

Hakan bai taba faruwa ba, kuma wannan sako ne aka soma tura wa Macron: Lokacinku ya kusan yi.

A shirye muke mu kawo karshen duk wata dangantaka da Faransa idan za mu yi hakan.

Amma kuma dangantakar da ke tsakanin Maroko da Faransa ce za ta iya ceto Macron din da kasashen yamma a Afirka.

Tasirin da Maroko ke da shi a nahiyar na kara habaka matuka kuma yana kara bazuwa a kasashe renon Faransa inda har take da banki a wuraren.

“Kasashen Larabawa suna ci gaba da turjiya game da abin da ke bazuwa a siyasar duniya kan dangantakar da ke tsakanin yankin da Amurka da China da kuma ta wani bangaren Rasha, inda ake kallon abin ta gasar nuna karfi tsakanin kasashen duniya,” kamar yadda Hafed Al-Ghwell ya rubuta.

“A takaice, aksarin kasashen yankin za su ci gaba da nesantar da kansu daga wannan tafiyar ta hanyar amfani da damar gasar da manyan kasashen suke yi domin samun abin da suke so”.

Akwai yiwuwar masanin na Amurka yana magana ne kan Faransa da Maroko, wanda ke nuna irin raunin mulkin mallaka wanda yake nunawa a Marokon, inda akalla cikin tsari mai wahala, ‘yan kasashen Turai suke bin hanya mai sauki domin samun katin zama a kasa.

Togaciya: Wannan ra'ayi ne na mutum da ya rubuta makalar, ba lalle ba ne ya zama ra'ayin TRT Afrika.

TRT World