Daga Kabir Adamu
Nahiyar Afirka tana fuskar juyin mulki iri-iri, inda kasashe da dama suke fada wa hannun mulkin sojoji – ta baya-bayan nan ita ce kasar Gabon wacce ke yankin Tsakiyar Afirka.
Ko da yake daya daga cikin juyin mulkin da ya fi kowanne sarkakiya shi ne wanda aka yi a Nijar. Fiye da wata daya kenan tun bayan da sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnatin Nijar.
Tun lokacin da jagororin juyin mulkin wadanda yanzu suke kiran kansu Majalisar Tsaron Kasa wato yake National Council for the Safeguard of the Homeland (CNSP), suna kara karfafa mulkinsu bayan sun sha gaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yankin Yammacin Afirka (ECOWAS) wadda ke fafutikar dawo da tafarkin dimokuradiyya a kasar.
Har yanzu Bazoum na tsare
Hambararren Shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa ciki har da dansa wanda ke zuwa makaranta, suna ci gaba da kasancewa a tsare, rahotanni sun ce suna cikin wani mawuyacin hali a wurin da ake tsare da su a fadar shugaban kasa a birnin Yamai.
Majalisar Tsaron Kasa (CNSP) tana samun goyon baya sosai daga cikin gida da kuma wasu kasashe da ke karkashin mulkin soja kamar Burkina Faso da Guinea da Mali da kuma kasar Rasha.
Sojojin sun yi watsi da bukatocin Kungiyar ECOWAS na mayar da kasar kan tsarin dimokuradiyya, ciki har da dawo da hambararren shugaban kan mulki – wani abu mai kamar wuya.
Jagororin juyin mulkin sun kara tabbatar da ikonsu ta hanyar nada ministoci da gwamnonin yankin da kara bunkasa goyon bayan da suke samu daga al'umma.
A ranar 26 ga watan Agustan shekarar 2023, jagororin juyin mulki shirya wani gangamin nuna musu goyon baya a filin wasa na Seyni Kountche mai daukar mutum 30,000 a tsakiyar birnin Yammai.
An samu 'yan Nijar akalla 20,000 da suka halarci taron, ana bushe-bushe kaho da daga tutar Nijar da Aljeriya da kuma Rasha, an yi raye-raye da wasanni iri-iri a filin wasan.
An rika daga rubuce-rubuce nuna goyon baya ga sojoji da kuma daga sakonnin nuna kin jinin kasar Faransa da Kungiyar ECOWAS. Ana zargin Faransa da Kasashen Yamma kawayenta da kitsa shirin amfani da karfin soja a kan Nijar da ECOWAS ke jagoranta.
ECOWAS ta yi Allah wadai
ECOWAS ta yi taro a ranar 30 ga watan Yulin shekarar 2023 da kuma a ranar 10 ga watan Agustan 2023, kuma Majalisar Zaman Lafiya da Tsaro ta Tarayyar Afirka (AU) ita ma ta yi taro a ranar 14 ga watan Agustan 2023.
Kungiyoyin biyu sun ci gaba da yin Allah-wadai da abin da suka kira "yunkurin juyin mulkin" a Nijar kuma sun sanya mata takunkuman tattalin arzikin da kuma yiwuwar amfani da karfin soji wajen dawo da mulkin dimokradiyya a kasar.
Tun ranar 30 ga watan Yulin 2023, kungiyar ECOWAS a martani kan juyin mulkin Nijar, ta kakaba takunkuman tattalin arziki ciki har da rufe boda da rufe asusun bankin kasar a kasashe mambobin kungiyar kuma Nijeriya ta yanke wutar lantarkin kasar – Nijar ta dogara da Nijeriya kan wutar lantarki.
Wadannan takunkuman sun kara sa al'amuran rayuwa sun kara tabarbarewa a Nijar, Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi cewa yara miliyan biyu suna hadarin fada wa matsananciyar yunwa da rashin samun taimakon da ya dace da kuma magunguna.
ECOWAS ta aika da tawagogin diflomasiyya da dama zuwa Nijar a kokarin warware matsalar. Daya daga cikin tawagogin wanda tsohon Shugaban Mulkin Sojin Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar (Mai Ritaya) ya jagoranta da wasu malaman addini, ba su samu yadda suke so ba daga wajen jagororin juyin mulkin.
A ziyarar da suka kai ta baya-bayan nan, wakilin kungiyar ECOWAS Janar Abdulsalami Abubakar (Mai Ritaya) da tawagarsa sun gana da jagoran juyin mulkin Janar Abdourahamane Tchiani da tawagarsa, da kuma hambararren Shugaba Mohamed Bazoum.
Watsi da shirin mika mulki nan da shekara uku
Bayan ganawar, jagoran juyin mulkin ya nuna sha'awarsa ga tattaunawa. Kodayake, a rana guda, a wani jawabi da aka yada a talabijin, inda Majalisar Tsaron Kasa (CNSP) ta bayyana cewa za ta mika mulki ga farar hula nan da shekara uku.
Kungiyar ECOWAS ta watsi da shirin mika mulki ga farar hula cikin shekara uku kuma ta nanata aniyyarta ta dawo da Nijar kan turbar dimokradiyya. Kungiyar ta sha maimaita cewa ta fi son warware matsalar ta hanyar dimokradiyya, amma kuma ta ce za ta iya amfani da karfin soji idan ta kama.
Ko da yake dangantaka tsakanin jagoran juyin mulkin da Faransa wadda ita ta yi wa kasar mulkin mallaka, tana ci gaba da lalacewa.
Abin da ya biyo bayan juyin mulkin, da kuma Faransa da ta ki yin maraba da juyin mulkin, Majalisar Tsaron Kasa (CNSP) ta sanar da soke duk wata hulda da sojojin Faransa.
Bugu da kari sojojin sun dakatar da lasisin kafafen yada labaran Faransa da ke aiki a Nijar ciki har da Radio France International (RFI) da France 24.
Majalisar Tsaron Kasa (CNSP) ta bai wa jakadan Faransa a Nijar wa'adin sa'a 48 da ya fice daga kasar. A nata martanin Faransa ta yi watsi da matakin kuma ta ce CNSP ba ta hurumin daukar wannan mataki.
Akwai wani tanadi da ke cewa tabarbarewar dangantaka tsakanin kassshen biyu, wanda zai iya jawo karshen huldar tattalin arziki, abin da zai iya tasiri kan yarjejeniyar hakar ma'adanai tsakanin kamfanin Faransa da kasar Nijar.
Siyasar Kasashen Yamma
Amurka a nata bangaren dangane da abubuwa da ke faruwa a Nijar ta ce tana baya-baya saboda daidaita maradunta da kuma bukatar wanzar da dimokradiyyar Kasashen Yamma a fadin duniya.
Har yanzu Amurka ba ta bayyana aikin CNSP a matsayin juyin mulki ba kuma ta tura wakilan diflomasiyya da dama zuwa Nijar ba tare da samun nasara ba, ban da batun cewa har yanzu jagororin juyin mulki ba su taba maradun Amurka da ke kasar ba.
Idan gwamnatin Joe Biden ta ayyana aikin CNSP da juyin mulkin, to hakan zai jawo cikas ga taimakon da Amurka take bai wa Nijar a bangaren tsaro.
Amurka tana da dakaru 1,100 a Nijar. Tana da wani sansanin jirage marasa matuka a kusa da Agadez, ta kashe dala miliyan 100 wajen gina sansanin kuma tana amfani da shi wajen tattara bayanan sirri da wasu aikace-aikacen tsaro a yankin Sahel tun shekarar 2018.
Abubuwa da yawa da ke faruwa za su yi tasiri a kan makomar Nijar, ciki har da yadda kungiyar ECOWAS take tafiyar da matsalar da batun barazanar amfani da karfin soja wanda mutane da yawa ba sa goyon baya da kuma kasashe mambobin kungiyar.
Wani batu kuma shi ne yadda Faransa da Amurka suke kokarin hada karfi wuri daya don su yi hadin gwiwa a kokarin fitar da matsaya daya.
Yadda wasu kasashen Yankin Gabas ta Tsakiya da wasu kasashe kamar Turkiyya suka mayar da martani kan abubuwan da ke faruwa a Rasha kan mutuwar shugaban kungiyar sojojin haya ta Wagner, Yevgeny Prigozhin, hakan ma zai yi tasiri kan abubuwan da ke faruwa a Nijar.
Marubucin Dokta Kabir Adamu shi ne Manajan Darakta a kamfani mai nazari kan harkokin tsaro wato Beacon Consulting Ltd a Nijeriya da Sahel.
Togaciya: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin TRT Afrika ba.